← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 80

Sashe 42

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ya sauke yana Dan ya mutse fuska yace"Wallahi Momy nagaji ne ,ayi ta abu daya babu ji babu gani ,yau hutawa zanyi duk mai son ganina sai gobe karfe biyu na rana, domin sai nayi bacci a gida,
"Dole mana kai ne can kai ne nan ,abincin kirki ma baka tsaya kaci, ya kamata ka huta ,tukkuna"
"Momy yanzu ma yunwa nakeji wallahi'
Yafada yana kokarin mikewa tsaye
Momy tace "ai kuwa yanzu sai dai in shiga kchin in girka maka da kaina ,domin nasan baza kaci towo ba"
"Momy wa yafada miki , sosai zanci indai miyar tayi min"
Momy tayi dariya tace"dole ma tayi maka miyar ,sabida wacce tayi gwana ce a fannin girki"
Tare suka isa daining din suna hira cikin fahimta Momy ta hada mishi towon semo miyar agushi taji wadataccan naman
rago ga man shanu ,sannan ta hada mushi farfusu na kan rago gefe ga lemo da ruwa mai sanyi
Nasir yaji duk yunwar da yakeji ta taso sabida yadda kamshin girkin ya cika masa ciki
Yayi bisimillah ya fara ciki
Momy tace"wai cin towa da cokali my Son, yanzu kana jin dadi a haka"
Dariya yayi kawai bai ce mata komai ba, ya cigaba da cin towonshi, yau sha rabon da ya samu abinci mai gamsarwa irin na yau
[29/05/2019 2:22 PM]
Binta Umar Abbale: Dama shi ba gwanin cin abinci bane yafi kauri gurin kayan zaki mussaman madara da kalolin buscut da alawa , bini-bini shan sweet tamkar yaro karami , sai Momy tayi da gaske yake tsayawa yaci abinci ko lokacin da yana yaro ,dama in ya shiga gurin aunty itace take bashi girkinta irin na gargajiya lokacin, yai taci yana santi ,amma yanzu yau sharaban shi da yaci girkin aunty.

Yanzu da kyar ya cinye daya duk kurarin yunwar da yakeyi , bawai Dan towon ya gimshe shi ba, sai Dan cikinshi ya cika ,ya dauki tissue ya goge bakinshi , fuskarshi dauke da fara'a yace"Momy abincin nan yayi testing sosai da sosai naji dadinsa"
Momy tayi dariya tana nuna plate din tace"duba Dan Allah sai kace wanda yaci malmala uku ,har yaushe ka gama jin testing din nashi"
"Momy ji nake cikina kamar ya fashe yanzu, na koshi sosai amma ki aje min mai ma a kecewa"?

Yafada yana kallonta
Momy tace "dumame kakeso kace"?

