← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 80

Sashe 39

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryam tafada a hasale tana nuna Dr Sofia da hannu cikin turanci tace"ko kunce ko baku ce ba dole Baban gida zai bar asibitin nan tunda ba Ku zaku bashi lafia ba , ni nan na isa in kula dashi tunda nima abinda na karanta kenan baku kadai Allah ya bawa ilimin ba,akin banza aikin wofi ,sai anyi magana ki dinga yiwa mutane turamci banza da wofi da wani rubban bakin ki da yagaji da shan giya da kayan maye"
[26/05/2019 12:07 PM]
Binta Umar Abbale: Shiru dakin yayi duk sun zubawa Maryam ido
Momy taji dadin abinda Maryam tayiwa Dr Sofia ,sabida ta lura yarinyar tana da girman kai
Dr Sofia ta kalli Nasir ranta a bace tace"kaji abinda wannan yarin take cewa ko, kamar ni zata dinga zagi tana fadawa magana ,ina kan aiki na"
Shiru yayi kawai baice mata komai amma ranshi yayi bala'in baci da abinda Maryam din tayi ,wato duk kokarin da yakeyi a kansu bata gani,ya lura zaqewarta tayi yawa amma zai taka mata burki
Fita yayi daga dakin batare da kara magana ba Dr Sofia tabishi a baya itama ranta a bace , duk suka bisu da kallo,
Maryam ta sauke ajiyar zuciya tanajin dadi ko babu komai ta'amayar da abinda yake damunta
Ko da Nasir ya fita ,kai tsaye bakin get ya nufa Dr Sofia Na bayanshi ya samu Sucurity ya kalle ta cikin turanci yace"kuje tare dasu ki sasu su fito da wannan yarinyar ayi waje da ita ,ita kadai nace kiyiwa haka banda sauran, zan fita ki kula da kowa ,sannan ki duba wannan takkadun da suke hannunki duk Wanda kikaga ya cancan ci a dauke shi aiki sai ki dauki sunanshi ,ki kirashi domin kiyi masa intervio"
Cikin jin dadin hukumcin da ya yanke tace" OK za'ayi duk abinda kace,sai kadawo"
Nasir ya shige motarshi ranshi a bace
Dr Sofia ita da Security din suka nufi cikin Asibitin
Suna zaune shiru kowa yana sakawa da kwancewa ,mussaman Malam Ya'u yana tunanin mai nene mifita a rayuwarsu Suka ji an turo dakin an shi go
Cikin bada Umarni Dr Sofia ta nuna Maryam da hannu tamkar wacce tayi gagarimin laifi cikin turanci tace "kuyi waje da ita"
Kafin Momy tayi magana tuni sunyi kan Maryam suna zare ido
Momy ta daka musu tsawa tace"kar Wanda ya kuskura ya taba ta wallahi ranku zai baci"
Daya daga cikinsu yace"Madam umarni ne daga oga"
"Ok Umarni ya baku Nasir din cewar kuzo Ku fita damu"?

Duk cikin turanci suke maganar.

Yace"No ita kadai yace mu fita da ita"
"To shikkenan Momy tafada rai abace tace nice Mahaifiyarshi ,ba Maryam ya kora ba ni ya kora kuma zan fita yanzu"
Dr Sofia tace"Mom kiyi hakuri , wan can yarinyar ya bada umarni a fitar masa ,ba ke ba please mom
Momy tace "rufe min baki bana son zan can banza"
Malam Ya'u dake tsaya jikinsa a sanyaye duk da bayajin turanci amma ya fuskanci abinda yake faruwa ba mai dadi bane ,gashi yaga ana nuna "yarshi da hannu Allah yasa bata wani laifi tayi ba
Ya tari Momy wacce take ta faman fada da turanci,yace duk da dai bana fahimtar abinda kuke cewa Hajiya ina ganin abin duk bai kai na daukar zafi haka ba,ina ganin tunda Baban gida yasamu lafia zamu bar asibitin nan mungude da karamchi Allah ya kara girma"
Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "ai ko baka fada dole zamu bar asibitin nan yanzu, shi kuma Nasir din zaizo ya same ni"
Abin mamaki duk da tsawar da Momy tayiwa Sucurty din ,ta kuma ce musu ita mahaifiyar Mai asibitin ce ,hakan bai sa sun kauce daga kanta ba su tsaye kikam !

