← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 80

Sashe 51

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallamar su Alhaji Alhasan ce ta katse Momy, fuska a sake ta amsa tana musu barka da zuwa
Momy ta nuna musu kujeru tace bisimillah Ku zazzauna
Cikin mutumci suka gaigaisa da juna, Alhaji Alhassan yayi gyaran Murya yana kallon Momy yace"tabbas Hajiya Aminatu kin haifu kuma kin haifi Dan halak, yafada yana nuna Nasir ya cigaba da cewa Wannan yaro ya rufa min asiri a lokacin da Dan Uwanshi Abdul latif ya so ya tona min a siri a cikin jama'a
[09/06, 00:18] +234 808 996 5176: [08/06/2019 7:23 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*112*
Alhaji Alhassan ya cigaba da cewa "Nasiru babu abinda zan ce dakai, ka rufa min asiri koma ka cika Umarnin da mahaifinka ya bari ubangiji Allah ya tayaka riko yayi maka jagora, Allah ya rufa maka asiri ya kareka daga sharrin masu sharri"
Fuska a sake Momy tace"wallahi babu komai Alhaji dama duk abinda kaga ya faru to dama haka Allah ya hukunta Allah ya rubuta Maryam ba matar Abdul bace shiyasa haka tafaru kuma dama mutum bai taba auran matar wani ba, ni dai abinda nakeso don Allah karkayiwa Abdul baki ka qaddara cewar dama Allah bai nufa Maryam zata zama matarshi ba"
"Duk abinda ya faru ya wuce agurina Hajiya shi kuma abinda yayi kanshi ya cuta ba wani ba gaba zaizo yana nadama, yayi nufin tozarta yarinyar mutane sai Allah ya rufa mata asiri dake batada hakkinsa"
"Momy ta sauke ajiyar zuciya sannan tace"wallahi Alhaji banji dadi wannan abu ba
"Allah yasa haka shi yafi alkairi"
"Alkairin kenan ma ki kwantar da hankalinki"
Alhaji Alhassan yafada yana kokarin mikewa tare da jama'arsa
Nasir ya mike ya biyo bayansu,
Da sauri Momy ta dauko masa babar rigarsa ta biyosu a baya ta mika masa wai lallai sai yasa
Dole tasa ya karba yasa tare da sa bakin Alhji Alhassan yace"a kwai sauran jama'ata dole zaka fito ku gaggaisa sosai domin dazu bansan lokacin daka gudo gida ba"
Momy tasa dariya gami da cewa"kamar ka manta halin Dan naka Alhaji kasan kwata-kwata baya son jama'a fa"
Shima dariyar yasa yace" dole yanzu yayi hulda da jama'a yadda nauyi ya hau kanshi yanzu yazama cikkaken mutum"
Momy tayi murmushi ita kadai tasan farin cikin da take ciki
Sai data ga ficewarsu sannan ta koma ciki
To ban garan su Maryam kuwa lokacin da labari iskesu, kasa katabus sukayi jikinsu yayi sanyi, Aunty tafi minti ashirin tana jajanta abun , Nasir ne ya auri diyarta Maryam anya wannan Abu ya hadu
Sai ta dinga tuhumar Nafi'u yadda a kaiyi haka tafaru, nan ya warware mata dukkanin abinda ya faru
Maryam kamar ta mutu Dan bakin ciki kuka takeyi wiwi, babu Abinda zata cewa Anwar sai dai tace "Allah yayi mata sakayya wannan tozarcin da yayi mata cikin jama'a
[08/06/2019 7:42 PM]
Binta Umar Abbale: Shi kuma Abdul, ta barshi da Allah yadda yaci amanarta bazata taba yafe masa ba, in ta tuno wai ita matar aure ce kuma matar Nasir sai gabanta yayi ta mugun faduwa, Ya Rabi tayi tayi da ita tayi shiru abin ya gagara ,
Malam ya shigo yana sa6e babbar riga kana ganinshi kasan yana cikin tsantsan farin ciki
Kawai ya taddasu sunyi jingum jingum sai kace gidan makoki, ya bisu da kallo daya bayan daya kana ya mayar kan Maryam wacce ke rakube gefan kujera tana shirgar kuka kamar wacce a kai ma mutuwa
Ranshi ya baci ya daka mata tsawa gami da cewa"kukan mai kikeyi Maryamu"?

