← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 80

Sashe 36

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Saurin dauke kansa yayi daga kanta domin bayason yana kallon idonta da daddare,
Ta yunkura zata tashi takasa ,sabida yadda yayi mata rikon tsauri
Da kyar ta bude baki tace"ka sakar min jikina domin ni ba lalatarciya bace,kuma Allah ya isa taba min jiki da kayi"
Shiru yayi na minti uku yana dai dai ta nutsuwarshi domin kusancinsu da ita ya tayar mai da tsumammiyar sha'awarta ta shekaru da dama ,
Ya kwantar da ita sosai cikin kujera ,sannan ya fito ya maida kofar ya rufe ya zagaya mazauninshi ya zauna ya kunna motar,
Kai tsaye gida ya nufa da ita
Da kyar ta samu ta mike zaune jikinta a mace sakamakon tafiyar kafa da tayi abinda bata saba ba ,kallon hijab din ta tayi Wanda ya jike jagab da ruwa ,mamaki takeyi mai ya jika mata jiki haka
Ta kalleshi ganin ya nufi gida da ita tace"ka maryar dani asibiti domin aunty tanacan tana nemana nasani ko wannan hakki ma nasan Allah bazai barka dashi ba"
Babu abinda yace mata kawai ya cigaba da tukinshi batare da ya sauya hanya ba
Haka har suka je gida ,ya fito kawai ya kulle motar batare da ya kalli inda take zaune ba yayi shigewarsa part dinshi
Tafi minti goma a cikin motar tana saqawa tana kwancewa, sannan tafito jikinta duk yayi mata nauyi ta nufi part dinsu tana addu'ar Allah yasa kar taga Malam ya fito sallar dare domin yanzu ne lokancin tashinsa,
[24/05/2019 12:04 PM]
Binta Umar Abbale: A kuwa Malam Ya'u na tsugune a tsakar gida yana daura alwala,Maryam ta shigo
Gabanta yafadi ,addu'ata bata karbu ba
Kallonta yakeyi cikin mamaki yace"Maryama kece da dadaranan ,Allah yasa lafia
Domin ya kawo ko Baban gida ne rai yayi halinsa
Cikin ina ina tace "e nice Baba, aunty ce lallai sai na bawa uncle hakuri wai nayi masa rashin kunya,shine Na tawo gida nazo na bashi hakuri"
Cikin mamaki yake nazarinta yace"aunt taki ce tace"lallai kizo kibashi hakuri da daddaran nan,ai a bari sai da safe"
Daga kai tayi ,yace "shikkenan ai wuce ciki,zamu hadu da ita"
Maryam ta shige simi simi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki
Malam ko ya dade yana tunanin abin ,daga bisani ya daura alwalarsa ya mike daga gurin
Maryam ko tana shiga dakinta toleit ta shiga tayi wanka da ruwan zafi ,sannan ta dauro alwala tafito ta shirya tsaf ta hau kan dadduma ta tada sallah, tadade tana addu'oi a kan Allah ya kawo musu dauki ita da iyayenta ,sannan ta kwanta, tana tunanin abinda ya faru da ita a wannan dare
Fuskar Nasir kawai take gani yana mata gizo lokacin da tafarka daga suman da tayi ta ganta a kwance a jikinshi ga fuskarsa daf da tata, zuciyarta ra rinqa bugawa , tunda Allah ya hallice bata taba son wani kamar yadda take sonsa ba ,amma ta bawar zuciyarta sabida ta naganin yafi karfinta bayan haka kuma kwata-kwata bata sha'awar auran namiji manemin mata, sabida tana da kishi sosai shiyasa tun lokacin da taganshi da "yan matansa takeji kamar takashe kanta ta huta.