Ya saki dariya yana sosa kunnenshi da key din motarshi yace"yeah Momy ki aje min shi gobe ina tashi in karya dashi"
"Allah yasa"
Momy tafada tana tabe baki
Yana dariya yace"da gaske nake Momy wallahi zanci"
"To mai nace MySon Allah ya kaimu lafiya"
"Ameen Momyna"
Momy ta gyara zama tana kalonshi sosai tace"dama a kwai maganar da nakeso muyi dai , Myson"
Cikin nutsuwa ya kalleta yace"Momy ina sauraronki Allah yasa ta alkairi ce"
"Jiya Kawun ka Alh Salisu yazo min da wata magana, wai kafin dadynka ya rasu ya ce dashi ya aura maka "yar sa Mubina, Hakane wai"
Shiru yayi kawai yana kallonta sabida rashin abin cewa da jin maganar da Momy tazo masa da ita,
"Myson kanaji na fa kayi min shiru kawai, ka sa min ido"
"Momy Idont know"
"Kamar yaya baka sani ba"
"Momy to mai kikeso ince miki ne,uhumm , kina ganin tunda dady ya rasu mutanen basu kara waiwayar inda muke ba, sai yanzu kawai zaizo miki da wani zancensa , Wanda daga ji ma kinsan tsari ne ,domin biyan bukatar kansa, Duk wani abu da sukeyi da qumbiya qumbiya duk in da labarinshi, sabida haka babu wannan maganar a iya sanina dai dady ya bar wasiyyar ko bayan ranshi a daura Auran Abdul da wan can yarinyar, ke ma a gabanki a kayi haka, amma maganar da uncle Salisu yazo miki da'ita kwata-kwata babu ita"
[06/06, 01:48] +234 808 996 5176: [29/05/2019 8:28 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*96*
Momy ta bata fuska tana kallonshi tace"ya zakace in daina maganar kwata-kwata babu ita, yanzu kana nufin haka zakayi ta zama babu aure,kullum a kayi maka magana sai kace kai kaza kai kaza, kasan abinda bazai yiwu bane in zuba maka ido ina kallo babu aure, ya zama dole ka fito da matar aure a wannan lokacin, in ba haka ba kuwa duk irin hukuncin da kawunanka suka yanke a kanka babu ruwana"
Momy ta karashe maganar tana sauke a jiyar zuciya.

Shima fuskarshi ya hade sosai, cikin zuciyarsa yace lallai yanzu za muyi fada da Momy.

"Momy wai duka shekaruna nawa ne da zaki bi ki daga hankalinki a kan rashin aure na, har yanzu ban kai 30yaers ba, ina 27 yanzu Dan Allah ki kwanta da hankali ,aure lokaci ne in yazo zanyi,amma ni babu wata Mubina da zan aura, sabida tayi min tsofa"
Momy ta harareshi tana Jan tsaki tace"wallahi babu ruwana kaje Ku karata da Salisu domin ba zaka jawo min zagi ba"
"Momy ki kyaleni dashi kawai"
Nasir yafada yana kokarin mikewa
"A'a ni dai bance maka kaje kayi masa rashin kunya ba domin na San halinka"
Dariya Nasir yake yana kokarin shiga bedroom dinshi dake falon yace" Wai Momy mai yasa mutum in ya kasance mai fadar gaskiya ,sai kiga bashi da farin jini, ni yanzu fadar gaskiyar da nakeyi yasa a ke ganin rashin kunya ta kuma duk suka bi suka tsaneni,
"Hummm My son bakasan duniya yanzu tazama abinda ta zama ba , Allah dai ya kyauta, kullum dai ni gargadin da nake maka shine ka rike gaskiya duk inda kake"
"Insha Allahu Momyna"
Yafada yana kokarin shiga bedroom din nasa
Tsaf dakin komai a muhallinshi in banda kamshi babu abinda yake tashi a dakin, ya zube wayoyinshi kan bed ya nufi toleit domin yin Wanka, wani irin bacci yakeji ,gashi yana so ya duba desktop dinshi sabida ya kwana biyu bai San me asibitinsa yake ciki ba ,ya San dai Dr Sofia zata kula dashi sosai to amma dole gobe ya leqa ya ga abinda yake faruwa
[29/05/2019 9:05 PM]
Binta Umar Abbale: Wanka yayi ya fito ya cwando 3qouter ba tare da yasa ko vest ba ya zauna gefan gado yana duba wayoyinshi , jikinshi yayi sanyi jin wani irin feeling dake ta so masa yanzu-yanzu , kwana biyu abinda yake ta fama dashi kenan ,duk abinda yakeyi daurewa kawai yake, wayar ya aje gefan bed din ya kwanta rigin gine gami da Dora hannunwanshi duk biyun a saman kanshi idanshi a lumshe,shi kadai yasan halin da yake ciki, a yanzu fargabarshi ma kar ya kwanta bacci yayi mafarki da wannan fitinanniyar yarinyar tazo ta dameshi cikin bacci, shiyasa yake jin tsoran yin baccin, ya mike da sauri ya nufi firji ya dauko lemon tsami ya rabashi biyu kawai ya sanya a bakinshi yana tsotsa, a halin da yake ciki ,shi kadai ne zai iya rage masa wannan abin da yake damunshi a mararshi, ko tablet din ba zai masa abinda lemon tsami zai masa ba, shiyasa yake ajeshi da yawa cikin firjin dakin nasa
Da kyar bacci ya daukeshi mai cike da wahala da mafarkin Maryam gashi yana yin sex da'ita cikin garari, Dan haka a firgice ya farka misalin Uku da rabi Na dare, ya farka ya mike zaune sai gumi yakeyi tamkar Wanda yayi tsere jikinshi yake dubawa yana Jan tsaki, duk ya baci, babu yadda ya iya haka ya mike ya shiga toleit ya tsarkake kanshi ranshi a mugun bace ya rasa wane irin bala'i ne wannan yarinyar ta zame masa karfan kafa ,ta shiga rayuwarsa ta dabaibayeshi sai kace aljana, shi yanzu ma tsoranta yakeyi wallahi kwata-kwata baya so ya ganta domin ganinta ba alkairi bane a gareshi.

