← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 80

Sashe 45

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ga dalili nan na fada maka"
Momy tafada
"Ouk sabida a auri "yarshi yazo har gida ya zageki"
Yafada a zafafe sai huci yakeyi"
"Cam down My son, ban fada maka wannan magana ba fa domin ta daga maka hankali, kuma bance in kaje kayi mishi rashin kirki ba, ni dai kawai ga umarnin da na baka"
Shiru yayi kawai ya koma ya kwanta hade da rimtse idonsa lallai dole yayiwa tufkar hanci domin kuwa babu shegan da ya'isa yazo ya runka tadaga mahaifiyarshi hankali wallahi ,sabida a halin yanzu ita kadai ce ta rage masa
[31/05/2019 9:28 AM]
Binta Umar Abbale: Momy tace"kayi shiru ba kace komai ba My son don Allah ka fitar dani kunya, wallahi nagaji da wannan cin mutumci"
Da kyar ya dago kanshi ya zuba mata idonshi wadanda suka sauya kala yace"Momy kinaso in auri Mubina ko"?

"Inaso mai My son"
"Ki kwantar da hankalinki insha Allahu zan aureta tunda kinaso"
Momy ta saki fuska sosai tace"Allah yayi maka Albarka My son Ubangiji ya shiga al'amarinka, yadda kake bina kaima In sha Allahu naka yaran zasu bika"
Mikewa tsaye yayi yace"Momy nagode da addu'a, zan shiga ciki"
"Ba zakaci abinci ba ne"?

Momy ta tambayeshi
Shiru yayi yana Dan murmushi
Itama Murmushin tayi tace"OK zakayi halin naka ko"
Sai ya saki dariya kawai yace" Momy ni tun a motana na cika cikina,in kinason saura in dauko miki"
"A'a rabani da kayan zaqi nan"
Momy tafada tana tabe baki
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [31/05/2019 4:58 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*100*
Murmushi yayi kawai ya wuce dakinsa, zuciyarsa sai zafi take yi, shi yarasa mai yasa mutane sukeyin haka, amma dole zai tari Uncle dinsa, ya kiyaye zuwa gurin Momynshi yana bata mata rai duk abinda ya dameshi yafi mutumci ya tunkareshi da maganar
Amma Sam!

Bazai yadda da bacin ran Momynshi ba.

Karfe goma shaura Abdul latif ya shigo gidan yayi parking din motarshi Nasir din ya kira a waya "hello Abdul din yafada bayan yaji andauki wayar
"Kashigo ne"?

Nasir din ya fada
"Eh kana part dinka ko kana gurin Momy"?

"Kashigo gurin Momy kawai"
"Ok"
Abdul yafada ya kashe wayar
Momy Na zaune cikin kwalliya kamar ko da yaushe, suka gaisa da Abdul cikin sakin fuska tana tambayarshi mutan gida
"Lafiya kalau Momy"
"To masha Allahu"
Nasir yana zaune kan kujera cin abinci ,hannunshi rike da waya yana latsawa Abdul ya karasa inda yake ya zauna kujara guda, gami da mika masa hannu
"Ya a kayi ne Alhaji"
Nasir yafada hannushi rike da hannun Abdul din
"Normal Alhaji"
Abdul yafada yana dariya
Yace"ya shirye-shirye"?

"Na kammala sai tafiya kawai"
"OK kasan abinda ya kawoni gurin ka"?

"Sai kafada"
Nasir ya fada yana danna waya
"Zan kawo maka takkadun Maryam ka duba don Allah ka dauke ta aiki a hospital dinka ,kasan a nan zan barta cikin Estet din mu Na family kafin in kammala ginina ,in kuma nasamu gurin zama zan dauketa mu tafi tare"
Ba tare da ya kalleshi ba yace"wacece Maryam"?

