← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 80

Sashe 44

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar yace"in har kikaga na sake ki to ki tabbata kin yi min irin wannan abin da kikeyi min a cikin baccina"
Tana kuka tace"to zanyi maka ka sake ni"
Kirjinta ya zubawa ido yana kallo kamar wani tsohon maye
Tayi saurin sanya hannunta ta dafe
Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya saketa har yanzu idonshi na kafe a kanta kamar zai cinye ta , shi kadai yasan abinda yake ji a jikinshi yarinyar ta tayar masa da muguwar sha'awa.

Mikewa tayi tana kuka ta kalleshi duk yayi bake bake a kan bed din ga kafafunta a cinyarshi cinyoyinta duk a waje ta janyo rigarta tana rufewa sai kukan bakin ciki takeyi Yau Nasir har pant din ta sai da yagani wannan abu da mai yayi kama
Ta mayar da botiran rigarta da sauri ta mike tsaye kan bed din tana kokarin dirga da kan gadon
Yayi saurin damkar hannunta idonsa jazir ya ce "na fada miki yau sai kiyi mini a zahiri sannan zan kyaleki ki tafi"
Cikin kuka ta fuxge hannunta tana nunashi da Dan ya tsa tace"Wallahi bazan taba yafe maka ba abinda kayimin mugu"
Cikin dauriya yace"nima bazan taba yafe miki ba abinda kike min muguwa azzalima kawai"
Maryam ta nufi kofa a fusace, yayi saurin tarar gabanta yana bin jikinta da kallo sosai yace"koma ki shiga toleit ki wanke fuskarki masharanciya wato zaki fita a haka Momy ta zaci nayi miki wani abu ko"
[30/05/2019 11:13 PM]
Binta Umar Abbale: Domin ya kyaleta ta fita yasa ta nufi toleit din kamar yadda yace
Zama yayi gefan kadon sai nishi yakeyi sosai shi kadai yasan halin da yake ciki game da yarinyar
Maryam ta fito tana goge fuskarta , ya bita da kallo kawai har ta bude dakin ta fita
Momy na zaune a farlo taji shiru tayi yawa , ta kalleta cikin zargi tace" kin gama Dota Allah yasa dai bai ci zalinki ba"
Cikin "yar dariya tace" Momy kenan babu abinda yayi min na tsaya na hada masa wanki ne sannan Na matse masa kananun boxars din shi"
"To sannu Dota Allah yayi miki albarka"
Momy tafada cikin farin ciki
Maryam kwata-kwata bata son su hada ido da Momy sabida ta fuskanci kallon tuhuma Momyn take mata, sai kawai tayi mata sallama ta fice da Sauri
Momy ta bita da kallo cikin tsarguwa sai ta mike kawai ta nufi dakin Nasir din.

Maryam kuwa tayi da tasani yafi dubu da tasan abinda zai faru da bata soma zuwa ba
A kwance ta sameshi yayi rigingine ya zubawa POP din dake manne a saman dakin Momy tabi gadon da kallo ganin yadda duk ya hargishe ,wai nan an gyara,
Shigowar Momy bai sa shi ya dago kanshi ba sabida jikinshi ya bashi cewar ita ce
Ta tsaya a kanshi cikin kausassiyar murya tace"My son"
Ya dago kanshi ya na kallonta
Momy taga idonshi sunyi jazir sai gabanta yafadi, tabbas tayi ganganci da ta tura yarinyar dakinshi a halin tasan yananan
Jikinta a sanyaye tace"mai kayiwa yarinyar nan? naga kamar ta fita a hargitse"
Ya mutse fuska yayi yace"Momy ita baki tambayeta mai tayi min ba sai ni"
"Ba dole in tambaye ka ba, sabida nafi kowa sanin halinka"
Momy tafada cikin bacin rai
Mikewa zaune yayi jikinshi a sanyaye yace"Momy wane irin hali ne dani"?