Ya Rabi tace"wallahi kuka take tun da taji labarin abinda ya faru, anyi anyi tayi shiru taki yi"
Zama yayi cikin kujera yana fuskantar ta yace" wani irin kuka zakiyi Maryamu ke da Allah ya rufawa Asiri lokacin da a kaso a tona miki, tabbas nasan a kwai abinda Allah ya boye a wannan al'amarin,
Abinda nakeso dake shine ki kwantar da hankalinki kina tare da albarkamu insha Allahu zakiga alkairi a rayuwarki mutukar kika yimana biyyaya, nine mahaifinki na kuma karbi sadakinki na kuma bawa Nasiru Auranki a madadin Abdul"
Malam ya karashe maganar gami da zira hannu cikin aljihun malin malin din dake jikinshi ya ciro kudi yace"ga kudin sadakin ki Maryamu Allah yayi miki albarka ya baki zuri'a tagari tare da "yar uwarki abokinyar zamanki"
Maryam tana kuka ta sanya hannu bibbiyu ta karbi kudin dake hannun mahaifinta
[09/06, 19:26] +234 808 996 5176: [09/06/2019 2:23 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*113*
Da kyar Ya Rabi ta rarrashi Maryam ta bar kukan da takeyi ta sanyata tayi Wanka ta fito mata da wani uban les blue colour yayi mugun yi mata kyau abinka da farar fata ta sata tayi kwalliya dai-dai misali dama Maryam bata da matsalar gashi kullum cikin gyarashi take, dan haka Ya Rabi ta kara gyara matashi sosai ta fito mata da mayafi pink colour hade da yari da sarka fashion munti colour set din Takalmi da jaka iri daya masu bala'in kyau da tsada,kan kace kwabo Maryam tafito Amarya sosai tayi kyau, haka "yan uwan mahaifiyarta suka sanya ta a gaba suna ta bata baki kan ta godewa Allah akan sauyin da yayi mata, dama haka shi yafi alkairi a rayuwarta
Lokacin da Mubina taji labarin abinda ya faru sai da takusa yin dan Karamin hauka, kamar ita ace zatayi kishi da wannan yarinyar tasan tafita komai na rayuwa ilimi kudi wayewa nasaba uwa uba kyau ita a ganinta tafi Maryam komai da komai sabida haka taci alwashin akan sai dai Nasir ya zaba ita ko Maryam din domin bazata taba yin kishi da wannan jahilar ba.

Kwayenta sai zugata sukeyi kan in taje kar ta saurarwa Maryam kuma kar ta sake ta yadda su zauna gida daya da ita domin babu aji.

