← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 80

Sashe 6

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai tuni Nasir ya shige part dinsa Sai ta dinga diri diri dan bata San in da yayi Ba tafi minti biyar a gurin a tsaya kamar ta koma da Abincin sai kawai ta karasa can bakin Get gurin Kakanta Baban Gida da Mahaifinta tsakanin Bakin Get din da Ai nihin cikin gidan A kwai "yar tafiya gaskiya tunda gidan Ba nawasa bane domain har kwalta ce a shimfide a wasu guraran .tana ajiyar zuciya takarasa gurinsu Malam Ya'u na ganinta yace ina zakije da kayan Hannuki ?

A Nutse tace Aunty CE tace in kai wa Wani Nasir tace nabi bayanshi gashi ban San inda ya shiga kafin Malam Ya'u yace komai Baban gida ya mike yana dariya yace muje in nuna miki gurinshi sokowa kawai nama Fasa auran dake tunda Ba kya ganewa"
*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:59] +234 808 996 5176:
*YARO DA KUDI*
WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)
Dariya tayi tana sun kuyar da kai Dan idan da sabo tasaba da irin wannan tsokanar da Baban gida yake mata na kaka da jika,
Part din Nasir ya Nuna mata yace ki shiga yana ciki kinji ko Tace to" Shi kuma ya juya ya koma Bakin Get din,
Tafi minti goma tana Aikin buga kofar dakinshi nashi shiru ba'abude Ba cikin gajiya ta zauna gefe tanaji kamar ta koma kawai wata zuciyar tasa ta daukar dutse ta fara bubbuga kofar dashi da qarfin gaske'
A hargitse Nasir yafito daga toilet daga shi sai gajeran wando jikinshi duk kumfa yana Fadin Wane Mahaukacin ne yake min wannan Dan iskan bugun kofar tamkar zai fasa min kune Dan iskanci ,shi duk a zatonshi irin Abokananshi na nane suka fara zuwa su dameshi jin cewar ya shigo kasar , kan yabude kofar sai mita yake yace ko waye basai ya kirani a waya ba meye amfanin Wayar tawa Mtsssss
Yana bude kofar yayi Arba da Maryam tsaye hannuta riqe da kwandon kayan Abinci Fuskarta ta nuna Alamun kosawa
Shi har ga Allah ya Manta da cewar Aunty tace yarinyar tabiyo shi da Abinci Wallahi sabida haka Wani banzan kallo yabi ta dashi yana ta6e baki yace ke wace irin daqiqiyar yarinyace iyi zakizo kinawa mutane bugu irin na Mahaukata Sabida gidadanchi irin naki
Kallonsa Maryam take cikin Mamaki sabida yadda yake yabata Mamaki ganin yadda yanzu nan a gurunsu yake ta dariya da wasa dasu Na'fiu Amma dubi yanzu yana kokarin zaginta,
Dake yarinya ce mai sanyin Hali sai tace dama Aunty ce tace in kawo maka Abinci Uncle kayi hakuri,"
Mtssss yaja yashige cikin dakin ya barta nan tsaye , ganin ya tafi ya barta sai kawai ta ajiye kwandon nan tayi nufin fita ranta a 6ace duk da take yarinya bata kaunar mutum mai wulakanci tana da gudun "yayan masu kudi sosai Dan ko A skull dinsu bata sakewa dasu kasancewar duk makarantar babu Dan talaka makarantace ta "yayan wane da wane Dan Alhji Huseen ne duk yake daukar nauyinsu ita da qannata,
Cikin tsawa yace ke mai kama da jinsun ifiritu dawo nan ki kwashe kayan Abinciki da dai bake kika kawo min sai inci, Ni Wallahi tsoro kike bani maza fice min daga daki yafada yana dauke idonshi a kanta lokacin da ta Joyo Cikin Mamaki Maryam take duk da yarintarta a lokacin bai hana ta Fahimtar meye ma'anar sunan ifiritu yake Nufi Ba, jikinta a sanyaye ta dawo da nufi kwashe kayan, sai kuma ya caja shawara yace ke barshi ma nafasa Fice min daga daki duk randa nakara ganin kafarki cikin dakinan sai nasa su Rambo sun cakalkalamin Namanki yana Nufin karnikan su na gidan,
Simi Simi Maryam tafice daga dakin kamar tayi kuka
Binta yayi da kallo lokacin datake kokarin fita daga dakin a Filice yace haka kawai kisanya ni Mafarkai da Faduwar gaba babu gaira babu dalili ki cuceni
Abinda yasa ya hanata mayar da Abincin yasan dole ran Auntynsa ya 6aci shiyasa basa haka da Auntynsa ko bazaici Abu Ba in tabashi ya kan qar6a ne kawai domin yafaranta mata,
*gaskiya bana samun commet a wannan book ko in dai nayi muku*
*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:59] +234 808 996 5176:
YARO DA KUDI*
WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)
Jiki a sanyaye Maryam ta koma 6angaransu Aunty tace meye kika dade be,?

Tun dazu haka, Cikin sanyin muryarta tace lokacin Dana fita ban ganshi Ba ,shine Baba ya nuna gurinshi,Aunty tace ai sai ki wuce ciki ke kinfiye Nawa da sanyi jiki shiyasa har kika kasa taddashi kin San a kwai isilamiyya ko?