Suna jira ta tashi.

Ita ko Maryam Sam abin bai mata ciwo ba domin tasan Dan ya bata mata rai ya yanke wannan hukunci, sai ta kalli Momy tace "kiyi hakuri Momy wallahi ni kaina narasa wace irin qiyyaya uncle ke min amma babu komai"
Momy tace"ai ke zan bawa hakuri Maryam kinji ,babu komai zaizo ya same ni, tafada tana mikewa tsaye tana gyara zaman hijab din ta
Su aunty ma mikewa sukayi ,Yaya Rabi tana kokarin tashin Mahaifin nata, Malam Ya karaso gurin ya tasheshi ya mike jikinshi babu kwari sosai ,sai ya jin ginar dashi a kafarshi suka na kokarin fita daga dakin
Suma suka biyo bayansu kowanne da rai a bace, Dr Sofia ko babu abinda ya dame ta, haka wannan Sucurty suka tasasu a gaba har sai da sukaga sun fice daga asibitin sannan suka dai na binsu sai kace wasu masu laifi.
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [26/05/2019 9:16 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*91*
Wannan abu da Nasir yayi ya 6ata ran Momy sosai, tunda take dashi bai taba mata abinda ya ta6a mata zuciya ba irin na yau,kwata-kwata ta lura Nasir bai san darajar dan'adam ba ko kadan ,giyar kudi tana dibanshi ya nawa kowa kallon kaskanci,amma wannan karon dole ta nuna masa bacin ranta, rai a bace suka karasa gida,dukkaninsu suka fito daga motar bayan Momy tayi parking,kai tsaye part dinta ta nufa ,batare da ta tsaya a gurin ba domin wani irin nauyi da kunyar mutanan takeji, gashi dai kullum Nasir din zai yi musu rashin mutumci amma sabida karamci da dattako basa nuna wani bacin rai a tare dasu,
To bayan Momy ta wuce Malam ya shiga da Baban gida wajansa ,su aunty suka gyara masa ko ina ,sannan suka fito,suka barshi tare da Malam Ya'u suna hira ,Baban gida ya kalli Ya'u yace"dama a kwai maganar da nadade inaso muyi da kai"
Malam Ya'u ya gyara zama yana fuskanta Baban gida cikin girmamawa yace"ina sauraron ka Baba"
Baban gida ya sauke ajiyar zuciya cikin alamu na marasa lafia yace"lokaci yayi da za'a ce ka tsaya da kafarka ma'ana ka dai na ci a karkashin wani , tun lokacin da Marigayi Alh yana raye naso ka karbi kasuwanci kamar yadda shi Alh ya so a lokacin ,kai ka nuna kafison ka zauna a bakin get ko"
"Kwarai kuwa Baba ni kai na sai yanzu nasan na tafka babban kuskure wallahi"
Baban gida yace"dama ba wani abin ake gudu ba sai mutuwa"
"Kwarai kuwa Baba"
"Yanzu abinda za'ayi a kwai wata gona ta can garinmu albasu zan siyar da rabi sai in baka kudin ka fara juyawa ko yaya kace"
"To madallah Allah ya saka da alkairi,wallahi nima tuntuni nake shawarwarin yaya za'ayi"
"Abinda za'ayi kenan ai "
Baban gida yafada yana gyara kwanciyarsa
Nan dai Malam Ya'u yayita godiya suka tsayar da maganar cewar zasuje can albasu garinsu Baban gida domin a siyar da gonar sabida sauran "yan uwanshi duk suna can shine kawai yafito nai man abinci cikin gari a wancan zamanin har ta kaishi da yin aure ya haifi su Yaya Rabi da aunty Lokacin da mahaifiyarsu ta rasu aunty da girmanta a lokacin Yaya Rabi a kayiwa aure ,to bayan rasuwar mahaifiyar tasu sai auntt ta cigaba da kula da mahaifinta har lokacin da ta auri malam Ya'u
Malam Ya'u ya gyara masa kwanciya ya mike ya fito cikin farin ciki ya nufi bangaransu,
Ya na zuwa ya sanarwa da aunty halin da a ke ciki
Suma sun goyi da bayan haka sabida dama tun dazu abinda suke tattauna kenan
Maryam tana kicin tana aikin hada musu abinci ita ma taji dadin wannan lamari dama burinta bai wuce ta dai na ci a karkashin Nasir ba ,Dan rainin hankali.
[26/05/2019 9:38 PM]
Binta Umar Abbale: Nasir kuwa sai wajan sha biyu na dare ya shigo gida.