"Kafi kowa sani ai"
Murmushi yayi mai ciwo yace"Momy kenan , ki tambayeta in da abinda nayi mata, wai mai yasa zuciyarki take wasiwasi a kai na ne , Momy mai zanyi da wannan zabiyar yarinya, ok tunda abin ya zama haka, kar ki kara turo ta tayi min gyara a dakina"
[30/05/2019 11:35 PM]
Binta Umar Abbale: Momy tace"a kwai abinda ya faru tsakanika da ita myson ni ba Yarinya bace"
Dariya ce ta kashi sosai ya rika yi ganin yadda Momy ta dage tana tuhumarsa
Yace"ok toum Momy tunda kince haka sai kije kiyi mata ruwan zaki kawai"
Kunya ce ta kama Momyn ta kai masa duka a kanshi tace"baka da kunya ko Myson "
"To Momy kin dage sai tuhuma ta kikeyi wai mai nayi mata, ai in nayi mata wani abu daga lokacin da ta fita zaki ga alamu ko ta wurin tafiyarta ne"
Momy tace"to mubar naganar ma daga yau na daina sata tayi maka aiki yafi alkairi"
Tabe baki yayi kawai ya koma ya kwanta ,tace" ka fasa fita yanzu ne"
"Yanzu zan fita Momy ina hutawa ne"
"Ok sai ka fito"
Ya fi miti goma a kwance bayan fitar Momy din sai mutsu-mutsu yakeyi duk ya rasa inda zai sa kanshi da kyar dai ya mike ya nufi toleit ya sake yin wani wankan tun kafin ya gama yafara jin wani sanyi-sanyi yana ratsa shi a daddafe ya fito cikin karfin hali yake kimtsawa zazzabi ne yake so ya rufeshi ,haka dai ya daure ya gama kimtsawa ya fito cikin shirin fita
Momy ta kalli agogo tace"baka yi yamma ba kuwa myson dubi time"
"Momy karki damu Hospital kawai zan shiga daga nan babu inda zan je"
"To Allah ya tsare"
Momy tafada
Yana fita Giss dama yana tsaye ,sai kawai ya rufa masa baya Tony ya bude masa mota ya shiga yayi saurin zagayawa ya zauna gurinshi, Giss ya shiga Tony ya ja motar suka fita daga gidan.
[06/06, 01:48] +234 808 996 5176: [31/05/2019 8:53 AM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*99*
Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin, Maryam ta rika kiyaye haduwarta da Nasir sabida wata irin kunyarsa take ji sosai kuma har yanzu soyyayrsa tana nan daram a cikin zuciyarta
Yau misalin Tara Na dare suna zaune ita da Abdul a harabar gidan suna hira cikin nishadi ,shima yau kwanansa biyu da dawowa sosai Maryam tayi kwalliya tana cikin atamfa "yar Ghana anyi mata duguwar riga mai babban hannu sosai tayi kyau ta yafa mayafi kalar kayan fuskarta ta sha kwalliya suna zaune a cikin wasu kujeru farare masu kyau
Abdul yace"insha Allahu a satinan za'akawo komai na aure za'a sa sati hudu daurin aure, in naje nadawo"
Maryam ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya tace"to Allah ya kaimu"
Yace" maganar aikinki kuma zan samu Nasir da takkadunki nasan bazai ki daukirki ba tunda tunda takkadunki sunyi
kyau
Da sauri ta dago kai tana kallonsa jin abinda yace
Tace" Kana ganin zai dauke ni kuwa kasan bama shiri dashi"
Dariya Abdul yayi yace"karki damu nasan yadda zanyi dashi"
Sai wajan karfe goma da rabi Abdul ya mike da niyar tafiya bayan ya aje wasu manya manyan ledoji
Maryam ta mike ta biyo bayanshi suna tafiya suna hira har ya karaso kusa da motarshi, ya shiga yana kokarin fita , Mai gadi ya bude get din Nasir motar Nasir ta shigo cikin gidan
Sai ya kashe motar kawai ya fito yana jiranshi Maryam na tsaye a gefanshi kanta a kasa,Sam bataso ta hada ido da Nasir din
Giss ya bude masa kofa ya fito ,fuskarshi babu yabo ballasa ya mikawa Abdul hannu suka gaisa
Abdul yace" yanzu nake zan can kada ma"
Fuskarshi ya saki yace" yaushe kadawo ne Alhaji"
"Yau kwana biyu da dawowa wallahi, nazo ganin amarya na"
"Ok andawo lafiya ya aiki"?

