Sashe 49
Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiyasa yakeso yasan wace irin alfarma ce wannan
[06/06, 01:52] +234 808 996 5176: [05/06/2019 4:28 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*67*
Cikin nutsuwa Maryam tace"dazu munyi magana da Dr Sofia cewar zan fara aiki ranar Monday, sai na nemi alfarmar cewar inaso abari zuwa litinin ta sama, sabida a cikin wannan satin zanyi aure shine tace sai na nemi izini daga gareka"
Shiru yayi yana sauraron muryarta jikinshi yayi bala'in sanyi muryata ta kashe masa jiki sosai, da kyar yayi gyaran murya yace" duk abinda Dr Sofia tafada miki hakane in kina bukatar yin aiki a wannan hospital din zaki bi doka ni babu ruwana da wani ranar auranki, sabida haka tilas zaki fara zuwa aiki ranar da aka bukata,sabida haka zabi ya rage naki, kinsan dai baki fi kowa ba"
Yana gama fadin haka ya kashe wayarsa batare da ya saurari abinda zata ce ba
Maryam tayi sakato da waya a hannu tana mamakin wannan Abu kwata-kwata tarasa tunanin da zatayi dole zata sami Momy da maganar kuma zata fada mata komai
"Wallahi tallahi Abdul indai nice Na haifeka baka isa ka auri yarinyar nan ragowar maza, domin baza ka bata min zuria ta ba"
Hajiya Rakiya tafada tana nuna Abdul da hannu bakinta sai kumfa yake sabida tsabar masifa
Abdul ya rirrike mata kafafu tamkar zaiyi kuka yace"Hajiya kiyi min rai ki lamunce min in auri yarinyar nan, wallahi zakiji dadin zama da ita Maryam yarinya ce kintsatstsiya kamila mai hankali da nutsuwa, dan girman Allah ki yi hakuri ki amince min"
Yakarashe maganar kamar ya fashe da kuka
Hajiya Rakiya ta harzuka a zafafe tace"yanzu Abdul kamarka Dan asali Dan babban gida karasa wacce zaka aura sai wannan yarinyar to wallahi ashir dinka, yanzu-yanzu muka dawo ma daga gidansu nida Hajiya Mairo naje naci musu mutumci, duk wani abu da kasan ka kaimu kabar musu mutsiyata, amma baza mu taba had a jininmu da gurbataccan jini ba"
"Hajiya kin kasa fahimta ta wallahi Maryam yarinya ce mai hankali ki kwantar da hankalin ki Dan girman Allah ki bari Na aureta"
Yafada kamar zai fashe da kuka
"La'ila ha'illallahu"
Hajiya tafada tana tafa hannu cikin mamaki
Tacigaba da cewa "yanzu kuka zakayi kan wannan "yar iskar yarinyar"
"Ni Rakiya naga takaina maganar jama'ar gari ta tabbata dama an fada yarinyar mayya ce, oh ni Rakiya"
Tafada cikin mamaki
Shiru Abdul yayi kanshi a kasa sai kukan zuci yake ganin yadda Hajiyarshi take kokarin tara masa mutane
Suna cikin wannan halin Alh Alhassan ya shigo, cikin sallama
Ya bisu da kallo kawai yana mamaki Rakiya ganin yadda ta dora kafa daya kan daya ko amsa masa sallama ba tayi ba
Abdul ya amsa yana masa sannu da zuwa
[05/06/2019 4:55 PM]
Binta Umar Abbale: Ko zams bai yi ba ya kalli Abdul din dake gurfane gaban hajiyar yace"mai yake faruwa ne ?
