← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 80

Sashe 50

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anwar da indan dan ne suka fito cikin wasu "yan iskan kaya kananu kana ganinsu kasan babu mutumci suka tsaya jikin mota sunawa kowa kallon banza
Anwar ya tafito wani abokin Abdul din yana tambayarshi ina Abdul
Yace"bari in yi mishi magana"
Da kyar ya gano Abdul yana can cikin jama'a suna gaggaisawa yaji ana Jan hannunsa dole ya biyo bayanshi yace "kayi baki gaki su can"
Abdul tunda nesa ya gane Anwar ya karaso fuskarshi a sake yana mika musu hannu suna gaisawa
Babu walwala Anwar yace"na taya ka murna burinka ya cika Abdul yau zaka auri Maryam"
Dariya yayi yace"Allah ne abin godiya"
In Dan Dan ya zira hannu a aljihu ya zaro wani ambulam babba ya yaga shi ya fito da wasu hotona zasu kai kusan guda goma ya mikama Abdul
*innalillahi wa'inna ilaiyi rajiun*
Abinda Abdul yake nana tawa kan kace kwabo jikinshi ya jike da gumi lokaci kankani ya nemi miyau ya rasa a bakinshi, hotonan yake kallo daya bayan daya Maryam ce daga ita sai briziya da siket kanta babu Dan kwali ga Anwar yayi mata rumfa, Cikin mota gashi Anwar din babu riga abin babu kyan gani
Duk hotonan babu arziqi
Kafin ya dawo nutsuwarshi yaji muryar Abdul yana cewa "dama na fada maka sai dai kasamu ragowata
[07/06/2019 7:21 PM]
Binta Umar Abbale: Abdul idanshi yayi mugun ja tsabar bakinci tabbas babu abinda zai sa ya auri Maryam wallahi dole a warware
Wayarshi ce tayi kara hannunshi na rawa ya fito da ita daga aljihunsa Hajiyarshi ce jikinshi na rawa ya daga Muryar Hajiyarshi ya jiyo tana cewa "Abdul mutukar nice na haifeka kar ka sake a daura maka aure da wannan yarinya babu ni babu kai"
"Hajiya ko baki fada wallahi bazan auri karuwa ba zancanki ya tabbata"
'Abinda nake fada maka kenan yanzu-yanxu a ka kawomin wasu hotonta ita da farkanta suna fasikanci"
"E nima gasu a hannuna hotonan, Wallahi bazan auri ragowar wani ba"
Yafada a zafafe gami da kashe wayar
Yana juyowa yaga babu motar su Abdul a gurin
A fusace ya durfafi cikin jama'a sai huci yakeyi , kawai ya warci wata lasifika dake hannun wani maroki Wanda yake ta faman zabgawa Nasir kirari domin yaga fitowarshi gurin
"Ni Abdul latif Alhassan na fasa Auran Maryam Ya'u Maigadi domin bazan auri mazinaciya ba, sabida ni ban kasance mazina ci ba"
Tsit!

Guri yayi ana kallon kallo
Abdul ya watsa Hotonan cikin jama'a a fusace ya nufi inda motoci suke aje abokanshi suka rufa masa baya suna tu'ajibun wannan abu,haka suka ja motar suka bar gurin
Sai da suka fita daga Estet din sannan ya kira Mahaifinshi a waya yace"wallahi mutukar a ka daura masa aure da Maryam sakinta zaiyi sabida haka maganin ayi kar a fara.

Hankali Alhaji Hassan yayi mugun tashi sai zufa ce take keto masa Abokanshi suka kewayeshi suna tambayarshi ba'asi
Malam Ya'u yana zaune kanshi a kasa tunda wani abokinshi ya kawo mishi daya daga cikin hotonan Maryam da suke yawo a cikin Jama'a sai kukan zucci yake yanzu wai diyarshi ce cikin wani hali irin haka gashi kwata-kwata babu fuskar Anwar din sun rufe Dan kar a gani
Ya san Maryam tsarkakkiya ce Sam baza ta aikata ba yasan sharri ne
Wani Maroki ne ya dauki hotan guda ya na tafiya yana roko ya karasa har inda Nasir ke tsaye kusa da dady Mubina suna mamakin Al'amarin.

