← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 80

Sashe 53

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wata yar Momynta ce ta hangi Momy tsaye jingene da mota ,abin ya bata mamaki yanzu yanzu sukaje can gidanta domin su mikamata Mubina a matsayinta uwar miji ba ta nan abin mamaki sai gata anan ko mai ya kawota oho
Har kusa da Momy ta karasa inda Momy take tace"Hajiya Aminatu ashe kina nan, yanzu yanzu mukaje domin mu mika miki amarya kamar yadda al'ada ta gadar ba mu same ki ba"
Cikin nutsuwa da sakin fuska Momy tace"wallahi kuwa ai sabani mukayi domin bamu Dade da fitowa daga gida ba nayi tunanin zan sameku anan, ai babu matsala ga "yar uwar tata ma yanzu zan hadasu in yi musu nasiha"
Momy tafada tana kara damqe hannun Maryam
Hajiya Abu wato yayar Momyn Mubina ta dago kanta cikin mamaki tana kallon Momy kana ta mayar da kallonta kan Maryam wacce sukayi kafada da kafada da Momy cikin zuciyarta tace wato ita ce ta dauko ta ma lallai yarinyar tana da fada a gurin Momy
Sai ta hau yaqen karya tana danne abinda yake zuciyarta kamar gaske tace"Masha Allahu haka yayi, bari mu bude part din Mubina sai mu shiga ciki tunda dai ita ce uwargida"
"To babu matsala"
Momy tafada cikin nutsuwa da dattako
Hajiya Abu ta kauce daga gurin cikin dinbun mamaki dole sai sun zage damtse kan Hajiya Aminatu in ba haka ba burinsu baxai cika ba a kan Nasiru dole ne su ci arzigi su bar arziqi a mazauninsa.
[11/06/2019 7:49 AM] Binta Umar Abbale: Momy taja tsaki abinda ba halinta ba tace"wallahi wasu mutanen suna bani mamaki wai sai mutum yazo ya tadda mutane a guri ya kasa gaidashi sabida girman kai Allah ya kyauta"
Ya Rabi tayi murmushi tace"Hajiya kenan aiko mutane kowa da irinshi sai hakuri"
"Allah ya sawaqe ameen"
Momy tafada tana kara kiran wayar Nasir din a karo na biyu
Gashi tana ring bai daga ba Momy jikinta ya bata babu lafiya amma ta barwa zuciyarta addu'a kawai take masa
Hajiya Abu ta dawo gurin a karo na biyu tace"Hajiya Bisimilah"
Dukkaninsu suka rufa mata baya
Farlo a cike sai hayaniya suke Momy ta nufi wani bedrom dake falon tace"a shigo mata da Mubina
Nan Hajiya Abu ta kamo Hannun Mubina wacce ke cikin kawayenta sai shewa sukeyi
Kwata-kwata babu kunya irin ta amare a tare da ita fuskarta tasha kwalliya kamar me ga wani uban gashin ido da tsa in ta kalleka tamkar wata aljana mayafin dake jikinta ma figigi ne sai taunar jingam takeyi abun dai babu arziqi
Cikin nutsuwa Momy take binta da kallo tana nazarinta tabbas Mubina bata da da'a ko kadan tana zaune kan kujera har da Dora kafada daya kan daya babu abinda ya dameta
Momy ta sauke ajiyar zuciya tace"Mubina sauko kasa ki zauna kusa da "yar uwarki"
Sai da ta bata lokaci sannan ta sakko kasa tana wani ya mutse-ya mutse
"Alhmdullhi Allah kai ne abin godiya daka nuna min wannan rana da raina da lafiyata"
Momy tafada tana sauke ajiyar zuciya ta cigaba da cewa "Mubina ga kanwarki Maryam a matsayinki na babba wacce kika darata shekaru da hankali ga amanarta na baki a matsayinta na "yar uwarki domin bazan kirata kishiyar ki ba sabida banason kuyi zaman kishi ke da ita, inaso Ku zauna
da juna tamkar "yan uwan juna, nasan Maryam yarinya ce Mara hayaniya in kika rike girmanki da kambunki na uwar gida zakiji dadin zama da ita"
"Ke kuma Maryam ki dauki Mubina matsayin "yar uwarki kada kiyi kuskure ta yi miki gyara kiyi mata rashin kunya duk da nasan ba halinki bane yi nayi bari na bari kinga Mubina ta girme ki nesa ba kusa ba , da shi kanshi Wanda ya ajeku, sabida haka ki bata girmanta, Ku zauna lafiya don Allah in kukayi haka kungama burgeni sabida zaku kwantar da hankalin gudan jinana wato Nasir gashinan na damka muka amanarsa Ku kulamin dashi"
"Momy duk abinda kikice naji insha'Allah zanyi kokarin bin maganarki"
Maryam tafada kanta a sunkuye
Mubina ko sai da tagama yangarta sannan tana tabe baki tace"Momy duk naji abinda kikace ni mutukar mutum bai shiga hurumina ba to babu ruwana dashi sannan Momy ki jawa Nasir kunne bana son rainin hankali mutukar yana son zaman lafiya a gidanshi to ya rika bani girmana"
Cikin mamaki Momy tace"ya baki girma ko ki bashi girma, ai yanzu sai dai ke ki bashi girma tunda a karkashinsa kike kuma duk inda namiji yake komai kankantarshi to babbane ko dako ka girmeshi, in na fahimci abinda kikeso kice kinaso kice min kinaso Nasir ya mutun taki ko a matsayinki na wacce ta darashi shekaru
[12/06, 14:48] +234 808 996 5176: [11/06/2019 10:31 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*116*
shiru tayi kawai bata kara tankawa Momyn ba, amma ta kudurta a ranta ba zata zauna tana ji tana gani Nasir yana rai na mata hankali dole zata zage ta kwaci "yan cinta a matsayinta na babbar yarinya mai aji da wayewa
Momy ta cigaba da yi musu nasiha mai ratsa jiki daga bisani ta ce su maida Mubina dakinta, itama Maryam din nata part din zata mikata
Haka dai suka mike duk jikinsu babu kwari danginsu Mubina ganin babu fuska gurin Momy
Suna fita harabar gidan Momy takara kiran wayarshi a karo na uku tana mamakin dalilin da ya hanashi daukar wayarta
Sai da takusa tsinkewa sannan ya daga gami da yin sallama
Momy ta sauke ajiyar zuciya tace"Myson kai ko ina ka buyu tuntuni ina Kiran waya shiru kaqi dagawa"
Numfashi ya sauke yace"Afuwa Momyna wallahi miting muka shiga shiyasa kika ji ni shiru amma gani kan hanya"
"Aa mukan baza mu tsaya jiran isowarka ba Wallahi tun dazu muna waje tsaye da yarinyar nan kabi ka kulle duk part din, ko ina kakeso mu ajeta oho maka"
Ganin yadda Momynshi ta harzuqa da yawa yasa yace"sorry Momah nawa part din a bude yake Ku ajeta a can dazu mantawa nayi lokacin da nashigo ban baki key din part din nata ba wallahi sai da naje gurin Mubina sannan nagani, lokacin kuma na makara mutane na ta jirana"
Momy ranta yayi fati ganin yadda ya karbi abun tace"ai ya huce Myson amma da rai na ya baci wallahi"
Dariya yayi kawai yace" Momy Allah ya huci zuciyarki"
"Ai na hakura"tafada cikin farin ciki, ta cigaba da cewa" kace part dinka a bude yake ko"?
Chapter 53 · 0% Book details