Babban abinda yake hadata dashi shine rashin ganin girman iyayenta da bayayi ita duk mutumin da baya ganin darajar iyayenta to itama bazata ga girmanshi ba,shiyasa take ganin girman Abdul sabida yadda yakeson ta yake ganin girman iyayenta baya gudun talaucinsu, duk son da takewa uncle baza ta bari ya wulakan tamata iyaye ba,
Tun tana yarinyar "yar shekara bakwai baxata taba mantawa ba lokacin uncle din ya zo Hutu daga da ya shiga gurinsu aunty take fada mata shine a uncle dinta to tunda ga lokacin takejin wani Abu a zuciyarta a game dashi har yanzu tanajin abun ,sai dai taki yadda abin ya bayyana ya fito fili sabida tasan Nasir din ba tsaranta bane
[06/06, 01:45] +234 808 996 5176: [25/05/2019 10:06 AM]
Binta Umar Abbale: [25/05/2019 9:49 AM]
Binta Umar Abbale: [25/05/2019 9:16 AM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*88*
To shima nasa bangaran tunanin da yakeyi kenan tun da ya taso a rayuwarsa yayi hulda da mata iri -iri amma bai ta ba cin karo da yariyar da take caza masa kai ba kamar Maryam tunda ya daura idansa a kanta a lokacin da yazo hutu lokacin tana shekara bakwai a duniya yakejin wata muguwar tsanarta a zuciyarsa, haka kawai yaji baya son ganinta ko gilmawarta a guri ,dalili kuwa tun ranar ya fara mafarki da ita in har ya kwanta bacci, duk tsawon shekarun nan bai fasa mafarkin taba, shiyasa yake kauce wa abinda zai hadasu guri guda, amma can kasan zuciyarsa yana jin wani matsanan cin kishinta wanda yake sawa yaji kwata-kwata baya kaunar ya bude ido ya ganta da wani namiji.

Haka yayi ta juye juye kan bed yana jin wani iri a jikinsa yarinyar ta tayar masa da sha'awa wacce ta sanya masa kasala yaji ko Dan ya tsansa baya son ya daga, haka yayi ta taune lebanshi na kasa idanshi yayi ja ya mike da kyar ya nufi toleit ya dinga zubawa kanshi ruwan sanyi ko yaji sauqin abin amma abu yaci tura tamkar karawa kansa wata sha'awar yakeyi ,gashi yayi alkwarin ba zai sake kusantar wata mace ba mutukar ba matarshi bace
Ya fito a daddafe ya fara laliban magani ya balli biyu ya sanya a bakinshi batare da ruwa ba haka yake tsotsa ya fadi kan bed din rigif!

Hannuwanshi dafe da mararshi
Wajan minti goma sha biyar abin ya fara lafa masa ,sai gumi yakeyi tamkar babu Ac a dakin a haka bacci ya dauke shi na wahala.

Washe gari Maryam da wurwuri ta tashi tayi Wanka tsaf ta shiga kchin ta na hada abin karin kumallo Malam ya leqo yace"kiyi sauri ki kammala mutafi ,dazu da'a suba aunty taki tayo waya hankalinta a tashe ,wai an ne meki an rasa, nace mata ta kwantar da hankalinta gaki nan a gida"
Gabanta ne ya fadi tana jin tsoran haduwarta da aunty ,sabida tasan dole sai tayi mata fada, tafi jin tsoran aunty ta a kan Malam sabida shi bashi da zafi kamar aunty
Muryarta a sanyaye tace"to Baba yanzu zan gama insha Allahu"
Ficewa yayi daga kchin din hannunshi rike da carbi yana ja ya nufi bakin get din
Nasir ya fito jikinsa sanye da kayan motsa jiki , ya nufi bakin get din
Fuskarshi babu yabo babu fallasa ya mikawa Malam hannu domin su gaisa kamar yadda suka saba
Mamaki Malam yakeyi sabida Nasir din a kwanaki baya bashi hannu
Sai ya mika masa hannushi shima yace"Nasiru ka tashi lafia"
"Lafiya arrama "
Nasir din yafada yana kokarin zare hannusa
"To masha Allahu
Jiya kuma sai naga wannan yarinyar cikin dare wai aunty ta ce tazo ta Baja hakuri, Dan rashin hankali, nace bata bari gari ya waye ba"
[25/05/2019 9:48 AM]
Binta Umar Abbale: Gabanshi ne ya fadi kadan yana addu'ar Allah yasa kar yarinyar ta fada masa abinda ya faru ita dashi
Sai ya gyara fuska yace"Owk ai ni bangan taba ma kwata kwata a jiya"
Cikin mamaki Malam yace"tace kuma tazo gurinka tabaka hakuri"
Girgiza kai yayi kai tsaye yace"batazo ba"
Kawai ya fice ya bar Malam tsaye a gurin yana binshi da kallo
Zama yayi kan bainci dake gurin yana al'ajabin wannan abu ,amma zai zaunar da Maryam din ya tuhume ta yasan yarinyarsa tsarkakkiya ce kuma ba zatayi masa karya ba.

Nasir kuwa Can wani guri ya nufa cikin estet din nasu da suke motsa jiki yafara motsa jikinshi babu abinda ya dameshi.
Chapter 36 · 0% Book details