← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 80

Sashe 74

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'aga kai tayi cikin jin nauyin Momyn
"Ki kwantar da hankalin ki kinji ko my Dota daga yanzu kar ki k'ara yadda ya yaudare ki yace kizo kuje wani guri, ni nagane dalilinsa na tafiya dake hospital d'in kuma insha Allahu bukatar sa baza ta biya ba"
Momy ta karasa maganar tana kwantar mata da hankali
Tsaf Kyauta ta gama had'a komai ta haura sama inda suke,shi kuwa gajiya yayi da zama ya mike ya futa, ga wayar da Mubina take masa ta dame shi, duk ya rasa yaya zaiyi wani shashe na zuciyarsa yana nuna masa abunda yayi bai kyauta ba,yanzu Momyn shi ita kadai ta rage masa aduniya dole yaje ya bata hakuri in ta huce, ka tsaye gida ya nufu jikinsa duk babu k'wari,sai tunanin yadda zai bullowa al'amarin yake
Mubina na hakimce a farlo tayi shigar k'ananun kaya nonowan ta duk sun furfito ta saman riga,abunda yake rud'ar Nasir kenan, amma abun mamaki sai taga ya d'auke kansa ya tafi ya kwanta cikin kujera jikinsa babu kwari
Cikin kwarkwasa ta mike ta karasa inda yake ta zauna saitin kansa tana shafa sumar kansa had'e da fuskarsa sai wani lumshe ido take, tace"my only kana yi mun abunda gaka dama fa, tun jiya rabon da in sanya ka a idona, kana gurin waccan yarinuar da bata da mamora ajiki"
Idonshi d'aya ya bud'e yana kallon fuskarta, tayi masa inkiya da ido, wai ya kalli k'irjinta,aikuwa ya zubawa k'irjin ido sosai yana jin wani feeling a jikinshi amma yasan yanda yake cikin damuwar nan ko yace zaiyi wani abu ba iyawa zai yi ba, yana leb'anshi na k'asa ya lasa yace"my Mubina yunwa nake ji sosai ki bani abunci"
A haukanta wai ta zaci yunwar sex yakeji saboda tasan halin mutumnin ta,kawai sai ta d'ora hannsa kan k'irjinta tana shafawa tace"muje in baka abunci ka"
Cire hannunsa yayi da sauri yana k'okarin mikewa zaune yace"dallah matsa, ina miki maganar ina jin yunwa kina min wata magana sam baki iya komai ba ke kam
Mik'ewa tayi tace"to shikkenan bari in je in maka girki, ni kasan ban iya komai ba, sai dafa indomee"
"Sai ki koya kuwa domin nagaji da cin abunci a waje, sai kace wani mara galihu, mara gata
Kchin ta wuce tana wata irin tafiya, ya dauke kansa yana duba wayarsa numabar Maryam ya kira, Momy ce, ta mik'a mata wayar tace" Momy ancle ne"
Momy tace"me zai miki to, ki kyaleshi kawai,sai kin horashi tukkuna"
Wayar ta aje har ta katse sai ya kara kira nan ma taki dagawa, sai da ya kira sau uku bata d'aga ba shi kansa sai ya rasa meye dalilin da yasa yake kiranta wata zuciyar tace kace mata me to, haka ya kashe wayar yana d'acin rai,l
[26/07, 21:47] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*160*
Yana nan zaune yana fama da waya cikin rashin sanin abun yi Mubina tq shigo farlo hannuta rike da wani plate wanda ta zubo jolop d'in taliya, taji nama gashi nan duk a sama, da tattasai, duk sun batso, ta aje masa kan k'aramin teble d'in gabansa taje ta d'auko ruwa da lemo, duk ta aje masa yana budewa yaji karnin nama zuciyarsa ta fara tashi yayi saurin rufewa ya mike ya canza guri, Mikewa tayi ta koma kusq dashi tana fari da ido tace"me yasa baza kaci ba, gashi nayi maka kokari, fuskarshi babu walwala yace" me ya aiki ni cin abunci da zan kwana ina amai, ai da wannan abuncin naki gwara in kwana ina ciye-ciye na, bai dame ni ba" tabe baki tayi itama tace"dama na fad'a maka ban iya wani girgi ba, nima
A ya mutse ya kalleta yace"Ok kina nufin haka kike zama da yunwa kullum"?

Girgiza kai tayi tace"ina cin abuncin gwangwani ne, ko in dafa indomee da kwai, ko in soya dan kali ko doya"
Tsaka yayi cikin jin haushin ta, hannuta ta zura cikin rigarsa tana shafa masa jiki sai lumshe ido take daka gani a bukace take, yana jinta ya share ta, yunwa yakeji sosai,kuma ya gaji da ciye-ciyen kayan zak'insa abu me gishiri-gishiri yake shawa'a lumshe ido yake kawai cikin tunanin neman mafuta
Ganin yadda yake lumshe ido yasa take ganin kamar wasan yafara shigarsa, sai ta fara tube masa rigar jikinsa, jikinta na kyarma!

