← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 80

Sashe 32

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Duk suna zaune a inda ya barsu ,ya kalli aunt yana ya mutse fuska kamar bayaso yace"ya samu bacci yanzu alhmdullhi jiki yayi sauki sai dai zai kwanta anan tsowan sati domin samun kulawa ,amma a rika kiyayewa da cimarsa zan dorashi kan magani"
"Alhmdullahi Uncle Allah ya saka da alkairi kaji"
Aunt tafada tana kokarin mayar da hawayen da yakeso ya zubo mata
Ta cigaba da cewa "kayi hakuri kaji Nasir Wacan shashashar tana yi maka rashin kunya"
Bai ce komai ba ya kalli Momy tace "ni zan wuce Momy zan je in fidda kudi kin san mun fara business da aboki na Abbas ko zamu bude shakatawa a can bayan gari ,bayan haka kuma zan fitar da kudi za'ayo min odar motoci zan fara gwada wa in gani"
Cikin farin ciki Momy tace"Allah ya taimaka my son Allah yayi jagora"
Malam Ya'u dake tsaye hannunshi nannade a kirjinshi ,tun lokacin da Nasir yayi mishi tsawa jikinshi yayi sanyi sosai kwata-kwata bai ga laifin "yarshi ba sabida yasan kokarinta gurin ganin ta kare musu mutuchi cikin zuciyarsa yake nai mawarwa kanshi mafita dole ta fita ya nemi na kanshi ,domin ya tsaya da kakafunshi tunda a kwai sauran karfi a tare dashi ba zai yuhu ace ya zubawa Yaro kamar Nasir shi zai dinga da wainiya dashi da iyalinshi, in Alh Hussen yayi wannan daban da Nasir,yasan a kwai kudi masu yawa da har su kare rayuwarsu a gidan ,Wanda za'a iya dawainiya dasu ,to ma lokaci yayi da zai yi amfani da damarshi domin tsira da mutumci
Ya kalli Nasir din yana danne ,damuwar da take damunshi duk a kokarinshi na kula da amanar da akabar mishi,yace"Nasiru Allah yayi maka jagora Allah yayi riqo da hannuwanka yasa kafara wannan Sana'a a'sa"
Ciki ciki Nasir ya amsa ya Sakai ya fice daga Ofis din batare da ya amsa wa aunt maganar da take masa ba
Momy tace"sai hakuri nima in halin nashi ya motsa haka yake yimin in ta yi mishi magana yana share ni"
[06/06, 00:48] +234 808 996 5176: [20/05/2019 8:57 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*80*
Wata yayar aunty mai suna Rabi tace"ai babu komai Hajiya wallahi ,ai yaron ma yana kokari mu dai babu abinda zamuce sai dai muce Allah ya saka muku da alkairi ubangiji Allah ya jikan Alhji Huseen domin yayi mana abinda bazamu taba matan tawa dashi ba"
Momy tayi murmushi tace "babu komai Rabi ai duk yiwa kai ne , zamu cigaba daga inda dady ya tsaya ,domin mu cika masa burinsa,ni dai fatana daku dan Allah ku riqa hakuri kan dukkanin abinda zai biyo baya ta gefan Nasir ,wallahi ni kai na narasa in da ya sa gaba,kullum cikin bacin rai yake, duk ya canja hali"
Tausayin ta ne ya kama Ya'u yace"Hajiya ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu komai zai warware ai mun gode Allah ma , yanzu Nasir ta samu ba kamar da ba yana sallah cikin jam'i wannan shine mataki na farkon shiriya ,duk wasu abubuwa da yakeyi zai dai nayi in sha Allahu"
"To masha Allah Malam Godiya nake da wannan addu'a taka"
Momy tafada Tana jin dadin yadda Malam Ya'u yake kula da Nasir din kuma baya ,yadda ya sa bacin ran abinda Nasir din yake masa
Nasir yana fita ,suka ci karo da Abdul latif yana parking din motarsa a gurin da'aka tanada domin ajiye ta
Nasir ya dakata har Abdul din ya fito bayan ya kulle motar ya karaso gurin Nasir din Fuskarshi babu yabo babu fallasa ,ya bashi hannu kamar yadda suka saba,Nasir tace"ya akayi ne, ina ka shiga kwana biyu"
Abdul yace"ka manta nace da kai zanje Legos ko kasan na sami aiki acan wani babban kamfani ne suka dauke ni aiki wallahi, naje munyi intervio dasu kwanana biyar a can "
"Ok na manta wallahi amma na taya ka murna , sosai yaushe zaka tafi"
"Sai Monday ta sama amma ranar Sunday zan tafi da safe"
Tabe baki Nasir yayi kadan yace"yaya salary din ka ,yana da kyau in ce ko"
Abdul yace " alhamdullhi babu laifi , dubu Dari da sittin ne"
Dariya Nasir yayi yana nuna Abdul da hannu cikin tsabar iskanci da ya saba yi masa yace" ok kana nufin da wannan zaka iya rike mace ,ka tsaya sai wata za'a biya ka kudin da basu kai sun kawo ba ,ai da wannan aiki da ka hakura ,ka nema a nan kawai ,domin zai fi maka"
Abdul ya hade fuska yace"banason wulakanci da rainin hankali Malam ni rayuwata ban takura ta ba ina yin komai a tsari da sannu sannu komai mai zuwa ne
[20/05/2019 9:16 PM] Binta Umar Abbale: Nasir ya zakuda kafada alamun bai damu ba yace"ok tunda haka kake ganin zai fi maka shikkenan ai"
Kokarin bude motarsa yakeyi Abdul yace "ina zaka yanzu ,daga can gidanku nake naje gurin mutuniyar , sai naji mummunan labari wai Baban gida babu lafiya"
"Eh Hakane"
Nasir yafada bayan ya shiga motarshi yana kokarin kunna motar ya kalli Abdul latif fuskarshi ta rikide tamkar zaki a cikin dawa yana Neman abinci yace" wai kai har yanzu kana kan bakanka na auran waccan yarinyar"?