Haka ya fito ya sanya jallabiya fara kar sannan ya shimfida daddama ya tada sallah raka'atanil fajri,
Ya Jima yana addu'a wanda duk rabi ta dadynshi ce Sosai yake zubar da hawaye sabida , shi kadai yasan bakin cikin da yakeyi in ya tuno dady yayi bala'in kewarshi sosai ,yana tausayin Momynshi Sosai da sosai, shiyasa yake biye mata da duk abinda tazo
Bayan ya dawo daga sallar asuba kwanciya yayi kawai, cikin ikon Allah bacci ya daukeshi mai nauyin gaske.

Momy ta sauko daga sama misalin 8:00 na safe Uwani na ta faman goge -goge bayan ta gama shirya daining suka gaisa da Momy cikin mutumci
Tace"Kinji motsin Nasir kuwa"?

Cikin nutsuwa Uwani tace"A'a Hajiya bai fito ba"
Momy tace"mybe bacci yakeyi domin yace yau bacci zai yini yanayi"
Uwani tayi murmushi tace"ai gwara ya huta kuwa *Yaro* mai halin Manya ,abinda yakeyi wallahi Dan shekaru hamsin ba zai iya ba,ai Nasiru yana da Hankali da sanin ya kamata kuma yana da adalci ga taimako hajiya, nake fada miki kwana uku da suka wuce yasa Nura ya kaimin kayan abinci komai da komai sannan ya Dora da kudi wai nayi cefane
Momy tayi dariya tana kallon Uwani tace"Allah Na gode maka daka nuna min zuwan wannan rana"
[29/05/2019 9:47 PM]
Binta Umar Abbale: Uwani ta cigaba da cewa "wallahi kuwa Hajiya nace ni mai zanyi da kayan abinci tunda komai ina samu a gidan nan,sai kawai na aikewa da kanwata Furera can qauye tayi ta murna har da kuka dama tana fama da mijinta , bayayin aikin komai ga yara biyar Duk ita take dawainiya dasu"
Momy tace"Assh!

Uwani amma baki taba fada ba sai yanzu,gashi kullum ana fitar da abinci a gidan nan mai yasa kikayi haka"
"Wallahi Hajiya sha'anin mantuwa ne kawai amma insha Allahu zan kiyaye"
Uwani tafada tana karkade kujeru
Momy tace"shikkenan yanzu in ya fito zan mishi magana ya sa ka sunanta a lis duk karshen wata sai a dinga fitar mata da nata"
Uwani ta rika godiya kamar ta ari Baki
Momy tace"babu komai duk Wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimakeshi"
Momy macace mai mutukar tausayi sosai kuma bata da girman kai ,tana zama da masu aikinta suyi hira cikin mutumci ,shiyasa suka saba da ita sosai.
Chapter 42 · 0% Book details