Mika masa Hotan yayi yace"Yallabai mai zakace a kan wannan Abu"
Nasir ya kalli hotan hannunshi, gabanshi yayi muguwar faduwa, kamar yanzu abin ya faro hotan Maryam ne da Anwar cikin mota kwanakin baya
*innalillahi wa'innailaihi raji'un*
[08/06, 19:50] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*110*
Da sauri ya karbi hotan ya yagashi gutsi-gutsi hankalinshi a mugun tashe ya shiga gida, ganin yanayi da ya shiga yasa Hankalin Momy din yayi mugun tashi kafin ta ankara ya fadi bakin kofar dakinshi sai wani irin nishi yakeyi tamkar zuciyarshi zatayi bindiga,
Da sauri Momy ya karaso gurin ta kamashi ta rike tana salati sai kokarin cire masa babbar rigar jikinshi take ganin yadda yake ta zabga gumi, bakinshi sai karkarwa yakeyi ya gaza furta komai gashi so yakeyi yayi magana amma ya kasa, Momy ta mike daga gurin hankali a tashe ta nufi kofar fita da kyar ya jawo maganar daga bakinshi yace"Momyna"
Momy tadawo gurin da sauri ta kama hannunshi ta rike tamau suka mike tsaye a tare
Kujera suka nufa ta zaunar dashi sai kace wani yaro karama tace"wai meye ne My son naga kashigo hankali a tashe"
Shiru yayi kawai yana wani tunani Wanda shi kadai ya Yankewa kanshi
"Momy wace irin wasiyya dady ya bari kafin rasuwarshi kan auran Abdul da Maryam"?

"Myson, banaso ana maimaita magana guda a gabanka fa komai ya faru, yanzu maiye ya faru kake wannan tambayar"?

"Momy Abdul ya fito cikin jama'a yafa cewar ya fasa auran yarinyar ko an daura sai ya saketa"
"Subahannallahi"
Momy tafada hankali a tashe ta cigaba da cewa "duk mai ya jawo wannan abin Kuma"?

Momy tafada cikin mamaki
"Momy sai na daure Anwar har karshan numfashinsa, Momy ni Anwar zai tozarta a idan duniya"
Nasir yafada yana wani huci, kafin Momy tace"komai ya mike da sauri ba tare da ya mayar da babbar rigar ba ya nufi kofa
Momy ta biyo bayanshi da sauri tana kiranshi , batare da ya waigo ba yace"Momy ki koma akwai jama'a a waje kar kifito Dan Allah"
Momy ta tsaya kawai tana bin bayanshi da kallo har ya fice daga gidan
[08/06, 19:50] +234 808 996 5176: [08/06/2019 2:31 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*111*
Jama'a duk sun kewaye Alhaji Alhassan wanda yake cikin tsananin tashin hankali da damuwa, wai shi Abdul zai tonawa asiri a idan duniya, shi yanzu wazai share masa hawaye gashi ya tara mutane bai sai mai zai dasu ba, yana tsaka da wannan tunani yaji muryar maroki yana cewa "Alhamdullahi Tabbas kai dan halak ne Dan gadon alkairi dan na gada ba Dan haye ba, Allah yaja zamaninka Yaro mai halin manya, yanda, Ubangiji Allah ya tayaka roko, Maryama kin tsinci dami akala, kukanki ya kare da izinin Allah, Nasuru ya karbi aurenki a madadin Abdul latif, Allah yasanya alkairi ubangiji Allah ya tayaka roko jarimin Namiji"
Kankace kwabo guri ya hargitse da hayaniyar jama'a da ta maroka kowa da abinda yake cewa
Lokacin da Alhaji Alhassan ya tsinkayi abinda wannan marokin yake fada wani irin farin ciki ne ya lullubeshi, lallai Nasir ya haifu cikin Dan uwanshi Alhussen, wai yau Dan da ya haifa shine ya tozarta shi a idan duniya, kuma yaron da suka dauka a matsayin Mara kunya shine ya rufa masa asiri, dama haka duniya take.