"Yes of course" Abdul din yafada babu alamun wasa a tattare dashi
Nasir ya girgiza kai yana cije lebansa na kasa minti biyu ,sai ya dago kai yana sakin wani murmushi daga ni kasan na mugunta ne , yace "banaso in fada maka abinda zai tayar maka da hankali ,a kan yarinyar wallahi tun wuri ina baka shawarar ka janye maganar auranta shine zai fi maka alkairi"
Cikin namaki Abdul ya zubawa Nasir ido ya gyara tsayuwarsa sosai yace"wai kai don Allah yau dai ka fada min dalilin da yasa kake a dawa da wannan Abu,kar ka manta da cewar dady kafin ya rasu ya bar wasiyyar tabbatuwar auran"
Nasir ya girgiza kai yana jin wani mugun bakin ciki ,a zuciyarsa har yanzu ,yana ganin Hoton Anwar da Yarinyar cikin Mota
Abdul yace"kai nake sauraro kayi shiru ,yarinyar nan dai na tabbata baza tayi zina ba shine dai karshen wanda zai sa inji kyamar auranta,bayan haka kuwa duk abinda tayi mai sauki ne"
Nasir bakinshi na daci kwata-kwata ba yaji tes din komai sabida bacin rai ya tashi motarshi batare da ya kara cewa Abdul komai ba ,ya fige mota tamkar zai banke Abdul din
Cikin zafin nama Abdul ya kauce , yana kallonsa cikin mamaki abinda yayi sai kace wani mahaukaci ,sai da yaga ficeawarsa sannan ya sauke ajiyar zuciya shi ma ya bar gurin
[06/06, 01:42] +234 808 996 5176: [21/05/2019 9:20 AM] Binta Umar Abbale: [21/05/2019 8:43 AM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*81*
Abdul sun jima da Maryam suna hira cikin mutumchi da so da kaunar junansu da zai tafi ya ke fada mata ya samu aiki a legos sabida haka in an daura auransu can zasu tafi, Maryam taji dadi sosai tayi masa addu'a gami da fatan alkairi ,ya fito da kudi masu yawa ya bawa Malam Ya'u da kyar ya karba yana masa godiya Abdul yace babu komai Baba nan Maryam take fada musu ai ya samu aiki a legos Momy tayi murna sosai haka aunty ,har bakin motarshi ta rakashi suna ta soyyaya tace'Ya Abdul dama ina Neman wata alfarma"
Yace "fadi kome Nene my Maryam in ina dashi zanyi miki"
"Dama zance ne mai zai hana ka fara Neman min aiki nima tunda dai takkaduna sunyi kyau ,inaso in dinga kula da iyaye na da "yan uwana ,sabida yanayin rayuwar nan"
Wajan minti biyu Abdul bai ce komai ba , kwata-kwata bashi da ra'ayin matarshi tayi aiki ko na menene ,to amma tunda ya Riga yayi mata alkwari babu yadda zai yi ,yace"kar ki damu Zanyi kokarin Neman miki aiki insha'allahu kinga da anan zamu zauna sai ki fara aiki a nan asibitin nasan Nasir zai dauke ki aiki,kuma da albashi mai tsoka"
Jiki a sanyaye tace"yanzu can legos din bazan samu ba"?

"A'a ba wai baza ki samu bane , kafin a dauke ki ne aiki ,tunda bamu da hanya kinga can ba kamar nan bace"
'Hakane"
Maryam tafada tana girgiza kai
Yace"amma ki bari tukkuna zanyi shawarar abinyi kafin in tafi ,in da yiwuwar in barki anan din shikkenan sai ki zauna anan din ko"?

Maryam ta daga kai tace"zan zauna mana ai komai lokaci ne"
"To shikkenan ,tawan Allah ya kaimu wannan lokaci"
Rufe fuskarta tayi cikin jin kunya tace"ameen"
"Yawwa ko kefa"
Abdul yafada yana wani murmushi cikin jin dadi
Nan dai sukayi sallama cike da so da kaunar junansu ,Abdul ya shiga Mota ya tafi,
Maryam ta koma ciki
Momy ta koma gida tare da Ya'u sabuda ,ta sa Uwani mai aikinta ta shirya abunci mai kyau sosai ,sannan tasa Nura drever ya kai musu can asibitin
Aunty ce da yayarta Rabi sai Maryam da ta nace sai ta zauna sabida babu yadda Momy batayi da ita ba a kan tazo su tafi taqi ,sai su Naf'iu ne suka bita, aunty ko kallon inda take batayi sabida har yanzu tana jin haushinta kan rashin kunyar da tayiwa Nasir
Ma'iakatan gurin ne suke ta kai kawo a gurin ko ina tsaf-tsaf tayal din gurin fari tas!
Chapter 32 · 0% Book details