Nasir yafada yana binshi da wani kallo jin abinda yace
"Alhmdullhi wallahi komai normal"
Nasir ya zare hannunshi cikin gajiya yace"zan shiga ciki Abdul nima Na gaji ,gashi gobe nake saran zan wuce america amma bazan dade ba"
"Allah ya kaimu da jirgin safe zaka bi ko na yamma"?

"Na yamma"
Nasir yafada yana kokarin barin gurin
Abdul yace "zan shigo da wuri insha Allahu a kwai alfarmar da nake nema a gurinka"
"Allah ya kaimu lafia"
Yafada yana wucewa Giss ya na take masa baya
Duk wannan abinda yake faruwa Maryam kanta a kasa tana jin duk irin share-sharen da Nasir yakeyi shi kuma Abdul din sai wani binshi yakeyi lallai ta yadda Farin jini da daukaka a jininsa take
[31/05/2019 9:17 AM]
Binta Umar Abbale: Ita yanzu ta daina shiga sabgarsa ma kwata-kwata sabida ta lura ba karamin dan iska bane
Abdul yayi mata sallama ya wuce ita kuma jiki a sanyaye ta wuce bangarqnsu
Momy na zaune cikin kujera tana kallo kuma tana jiran shigowar Nasir din sabida bayan fitarshi dazu Alh Salisu yazo ya kare mata rashin mutumci wai itace take zigashi yakeyin duk abinda yakeyi cikinsu babu Wanda yake gani da gashi ,sabida haka lallai in ya dawo ta ce masa yaje yana naimanshi ,aura shi da Mubina babu fashi, tunda haka Mahaifinshi yace kafin rasuwarshi.

Momy ranta ya baci domin har kuka sai da tayi tunda take babu mutumin da ya taba tsayawa a kanta yayi mata cin nutumcin da Alh Salisu yayi mata yau, sabida haka mutukar ita ta haifi Nasir dole ne ya auri Mubina inyaso daga baya sai ya auri zabinshi.

Yayi Sallama ya shigo Momy ta bishi da kallo har ya karaso kusa da ita ya zauna, ita kanta tausayinsa takeji ganin yadda girma ya hau kanshi da kananun shekarunshi amma da yake *Yaron* yana da ilimi cikin nutsuwa yake tafi da komai
Yace"Momy na gaji wallahi"
Cikin tausayi ta kalleshi ,ta kasa cewa komai ma
Sai ya dago kai yana kallonta jin har ya shigo yayi magana Momy bata tanka mashi
Lallai akwai wani Abu
Ya gyara zamanshi sosai yace"Momy menene,?

Bafa nasan in ganki cikin damuwa, uhmm lafiya lau Na fita na barki"
"Myson lafia ba lafiya ba"
Momy tafada tana gyara zama sosai tana fuskartansa
"Tell me"
"Momy fada min ko manene kinji"
"Dazu bayan fitarka Kawunka yazo har cikin falon nan ya karemin zagi sosai wai lallai sai ka auri diyarshi ,sabida haka mutukar nice Na haifeka dole ne ka aureta domin mu samu kwanciyar hankali"
Ranshi ya baci mutuka jin abinda Momy take fada masa
Yace"Momy kikace "uncle Salisu yazo gida ya zage ki to akan me"?
Chapter 44 · 0% Book details