Abdul ya sha kunu yace"bana son iskanci fa"
Fuskarshi ya hade yace"ban fahimci wace Maryam kake nufi ba,ai shiyasa na tambayeka"
"Ok My wife dina yarinyar gidan nan"
Abdul yafada babu wasa a fuskarshi
Nasir ya dago kanshi yana kallonsa tsawon minti uku bai ce komai ba, ya saki Murmushi gami da cewa "a yanzu dai bama bukatar ma'aikata, in ma muna bukata to batayi ilimin da zata yi aiki a wannan asibitin ba"
"Mai kake nufi"?

Abdul yafada rai a bace
"Bana nufin komai"
Yafada hankalinshi Na kan wayarshi
"Look Nasir ka tsaya kayi min maganar da zan fahimta bafa na son wulakancin ka Wanda ka saba"
Abdul yafada ranshi a mugun bace
Momy ta waiwayo da sauri ganin yadda Abdul din yake daga murya tace"lafiya wai naji kuna magana Sama-sama"?
[31/05/2019 5:21 PM]
Binta Umar Abbale: "Momy wai sabida yaron nan bai da kirki nace masa, ya dauki yarinyar nan aiki a asibitinsa, shine yake fada min magana"
Momy ta kalleshi tana murmushi tace"duk abin ai ba Na zafi bane Abdul wace yarinya kake magana a kai"
"Momy Maryam nake miki magana fa"
"Ok Dota wai"?

"Eh Momy"?

Abdul ya fada yana mikewa tsaye ranshi a bace
Momy ta kalli Nasir yana zaune har'ila yau hankalinshi na kan wayarshi
Tace"Myson Dan Allah ina Neman alfarma nima ka dauketa aiki,wai maiye duniyar ne ,tunda dai Abdul din ya amince tayi ai shikkenan , Wanda ya taimaki wani shima Allah zai tai makeshi"
"Momy ki rabu dashi don Allah kar Allah yasa ya dauketa zan cigaba da nema mata"
"A'a duk baza ayi haka ba , ka koma ka zauna mu kashe magana"
Momy tafada tana kallon Abdul din
A gogo ya kalla yace"Momy wucewa zanyi wallahi banason abin bacin rai , zamu iya rigima dashi yanzu"
Cikin mamaki Momy tace"akan mace zakuyi rigima da Dan uwanka Abdul"?

Kunya ta kamashi sai ya sunkuyar da kanshi kawai
Momy tace"koma ka zauna"
Ya koma ya zauna kawai gami da dauke kanshi yaki yadda ya kalli Nasir din
Shi kuwa babu abinda ya dameshi
Momy tace"Myson "mai kace a kan maganar"?

Tafi minti biyu kafin yayi magana, daga bisani yace"Momy ni a yanzu bani da lokaci amma zata iya zuwa gurin Dr Sofia tayi mata intervio shikkenan sai ta ajeta a matsayin da ya dace"
"To ai babu matsala sai taje din"
Momy tafada,ta cigaba da cewa kai Abdul kaji abinda yace"
"Momy babu komai ai sai taje tunda naima takeyi,Allah ya rufa asiri"
"Ameen ameen"
Momy tafada ta cigaba da cewa dan Allah kar Ku yadda wata mace ta farraqa tsakaninku kunji ko"
"Momy kar kidamu insha'Allah"
Abdul din yafada yana mikewa da niyyar tafiya yayiwa Momy sallama
Bayan fitarshi Momy tace"don Allah my son ka rage girman kan nan gami da izza domin babu inda zata kai ka"
Dariya yayi sosai har sai da habarshi ta lo6a yana kallon Momy din yace" Momy yaya ake girman kai don Allah mutane da dama suna fadin haka a gareni , basu San cewar ni haka nuture dina ne ba"
"E ai duk da haka my son kana karawa da wani ni dai nace ka daina"
"Insha Allahu Momy kiyi min addu'a"
Momy ta zauna suka cigaba da hira cikin so da kaunar juna.
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [01/06/2019 5:11 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*101*
Nasir bai tafi America ba sai da yaje gurin kawunshi Salisu, sabida yadda yaga Hankalin Momy shi ya tashi a kan al'amari, nan uncle Salisu ya rika kwantar da kanshi yana rarrashinsa, da yayi hakuri ya aur
i Mubina, Nasir yayi mamaki ganin yadda yake kwantar masa da kai sai kawai ya basar , yace" magana ta wuce amma don Allah kar ka kara tayarmin da hankalin Momy domin abinda kayi mata ya daga mata hankali, zan wuce america, sati biyu zanyi zan dawo in yaso sai muyi maganar, Abin mamaki Dadyn Mubina ya dinga washe baki yana shi wa Nasir albarka nan Nasir ya tafi ya barshi sai mamakinshi yake,lallai mutane basu da kirki, wato in kana da kudi komai kafada dai-dai ne ,shi kanshi yasan ba don Allah uncle din nashi yakeso ya hadashi aure da diyarshi ba.
****
Yau satin daya da tafiyar Nasir ,Abdul ma ya tafi bayan ya kammala komai na maganar aure rana kawai ake jira,cikin so da kaunar juna sukayi sallama da Maryam.