Kai tsaye part dinshi ya wuce domin yayi wanka ga wata irin yunwa yana ji
Momy tana falo tana jiran dawowarsa ,tana jin shiguwar motarsa ta mike ta nufi part din nasa.

Fitowarshi kenan daga toliet yana tsane kanshi,Momy ta tura kofar dakin nashi ta shiga da sallama
Abin ya bashi mamaki ganin Momyn shi da daddaran nan ,sai ya tsaya yana kallonta ta karaso ta zauna gefan gadonsa ita ma shi take kallo kamar yadda take kallonsa
Yace"Momyna lafiya dai ko"?

Tace "lafia lau tunda gani ka ganni Allah ya dawo dani gida bayan korar karan da kasa akai mana"
Cikin namaki yaje ya zauna kusa da'ita yace"Momy waye yayi miki korar kare,ban fahimci abinda kikecewa ba"
Tace"dazu bayan fitarka waye ya turo Sucurty suzo su wulakanta Maryam"
Momy"wacece Maryam"
" Ok zakayi min rainin hankalin da kasaba ko"?

Momy tafada a fusace!

Dauke kai yayi yana nazari na minti biyu yace"Momy please ban fahimci me kike nufi ba wallahi , dazu dai nasan nasa Dr Sofia tasa ka Sucuty su fitar da yarinyar nan ganin tana nema tayi mana katsaldan a kan aikinmu ,ba na son bacin rai shiyasa na yanke wannan hukunci"
Momy ta hararashi tace"wannan ba hukumci bane wulakanta mutum ne abinda kayi Sam Baka kyauta ba, kamar ni ince musu ,su kyaleta suka qi ,ji sukayi mana tsaye a ka har sai da sukaga mubar asibitin sannan suka dai na bin mu sai kace wanda mukayi gagarimin laifi"
Ranshi ya baci jin abinda Dr Sofia tayi kafin ya tafi sai da yafada mata ga yadda zata yi
Yace" Kiyi hakuri Momy ba laifinsu bane ,ni na isa in sa a kore ki Momy ke nake gani nake jin sanyi a zuciyata Momy nayi missing din Dady Sosai ,kwalla ta taro a idanshi yana kokarin mayar da ita,amma sai da ta fito ,ya sa Dan ya tsanshi daya yana daukewa
Ita ma Momy zuciyarta ce ta karye sabida Nasir ya fama mata mikin da yake cikin zuciyarta ,sai tafara goge hawaye
"OK" "OK Momy yi shiru na dai na please ki dai na Dan Allah"
Nasir yafada yana marai rai cewa
Cikin kuka Momy tace"My Son Bakajin magana ko,ka manta wasiyyar dady din ka"
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [27/05/2019 1:19 PM]
Binta Umar Abbale: [27/05/2019 10:35 AM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*92*
Momy ta cigaba cewa My son baka kewar mahaifinka, da ka kayi missing din nashi da gaske da baza ka wofintar da wassiyar shi ba, nima kanaso ka dora hawan jini ,ko ka kasheni in na mutu ka huta ai"Momy ta karashe maganar tana goge fuskarta.
Chapter 39 · 0% Book details