← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 80

Sashe 10

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tamkar wani Dan dambe haka Nasir yayi kansu a hautsi ne ya daki kafar Anwar da wani mitsayacin takalmi mai ta yoyi da yasanya a kafarshi yanzu domin Wanka ya sakeyi gami da sake wani dressing din domin sake fita,
Ya San ya hannusa guda ya dauke Maryam daga kan Anwar din yana zaginta da turanci ya fidda hannu ya dinga gaura mata tafi tamkar Wanda Allah ya Aiko shi,
A kasalance Anwar ya mike yana kokarin kwatar maryam daga Hanunsa, Ya kai masa wani kutofo,yayi taga taga zai fadi ya tsaya da kafaunsa
Da sauri Abbas da Abdul latif wadanda kecan falo suka karasa gurin domin hayaniyar da sukaji kadan daga can bedroom din Nasir Dan a zatonsu ma ko fada ne ya hautsine a tsakaninsu su biyun.

Ya kara daga hannunsa zai kara kai mata mari Abdul latif ya riqe hannun yana masa wani irin kallo,
Bai ce komai ba ya mai da idonshi kan Maryam dake takure idon ta na zubar da hawaye,
Fizge hannusa yayi yace da Allah malam sakar min hannu wannan "yar iskar yarinyar ni zata nuna wa iskanci Dan Ubanta a dakina za ta kwanta a jikin wannan Dan iskan yafada yana nuna Anwar dake zaune da jiki a mace domin ya Riga yagama kwadaituwa da yarinyar,
Cikin mamaki Abdul ya maida idonshi kan maryam a karo na biyu ,yace" Maryam mai yakawo ki dakin nan ina kuma hijab din ki?

Cikin kuka tace Momy ce tace nazo na sharewa Ancle dakinshi nayi masa gyaragare wallahi,
Ajiyar zuciya ya sauke yace "zo ki wuce ki tafi kin ji ko" dakin Nasir din tayi niyar komawa domin dauko hijab din ta,
A zabure!

Yayi kan ta yana mata wulakantacan kallo ,ya tsare kofar dakin ,"yace get Out" joya wa tayi da nufin tafiya Abdul ya dakatar da ita ,ya kalli Nasir da rai a bace yace wallahi baza ta fita a haka na mahaifinta na waje a zaune Sam bai dace ba hakan"
Tsaki Nasir yaja ya shige dakinsa
Anwar yace"wai kai ina ruwanka da yarinyar ne malam naga fa kana min shishshigi a kanta wai ko son ta kake yi ne iyi ,Wallahi tunda na kwadaita da ita sai na biyawa kaina bukata ko ta halin yaya ne kai dai kafi kowa sanin halina"
Karaf!

A kunne Nasir lokacin da yake fitowa daga dakin sa hijab din Maryam a qasa yana ja wai bazai dauko da hannunshi ba,
Gabanshi ne yafadi jin Furucin Anwar yariga yasan halin sa ciki da waje tamkar maye yake gurin mace zai iyayin komai a kanta Dan ta wani fanni na yafishi son mata tunda shi ba kowace mace yake kwanciya da'ita bah'
Ba Dan komai ya hana Anwar cika burin sa ba a yanzu sai Dan in ya tuno da hallacin da Uwar yarinyar tayi masa ,bazai taba cutar da jinin Aunty shi ba zai bari a cuceta ba yarinyar taci darajar malam Ya'u da Aunty shi ,Amma da badan haka ba a gabanshi zai sa Anwar ya yagalgala masa ita wallahi sabida tsabar haushin da take bashi taqi fita daga rayuwarsa kullum ya kwanta sai tazo masa cikin baccinsa ta ida nunta masu ban tsoro a cewar sa ,shine dalilin da yake ganin anya Aunty shi ba mayya ta haifa ba ,tunda shi maye ruwansa da ita,
Da sauri Abdul yaje ya cire hijab din daga kasan kafar Nasir din ya mika mata yace"maza ki sa kinji ko kiyi tafiyarki Allah ya saka miki"
Da sauri ta karbi hijab din hannuta na rawa ta zira tayi hanyar fita daga dakin tana Addu'ar Neman tsari gami da godewa Allah da ya tsareta daga sharrin su Nasir
,,,,,,,,*
YARO DA KUDI*
WRITTEN BY*
_*Binta Umar*_
~*Maman Abdul Wahabu*~
~*Mrs Ahamad gwadaba*~
_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176
~*DEDIGATED TO MY FAN'S*~
Abdul latif ya daura idonsa kan Nasir bayan fitar Maryam Ransa A mugun bace yac" yanzu kai Nasir da kai za'a hada baki gurin cutar yarinyar can hakan da kukeyi yayi daidai kenan Abinda kuke a waje shine za kuzo gida kuyi mai Maryam tayi maka ?