Eh Aunty , to sai kuyi maza Ku kimtsa bana son makara,Aunty tafada tana shigewa kchin ita kuma Maryam din tashige cikin domin cire uniporm gami da yin Wanka domin shirin isilamiyya maryam yarinyace mai nutsuwa da hankali tana sanyin Hali Sosai Ana cewa duk mai suna Maryam tana da tsiwa banda wannan Maryam din ita ko Abu kayi mata da wuya kaga bacin ranta kuma a take a sannan zata manta batada riqo ko kadan,
Haka Abokan Nasir
Sukai tayin turoruwar zuwa jin cewa yazo hutu haka zasu shiga shashinsa su cika ai ta kallece kallecan finafinen batsa blue film gami da saka kide kide , Wani sa'in har mata ne suke zuwa irin "yan iskannan
Hankali Ya'u in yayi dubu ya tashi sabida ya lura tunda Nasir din yadawo baya fitowa sallah ckin jam'i kamar da ya lura yanzu Ba kasai fai yake tsayawa dasu Ba kamar da gaisuwace ka wai take hadasu ,domin yanzu Baban gida Ba kasafai yake zama a Bakin Get din Ba sabida girma Alhji Huseen ya ce ya huttashe dama rigima ce irin tashi tuntuni Alhaji Huseen din ya hanashi zama , yace Lailai sai ya zauna shikanshi Ya'u shi ya za6i zaman gurin ,Amma babu yadda Alhji Husen bai yi dashi Ba A kan yaje kasuwa ya bude masa shago ya zuba masa kaya ciki Amma yaqi yace zai zauna nan din , kawai sai Alhji Huseen din yasaka wani yaro ciki da sunan gurin na Ya'u ne duk cinikin da'ake a gurin nashi ne gaskya Alhji Huseen yacika mutumin kwarai,
A na ya gobe Nasir zai koma America ranar Asabar ne babu Aiki Mom' dinshi na gida tana zaune cikin kujera tasha kwalliyarta kamar ko da yaushe idonta sakaye da Farin tabarau irin na likitoci hannuta riqe da wani katon littafi irin nasu tana dubawa , Nasir yafito daga dakinshi dake cikin falon ,Cikin wata"yar iskar shiga wando iya gwiwa ya wani zazzago Dan har gajeran Wandonshi na ciki a nagani ke kyace wando zai sa6ulo yafadi ,Amma INA!a daure yake a qugunshi sosai da wani irin belt mai Masifar tsada ,Sai short' mai dogon Hannu cotton tana da kauri gaban rigar tambarin America ne As'ueal hannushi daure da wani tabkeken a gogo , Hakanan kafarshi sanye da boot Yayi bala'in haduwa,
Mom' ta dago kai tana kallonsa tace Ina zakaje haka My son, dubi time fa ya kamata ka zauna kayi shiryeshiryn Abinda bakayi Ba ko,
Kusa da'ita ya zauna yana kallon Agogo hannushi yace Mom' zanje ne muyi Sallama da Friends, dina Ai Ba wani dadewa zanyi Ba,
Murmushi tayi kadan tace A'a son nasan halinka fa yanzu kafita Kumar sai na ganka , wai kai Ba ka gajiya da yawace yawace ne?

Kasan halin dady ko"?
...................
*muje zuwa*
[23/04, 14:59] +234 808 996 5176:
YARO DA KUDI*
WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)
Momy' Manta da shi kawai kin San dole in fita muyi sallama da friends dina sai kawai in zauna nace miki bazan Dade Allah,
Momy tace dady naka za'a manta dashi Laila Nasir ka kanka kafi kowa sanin halinshi babu ruwana idan ta hadoku dashi,
Allah dady ne mom' yawa yake sai kace mace zan zauna a gida ai Ba zai yiwu Ba"
Ba nufinshi kai tazama a gida Ba duk inda zakaje kaje Amma ka daina dare a waje"
Hannunta ya ruqe yace Ok Mom karkidamu zan kula da kaina in Sha Allahu,,
Yawwa Abinda nakeso dakai kenan Mom din tafada Cikin walwala tace kaje My Son Allah ya tsare min kai"
Mikewa yayi shima Fuskarsa a sake ya manna mata kiss a kumatu , ita kuma tariqe Fuskar da hannunta tana dariya tace Allah ya shirya min kai yaro na,,
Yana tafiya yake Amsawa da Amin Momy ' sai nadawu ,Bai kai ga rufe bakinshi Ba yaji sunyi gware da Mutum, da sauri ya dago Kansa yana kallon Wanda ya bigeshi haka' Maryam ce Tsaye bakin kofa hannuta riqe da book dinta na makaranta , Tuni suka Watse a gurin sakamakon buguwar da sukayi da Nasir ,ta sanya Hannu ta dafe gushinta gami da tsugunawa domin kwashe Littatafan da sukayi dai dai a gurin,
Babu zato taji ya dago ta gami da gaggaura mata mari ka.

Hagu da dama, yana mata wani banzan kallo mai tattare da qyama yace, ke Aljana mai kika shigo yi nan iyi, Dan iskanci kin bigeni ban isa kibani hakuri kin wani hau kwasar littafanki sabida ga sa'anki ko?

Hawaye ne yake zubar Mata sosai tace kayi hakuri Uncle Wallahi banganka Ba' da sauri ya buge bakin yace Rufe mana rubabbaan bakinki ,Banza "yar kauye dama waddan nan idanun naki ai Ba naganin Mutane bane Naganin Aljanune irinki,,
Hakuri take bashi,Mom ta karaso gurin gami da qarbarta daga hannusa tace maye haka ,Son A ina ka iya mugunta domin Ba halayarka bace"
,,,,,,,
[23/04, 14:59] +234 808 996 5176:
YARO DA KUDI*
WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)
Yace Momy me yarinyar nan take shigowa tayiwa mutane a nan gurin iyi ?
Chapter 6 · 0% Book details