Bude ido yayi yana kallonta har ta cire masa riga,ta sabule masa dogon wandon dake jikinsa ya zama daga shi sai k'aramin wando, jikinsa ta haye tana masa wani irin salo, wanda ya kusa tafiya da nuffashin sa yq bude ido da sauri, yana kallonta murya a carke yace"Mubina bana son wasan nan yayi tsayi dani dake, baki da juria, sannan ni kuma yadda nake haka babu wani abu da zan iya dan yunwa nakeji nafad'a miki"
Kamar zatayi kuka tace"dole zakace haka mana tunda kaje ka gama k'arar da k'arfin ka gurin waccan shegiyar mana"
Wani murmushi ya yana tura leb'anshi ns kasa a bakinsa, tsigar jikinsa ce ta tashi da ya tuno ni'imar da yake kwasa gurin Maryam yace"wa ya fad'a miki, in kinaso in kwana ina aiki ki bani abunci abunci in koshi, amma haka ni bbu abunda zan iya yi miki"
Cikin damuwa Mubina tace"kaid'in ne zakace dole sai kaci abunci sannan zakayi abu bakayi niyya ba ne"
"Nafad'a miki tunda kika aure ni sai dai kiyi hakuri dani da halina, Magiya Mubina tafara yi masa duk tayi rauni, jikinta sai zuba yake kasancewar yau yini tayi tana bankar magani,
Dariya yake mata sosai yace" nifa abunda yasa nak'i bana so kiyi ciki ne kamar wancan yarinyar
Cikin kishi da damuwa Mubina tace"ai kaji rashin adalcin naka,wato ita saboda tsabar yin sex da ita harka d'irka mata ciki ko, hummm, to ni bashi ne a gabana ba, kawai ka biya min buk'atata, dama bana da ra'ayin haihuwa yanzu don kullum sai na sha pills saboda haka rayuwar mu zamu sha dakai"
Sai da ya gama ja mata rai sannan ya biya mata bukata, aikuwa yana gama wa yunwa tace gani nan, jikinsa har karkarwa yake, yayi wanka a gurguje, ya futo yana duba agogo daf ake da a kira sallahr magariba, wayar Momy ya kira sau biyu taki dagawa, sai ana ukun ta daga, tayi masa shiru, marairaice fuska yayi kamar yana gabanta yace"Momy yunwa nakeji please Momoh"
Ya karshe maganar kamar zaiyi kuka.

Shiru tayi masa sboda so take ta horashi tace"me zanyi maka to yanzu da kq kirani,yarone kai duk inda abunci yake kaje ka nema kaci"
"Momy in an idar da Sallah zanzo in ci anan
" Bani dashi karka sake kazo min gida kaji na fad'a maka, kasa matar ka tayi maka abunci mana"
"Momy matana tana gurinki fa"
Kashe wayar tayi ganin yanaso mayar da abun wasa.
*YARO DA KUDI*
*161*
Sai da akayi sallahr isha'i sannan ya nufi gidan Momy tare da Giss dan tsabar shiga irin na Mubina harda cewa kar ya dad'e ya dawo da wuri, bacin rai ma Sam bai bari yace mata komai ba.

Suna farlo dukaninsu har kyauta suna hira da kallo Maryam jikinta ya fara kwari ba kamar d'azu ba, tana cikin wata iriga mai hannun shimi doguwa ce,tana da tattara a gabanta, kanta da hula, yinin yau yini tayi cin d'ata Momy ta tashi Nura ya shiga kasuwa ya siyo mata da goba motsi kad'an Momy zata tambaye ta ko lafiya.

Sosai Momy take ji da ita
Sallama yayi ya shigo, daga Maryam d'in har Momy sai da gabansu ya fad'i kallonsa Momy tayi yana sanye da riga k'arama me yankakken hannu,da wandonta iya gwiwa, hatta da hular dake kansa hana sallah mahad'in rigar ce, kayan sun masa kyau ba kad'an ba, Kallo d'aya Maryam tai masa ta d'auke kanta,ita kan Allah ya jarrabe ta,da son wannan guy, kicin-kinci tayi da fuska Momy tayi tace"kai kuma meye zaka shigo mana gida kamar wani Wzkiy, dube ka fa, wannan sark'ar fa,na d'auka ka daina sanya su"
Zama yayi yana d'an bata fuska yace"Momy ki daina had'ani da wannan arnan don Allah"
"Dole in had'a ka dashi saboda kai dashi babu maraba, duba wasu iyayen sark'oki a wuyanka fa, kunnanshi ta kallah sai taga babu bari ma, tace"maza Ciro min wannan sarkokin tun kafin ranka ya baci, kana nema ka zama baba kana shirme"
Kyauta tace"aikuwa dai Uban gidana, ba girman ka bane"
Hararata yayi tai saurin sunkuar da kai kasa,yace "Momy wannan fa ba kafurci na aikata ba, yau sharabon da inyi irin wannan shiga sai yau,yau din ma dubi yanayin garin ana zafi sosai"
"Eh naji meye na sanya sark'a ai ta mata CE"
"Momah"!

Ya fad'a da damuwa a fuskarsa ya cigaba da cewe" duba ki gani ita kanta sark'ar set d'in kayan CE, kinga dole in sanya ta in ba haka ba zan b'ata dressing d'in,duba fa ki gani shi kanshi takalmin had'e suke" yafad'a yana nuna mata k'afarshi
Hararasa tayi tace"sarkin dressing da iya gayu ko american ma nan ta barka"
Murmushi yayi yana d'an Sosa tarin sumar dake kanshi wacce taji gyara sai kyalli take,da k'amshin mayuka masu tsada.

"Me kazo kayi mana da darenan haka"
Tafad'a kamar bata San abunda ya kawo shi ba
"Momy kin san abunda ya kawo ni fa"
Yafada yana karyar da kai,
Wai dole taji tausayinsa
Tab'e baki Momy tayi tace"meye amfqnin matar ka ne"?
Chapter 74 · 0% Book details