Yarinyar da take bala'in tsoranka wane irin Abu Aunty tayi maka zaka saka mata da haka"?

Ya karashe ya Maganar yana sauke ajiyar zuciya cikin tsantsan bacin rai!!

Wani kallon banza Nasir yayi masa yana ya mutse fuska cikin izgili yace" kai karfa ka kawo min maganar banza mana ,Kai meye ruwanka da ita lokacin da kashigo A kai na kaga yarinyar da zaka daura min jakar tsaba ,mai zanyi da'ita ,Aba sai kace zabiya Mtssss!

Sam Sam Allah ya tsareni ita Dan Uwarta mai yakawo ta dakina anan fa naganta har da tube hijab tamkar tana dakin Uwarta" ya karashe maganar yana wani zakuda kafada Alamar babu Abinda ya dameshi,
Dauke kansa yayi daga kan Nasir din cikin bacin rai har ila yau jin irin Furucin da yakeyi Lallai Nasir yayi Nisa!

Ya kalli su Anwar yana girgiza kai yace "Wallahi mutukar Wani Abu ya samu yarinyar nan ta dalilinku sai nayi Shara'a da Ku A kanta , kai ne mai furucin ko ta halin kaka sai ka kauda kwadayinka a kan ta ,yafada yana kallon Anwar,yaci gaba da cewa Wallahi duk in da zanshiga in fita zan shiga a kan in Daukar mata fansa
Wani kallon banza Anwar yayiwa Abdul din yace"Kai ka isa ka hanani ae kata Abinda nayi niyya A kan waccan yarinyar Mara galihu "yar mai gadi da har kake wani tada jijiyar wuya a kai kai a suwa Kai din banza" ya karashe maganar yana furzar da wani huci mai daci Aba kinshi,
Girgiza kai Abdul yayi yana binsu da kallo daya bayan daya ,ya kalli Anwar din A karo na biyu ganin yadda ya zaqe da yawa har yake wani rantse rantse gami da cin Alwashi a kan Maryam din Tabbas idan wani Abu ya same ta Wallahi Anwar sai ya gane bashi da wayo
Yace"OK toum tunda ka rantse ae ga fili nan ga mai doki sai ka bada himma tanan ni kuma zaka San ka tabowa kanka Abinda baza ka iya ba kana maganar Maryam bata da gata to tana da gatan Allah dani in sha'Allahu Allah zai tsareta daga sharrinku ,kai kuma Nasir ya fada yana nunashi da hannu yace "wallahi duk Abinda ya samu Maryam ka tabbata babu rufin Asiri dady sai yaji domin kanajin furucin wannan Mara mutuncin a kanta kayi shiru wato kabashi goyan baya kenan ko mai yarinyar nan tayi maka da kayi mata wannan tsanar da har zaka bada hadin kai gurin cutar da ita, nafada na kara maimaitawa kar Ku batawa yarinyar nan rayuw.....

Kai!

Arrama da kata mana Dan Allah ya isa haka" Abbas yafada Wanda tun zamansa a gurin bai ce uffan ba ,sai yanzu
Ya gyara zama gami da zakuda kafada ,yaci gaba dacewa,Ubanmu ne kai wai da zaka titsiye mu kana zagi ina Ruwanka da duk Abinda zamuyi Rayuwarka ko tamu ,Malam kar kasake kawo mana maganar banza yarinyar daka ke wani tada jijiyar Wuya A kanta kana da Alaqa da ita ne kai idan baza kayi ba sai ka hanamu kai baka isa ba Wallahi
Kaii!!