Naganku kamar cikin wani hali"
Hajiya tace" babu abinda yake faruwa sai alkairi ina fada masa ne kawai a matsayina na uwarsa ban amince ya auri tsintacciyar mage ba"
Wani kallo Alh Hassan yayi mata yace"to sai ki hana ai Allah ya kaimu ranar daurin auran"
"Ameen zan hana kuwa sabida ai bakai kadai kake da iko dashi ba"
Girgiza kai yayi kawai ya wuce ciki Abdul ya mike ya bi bayanshi Hajiyar ta bisu da wani kallo tana tabe baki
Ko da suka hau sama Abdul zubewa yayi kan Sofa yana fidda numfashi sama-sama zuciyarsa kamar ta yi bindiga Dan bakin ciki
Nan mahaifinshi yace "ka kwantar da hankalinka babu abinda ta isa ta hana sai ikon Allah
[06/06, 19:55] +234 808 996 5176: [06/06/2019 10:46 AM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*108*
Abdul ya sauke ajiyar zuciya yana kallon mahaifin nashi yace"wallahi alhaji ban San abinda yake damun hajiyata ba kwata-kwata takasa fahimtar abinda nakeso in fahimtar da ita a kan lamarin"
"Karkadamu da duk rikicin da zatazo maka dashi ka rabu da ita kawai tayi tagama aure da tilas a daurashi kai da Maryam din, sai dai in kaine
kabani kunya"
"Allah ya shigemana gaba"
Abdul yafada yana kokarin mikewa domin tafiya, nan sukayi sallama ko da ya sauko kasa hajia Rakiya tashi daga gurin sabida haka da sauri ya fice daga gidan domin bayaso ta kara ganinshi.
A daran yaje gurin Maryam yana bata hakuri kan wulakacin da hajiyarshi tazo tayi musu
Cikin mamaki Maryam take kallonsa tace"wallahi in banda kafada min yanzu Sam ban San abinda yake faruwa ba, amma don Allah ka kwantar da hankalinka in har ni rabonka ce to babu mahalukin da ya isa ya hanamu auran, shiyasa nakeso ka tsayar da ranka guri daya"
Haka dai Maryam tayi ta tattashin sa da kalamai masu sanyi kan kace kwabo zuciyar Abdul tayi sanyi sai hira suke cikin nishadi
To a wannan lokacin ma Nasir na can tare da Mubina ta rikeshi duk ta takura masa tahanashi tafiya gida duk ta cikashi da kissarta da kisisina
Tana zaune kusa dashi duk ta dabaibayeshi jikinta a nanike da nashi sai hira take masa
gashi tana sanye da wasu mutsiyatan eingilsh waer wanda ya fito mata da dukkanin halitar jikinta mussaman kirjinta
Shikam ji yakeyi Duk ta takura masa wallahi jikinshi yayi nauyi sosai Duk abinda take cewa baya ji sabuda ba wannan ne a gabanshi ba wata muguwar sha'awace ta ke damunshi ya rasa yadda zaiyi sai faman lumshe ido yakeyi
Lokaci kankani Mubina ta fahimci halin da ya shiga sai ta kara matsa kusa dashi gami da rike hannushi guda ta rintse a nata tana sakin ajiyar zuciya tace"mySugar boy ya akai ne wai na lura duk kayi sanyi wallahi, ka kwantar da hankalinka zan jiyar da kai dadi sosai da sosai ni dai abinda nakeso daga gareka ka so ni kamar yadda nake sonka"
Nasir ya bude lumsassun idansa Wanda suka kada sukayi jajazir ta sauke su a kanta maganarshi a sarke yace" ki gwada min irin son da kike min yanzu domin in tabbatar dashi"
Anzo gurin
Mubina tafada a zuciyarta
Batare da bata lokaci ba kawai ta haye cinyarsa gami da sakalo wuyansa da hannunsa suna fuskantar juna Mubina sai faman lumshe masa ido take
Shi kuwa ya kurawa kirjinta ido kurr!