Hanifa kuwa dariya take tana farin ciki a fili tafito tace"wallahi haukan bazan kike domin ko makawo ne ya sha fa ki ya shafa kishiyarki yasan tafiki kyau, nesa ba kusa ba sabida haka ki daina wani hura hanci"
Mubina ta rika zaginta kamar "yar maguzawa a kan me zatace Maryam tafita ita irin matan nan ne masu San kansu komai sun fi kowa iyawa
A waya ta kira Nasir din tace masa ita Sam bazata zauna gida daya da wata wallahi kuma sai dai ya zaba Ita ko Maryam
Lokacin yana tare da Momynsa kuma duk taji abinda Mubina tace hankalinta ya tashi, tun ba'aje ko ina ba Mubina tafara shigo da tsirfa dama kwata kwata ita tasan Maryam ba zata damu ba
Mubina ce abin ji
Ganin Nasir din bai bata amsa ba ya kashe wayarsa tace"My son wane mataki zaka dauka ne nifa banason rigima kuma ba nasan abinda zai daga maka hankali"
[09/06/2019 2:42 PM]
Binta Umar Abbale: Tsaki yaja yace"Momy karki damu babu macan da ta isa tasa na sauka daga kan ra'ayina , mutukar Mubina tana San zama dani dole tabi umarnina, Momy bani da ra'ayin raba gida kuma bazan raba ba tare zasu zauna da juna shikkean nagama magana"
"Myson ina ganin ka raba musu gidan kawai zaifi alkairi"
"Momy ki kyaleni Dan Allah wallahi Momy Mubina bata isa tasa ni nayi abinda banyi niyya ba, kawai ki bar maganar,ke dai kawai ki cigaba da min addu'a"
"Toum shikkenan My son Allah ya taya riko ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu"
"Ameen Momyna abinda nake so inji kenan"
"Yanzu cikin Estet din zaka zauna ko zaka fita"?

A jiyar zuciya ta sauke gami da cewa "gidan Dady dake Tarauni nan nasa a gyara dazu munyi waya da mai akin za'a mishi fanti ko wane part kowa zai dau daya tunda uku ne shikkenan naraba gaddama babu wacce zata ga "yar uwarta sai taso"
"Kayi dabara Myson"
Momy tafada ta cigaba da cewa "yanzu ni kadai zaka bari a gidan nan ko"
Dariya yayi yace"Momy ko kinaso in zauna nan din"?

Itama dariya tasa tace"A'a babu ruwana ni bana son zama da sirika, Myson ina nan ina maku fatan alkairi
Murmushi kawai yayi yana girgiza kai
Ya mike tsaye gami da cewa "zan shiga inyi Wanka in fito yanzu zan Dan fita a kwai wasu baki da za muyi daga Fatkwat abinda ya hana Abbas halarta daurin auran kenan, gashi na kashe wayoyina dole nasan zasu nemeni"
Momy tace" Yau dai daya su yi maka uziri yau ranar auranka ma sai ka fita My son"
Murmushi yayi yace"Momy kenan"
[11/06, 11:02] +234 808 996 5176: [10/06/2019 6:00 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*114*
Wanka yayi ya sanya wata shadda mai uban tsada wagambari fara kal ya sanya hula fara takalmi mai gidan dan tsaya baki sai a goganshi na silver mai mugun tsada sosai dressing din yayi mishi kyau kana ganinshi kasan ango ne hannushi rike da farin glass ya fito sai zabga kamshi yake
Momy na zaune tana waya da mutananta tana fada musu yadda al'amarin ya kasance, yace"Momy zan fita ni sai bayan isha'i zan dawo"
Momy ta mike ta biyo bayanshi tace"yanzu yaushe zasu tare iyalin naka"?

"Gobe insha Allahu
Za'ayi komai a gama"
"To Allah ya kaimu lafiya"
Momy tafada cikin farin ciki
Sai da ta ga fitarshi daga gidan sannan ta koma ciki
Ban garansu Mubina kuwa buki suke sosai da sosai babu yadda bata dayi da Nasir ba a kan ta shirya party tanaso ya hallata amma yace mata babu inda zashi dan bashi ya sata ba, haka dai tayi hidimar bikin ita da kawayenta
Wata kawar Ya Rabi ce tazo ta dauki Maryam ta kaita gidanta ta dauko mai mai kunshi gami da gyaran jiki, kunshi yayi kyau sosai baki da ja daki guda ta sata ta turara mata jiki gami da gyaran fata sai da fatar Maryam tayi mulmul sosai Hajiya Aisha ta shirya Maryam sosai sannan ta dauketa a motarta suka nufi wani hadaddan boutique ta dinga jidar mata kananun kaya masu kyau da tsada.
Chapter 51 · 0% Book details