Kauce Malam!!

Yafada A Fusace!

Tsaki Nasir yaja yana duba Wani Dan kareren agogo a daure a hannunshi bakwai shaura na Magariba Ya kalli su Abbas din yace "guys Ku tashi mu ware Ku rabuda wancan Komai Allah yace Annabi yace ko wa zai gayawa sanin Allah oho,"
Cikin Mutukar bacin rai Abdul ya fuce daga dakin yana Allah wadai da tur da wannan dabi'ar da Abokannanshi "yan Uwanshi suka jefa rayuwarsu ciki
Yana fita suka Kwashe da dariya gami da tafawa ,Nasir yace"ni narasa gane kan wancan gayan wallahi A kwai shiga Abinda babu ruwanka ko mai ya shafeshi da Lamarin yari yar oho"
Dariya Abbas yasa yace"mybe ko son ta yakeyi Dan ga Alamu nan sun bayyana"
Tabe baki Nasir yayi yace"tabbas da ya cika Dan Asara Wallahi yarasa wa zai so sai wancan yarinyar mai kama da ru66a66an tomatiri Allah ya sawaqe mai!!"
Dariya sukayi dukkaninsu gami da mikewa domin fita,Shima dariyar yasa yace"Wallahi nake gaya maka Ae irin su babu Abinda zakaji sunayi sai qarni in ka kusancesu Sam Sam yarinyar batayi ba yafada yana tabe baki,
Anwar yace"komai me takeyi sai na biya bukata ta a kanta Wallahi idan Uwar qarni ma takeyi bai da meni ba"
Gabanshi ne yafadi kadan ya Dan kalli Anwar din ta gefen ido ,jin Furucinsa har yanzu a kan Maryam din ,bai qara cewa komai ba har suka fice daga shashen gaba daya
Wata sabuwar mota suka shiga Nasir ya ware kida kamar yadda ya saba suka five daga gidan
,,,,,,,,,,*
YARO DA KUDI*
WRITTEN BY*
~*Binta Umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~
~*MRS AHAMAD GWADABE*~
_*WANNAN BOOK DIN NASIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176
*DEDIGATED TO:MY FAN'S*
Lokacin da Maryam ta fita daga dakin Nasir kai tsaye part din Mom ta nufa cikin Nutsuwarta tamkar babu Abinda ya faru.

Mom na kokarin hawa sama domin gabatar da sallah magariba ,sai ta dakata ganin shigowar Maryan din.

Cikin sakin Fuska tace" Maryam Kin gama ko?

Cikin Nutsuwarta kamar ko da yaushe tace"Eh Momy na nagama Farlour ne ban gyara ba sai gasu sunshigo game lokacin Sallar Magarb yayi zanje nayi Sallah".

Mom din ta gyara tsayuwarta tana kallon ta tace"ina fatan bai miki komai ba nasan Halin kayana"
Murmushi tayi kadan"tace Momy na kenan Mai zaiyi min Ancle din yace ne kawai in tafi tunda sun shigo "
"Daga haka fa" Momy tafada tana mata kallon tuhuma.

Sai ta duburburce tana tsoran kar Momyn ta Fahimci Abinda yafaru,yanzu gashi ita kuma qarya ba dabi'ar ta bace,
Kallon zargi Momyn take mata race"kifada min gaskiya daughter kinji ko"?

"Ok zo nan Muje sama Muyi sallah a nutse sai ki fada min"
Momyn tafada gami da karasowa inda take tsaye ta kama hannunta suka haura Sama inda dakunan su suke.

Bayan sun idar da sallahr ne Cikin Nutsuwa Mom din ta kalli Maryam tace"kifada min idan ya dake ki kamar yadda ya saba kinji doughater"
Shiru Maryam tayi tana wasa da hannunta.
Chapter 10 · 0% Book details