Fuskarshi ta fara shafawa da hannuwanta tana zagaye sajanshi Wanda ya kwanta yayi luwai a fuskar sai sheki takeyi
Rintse ido yayi yana karbar wasan domin bakaramin dadi yakeji ba abinka da mutumin da yake a bukace kan kace kwabo ya rikice ya kamo fuskarta da sauri yana laluben bakinta
An kawo kuka gida mutuwa dama haka take so
Nan take ta kamkameshi itama tana tura masa qirjinta ga bakinsu sarkafe da juna sai kiss sukeyi na fitar hankali
Kankace kwabo Nasir ya gigice ya fita hayyacinsa babu abinda yake bukata a lokacin in ba yaji yana biyawa kanshi bukata ba
[06/06/2019 11:18 AM]
Binta Umar Abbale: Kwanciya yayi sosai kan kujerar da yake kwance Mubina ta haye kanshi tana masa wani salo wanda ya kusa sumar dashi, ganin baya cikin nutsuwarshi yasa tafara yunkurin kwance masa belt Shi
Kamar a mafarki yayi firgigit ta mike zaune cikin zafin nama Mubina tayi "yar hantsile ta fadi kasa
Ya bude idonshi Wanda yayi mishi nauyi sosai yana kallon jikinshi yanzu yadawo hayyacinsa ya Dora jajayen idanshi kanta tana zaune kasan kafet itama ido yayi mici-mici sabida tsabar jaraba
Sai da ya kimtsa kansa tsaf ya mike tsaye yana gyara links din hannun rigarshi dake shart ce mai dogan hannu ranshi a mutukar bace ya nuna ta da hannu yace"wato abinda kike so kenan ko shiyasa kika matsa min sai nazo kinasa kiyi min fyade ko"
Mubina ta mike tsaya tana gyara yanayinta ta zabga masa harara tace"bana son sharri da lauya magana kai ne fa kace in gwada maka yadda nake sonka"
Kallonta yayi a dage yace"sabida ke kuma dama abinda kike so kenan ko, kin dai ji kunya"
"Bana San rashin mutumci Nasir, kai ne dai kaji kunya wallahi kazo kayi min kwance kana faman lumshe min ido tsaf Na fahimci abinda yake damun ka,
" To da kika fahimci abinda yake damuna dai a kace kiyimin fyade Dan tsabar iskanci ai Kya bari a daura auran tukkuna"
"Akwai Mara kunya irinka"
Mubina tafada tana huci, ita gadarata ta girmeshi
Jin abinda tace yasa ya tsaya yana kallonta yace"ni kike zagi"?
Kallonshi tayi taga fuskarshi a murtuke
Sai gabanta ya fadi tana jintsoran kar yace ya fasa, tasan halinshi da bakar zuciya
Tau inda inda bakinta na rawa ta gaza furta komai
Yace"mai maita abinda kikace min"?
Shiru tayi
Girgiza kai yayi kawai yana sharararta yace"wallahi kinci albarkacin Momyna amma da kinga abin mamaki, ki kaddara a ranki domin Momyna zan aureki domin kinsan ko da can din ma kece kike kidanki kike rawarki to ki taka a hankali in ba haka wallahi kikayi min rashin kunya hukunci zaki karba ki bar ganin kin girme ni ni babu abinda ya dameni,
Ki kiyaye"
Yana gama maganarshi yayi ficewarshi batare da ya saurareta ba
Mubina tayi sakato gabanta sai das!das!
Yakeyi baza ta manta ba tasan halinshi da muguwar baqar zuciya dole tayi taka tsan tsan dashi in ba haka ba zai iya sakinta ma ranar daurin aurensu
[08/06, 00:22] +234 808 996 5176: [07/06/2019 6:55 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*109*
Yau Asabar biyar ga watan biyar, yau ne ranar da a katsayar domin daurin aure, hausawa sukace komai Nisan jifa kasa zai fado.
Kofar gidan Dady cike da "yan uwa da abokan arziqi na Alhaji hassan, Abokan malam Yau ma ba abarsu a baya ba , guri yayi guri dady Mubina sai kai wa yake yana kawowa , maroka da masu vidio masu photo suna ta aikinsu guri ya kacame da hayaniyar maroka abin gwanin ban sha'awa Abdul bakinshi kamar ya yage sabida tsabar farin ciki yana cikin abokanshi sai gaggaisawa sukeyi, shi ko Nasir ya na gida a kwance babu yadda Momy batayi dashi ba kan ya shirya ya fito amma yaki
Wata mutsiyaciyar Mora ce ta keto gurin, hankalin kowa ya koma gurin.