Momy kadaici duk ya dameta sai ta fito harbar gidan ta zauna kan kujera kawai nan su Nafi'u suke zama da'ita suna hira Maryam ma sai ta samu gurin zuwa , siyi ta hira cikin fahimta
Ranar Momy ta tashi ta shiga ciki sai ta bar wayarta kan kujera Maryam na zaune suna chating da Abdul sai Murmushi takeyi kawai da'alama hirar tana mata dadi
Wayar Momy tafara kara da sauri ta kalli fuskar wayar, Myson ta gani yana yawo a fuskar wayar.

Gabanta ya fadi tayi kamar ta dauka wata zuciyar tace kar ki dauka, wayar ta katse kafin ta farga wani kiran ya kara shigowa,
Sai da takusa katsewa sannan ta daga batare da tace uffan ba
Ajiyar zuciya taji yana saukewa kafin taji wani irin voice da ya kusa sumar da ita a zaune Momynahhh"
Taji ya fada yana ajiye numfashi
Shiru babu magana
"Please Momy kiyi min magana mana yinin yau banji muryarki ba ayyuka sun dame ni"
Maryam tana ta kokawa da zuciyarta, jikinta yayi bala'in daukar dumi domin Nasir ya gama kashe mata gangar jiki, gaskiya tana bala'in kaunar Nasir
"Momy"
Maryam taji yafada da ainihin muryarsa ,sai taji kamar ma acikin damuwa yake
Sai tayi saurin kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya daki-dai
[01/06/2019 5:38 PM]
Binta Umar Abbale: Momy ta dawo gurin, ta kalli Maryam dake zaune tace"Dota na barki ke kadai ko"
Maryam tayi murmushi tace"A'a Momy chating nakeyi ma"
Wani kiran ne ya kara shigowa wayar Momy a karo na uku
Momy tayi saurin daukar wayar tana dariya
Tace"Myson yau nayi fushi ,nayi ta tsammanin kiranka tun da safe naji shiru nace Allah yasa lafiya"
Ajiyar zuciya ya sauke yace"Momy ina ta magana shine kika shareni ko"
Cikin mamaki tace"yaushe akayi haka, My son"?

"Yanzu Momy na kira sau biyu ina ta magana naji shiru"
Momy tayi murmushi tana kallon Maryam tace"ba nice na daga wayar ba Myson Dota ce wallahi ni Na shiga cikin gida"
Shiru yayi na minti biyu sannan yace"Momy mun gama magana da uncle ,in nadawo za mu tsayar da magana ina fatan haka yayi miki"
"Yayi dai-dai Allah yayi maka albarka"
"Ameen ameen Momyna"
Sukayi shira sama-sama sannan yayi mata sallama dama a cikin busy yake yanzu ma free ya samu shiyasa ya kirata sabida duk abinda yakeyi hankalinshi na kanta.

Bayan Momy ta aje waya ta kalli Maryam cikin murmushi tace"Dota Son'ya kira waya kinki magana mai yasa"?
Chapter 45 · 0% Book details