Dady Mubina yaji babu dadi a zuciyarsa ganin yadda al'amarin ya sauya amma da yake ya iya allonshi ko a fuska bai nuna ba a kaci gaba da hada-hada dashi.

Malam Ya'u ma yaji wani iri lokacin da yaji daga bakin marokin, Sam abin bai kwanta masa ba,domin yanzu shi lamarin masu kudin nan ya soma bashi tsoro.
[08/06/2019 3:11 PM]
Binta Umar Abbale: Ba tare da bata lokaci ba limamai da wakilai suka suka fara kasa goro da Alawa, cikin hukunci ubangija a ka fara daura auran Nasiru da Mubina sannan a ka daura da Maryam.

Nasir ko ya sha yabo da roka gurin maroka photo kuwa babu adadi duk inda ya yi suna biye dashi haka manyan mutane suka rika janshi suna photo dashi domin abin da yayi ya mutukar burgesu sosai suka dinga ya ba masa
Hayaniyar gurin ce ta fara sashi ciwon kai da ya lura idanun mutane ya Dan dauke daga kanshi kawai ya gudu gida
Yana shiga ya ga Momy a tsaye a harabar gidan fuskarta sai fitar da annuri takeyi, duk abinda ya faro a kunnenta ya faro Nasir bai taba faran tamata irin yau ba
Tun kafin ya karaso inda take tsaye ta cimmasa sai kawai ta rungume shi tsam tsam!

Shima ta sanya duk hannuwanshi ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya
Momy tace"My son baka taba faranta min ba irin yau Allah yayi maka albarka Myson ubangiji Allah ya tayaka riko, inama dady dinka yana raye ban san inda zai kai farin cikinsa ba, lallai ka cika Dan halak Myson Allah yayi maka jagora"
Dago tayi yayi daga jikinshi yana kallon fuskarta hawaye ya gani a kwarmin idonta sai ya sanya ya stunsa biyu ya na goge mata
Fuskarshi babu yabo babu fallasa yace"Momyna a yanzu babu abinda zanyi in faranta ran dady duk da baya raye a doran duniyar nan illa in kaunaci abinda yakeso Momy ni nasan irin kunci da damuwar da nake shiga duk lokacin da na tuna a irin yanayin da muka rabu da dadyna, wallahi ina shiga cikin matsanancinyar damuwa, bani da kowa Momy sai ke, nasan hakan da nayi kema zai faranta ranki ko"?

Momy ta girgiza kai kawai hawayen da take kokarin boyewa ya zubo a fuskarta Nasir ya fama mata wani miki a cikin zuciyarta
Tace"Myson ka Riga ka gama min komai a rayuwa ta, yanda kake min biyyaya in sha Allahu kaima "yayanka sai sun bika wannan nauyi kuma da Allah ya Dora maka Ubangi ya baka ikon yin rikeshi, insha Allahu Allah zai tsare maka rayuwarka da kai da zuri'arka, My son bazan taba dai na yi maka addu'a ba.

"Momy nagode sosai Allah yakara girma"
Yafada fuskarshi cike da murmushi
Tare suka shiga falo Momy na rike dashi tamkar wani zai kwace shi sai tsokanrshi takeyi ango babu babbar Riga
Ya zauna cikin kujera yana dafe kanshi yace"Momy in banda kin damu ni ina ruwana da wata babbar riga, ko dazu ma da nasa damuna tayi wallahi
Tace"Yanzu dole ka rika sanyawa sabida girma ya hau kanka"
"Momy wane irin girma kuma"
"Na aure gashi kana da mata biyu"
"Momy ko mata hudu gareni babu abinda zai hanani sanya kananun kaya"
Yafada yana tabe baki
"Nasan bazaka fasa halinka ba ai"
Momy tafada tana kokarin mikewa tsaye
Tace"a kawo maka abinci ko"?

"A'a Momy ruwan tea zan sha ya isa"
Yafada yana kallonta sabida yasan dole sai tayi magana
Hararashi tayi tace "baka isa ba kaji nafada mak....
Chapter 50 · 0% Book details