← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 80

Sashe 38

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Maryam tafada kai tsaye tana kallonshi babu kifta wa
"Yes"
Yafada yana zare mata ido
Dariya ce ta subuce mata bata shirya ba ,tace "wallahi da naji dadin haka kaga dana huta da ganinka a duniyar nan domin bana kaunar in bude ido in ganka a rayuwata"
Shiru yayi yana bin ta da kallo Sam maganganunta basu bata masa rai ba so yakeyi ya kirkiri abinda zai bakan ta mata rai yanzu
Zama yayi gefan gadon yana ya mutse fuska yace "Ke boyi boyi na zo nan Dan Ubanki ki fito min da kayan da zansa yanzu nan"
Wani mugun shocking Maryam taji a jikinta lokacin da ya kirata da wannan Kalmar Boyi-Boyi ,har da zagin Ubanta,lallai yau zata nuna masa tasan darajar iyayenta
[06/06, 01:45] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*89*
Maryam ta juyo a nutse tana kallonsa fuskarta babu yabo babu fallasa,tace "Nasir inaso kasa ni, ni Maryam wallahi nafi qarfin in zama boyi-boyin ka ,dukkanin abinda kaga ina yi maka ina yi makane kawai sabida darajar Momynka,amma kasani cewar kudinka ko takamarka basu isa su sa na yi maka bauta ba ,wallahi in har nice zan dauko maka kayan da zaka sa,to sai dai a kwana a haka,amma kai baka isa kasani abinda banyi niyya ba"
Idanshi tsaye a kanta har ta kare maganar
Ranshi a bace yace"Na nawa kuma yarinya ,Wanda yayi silar zuwanki duniya ma gashi can bakin get yana min gadi,ballantana ke!!"
Ya karashe maganar yana nunata da hannu cikin izgili
Kuka ne yakeso ya Kufcewa Maryam jin cin mutumcin ya shallake kanta ya dawo kan Mahaifinta
Tace"tabbas kafadi gaskiya mahaifina ba komai bane ,kuma ba kowa bane a duniyar nan ,muna nai man tsari da dukiyar da zata samu mu manta da Allah mu shagala da duniya murika sabon Allah a cikinta"
"Ke kika sani dai yarinya na get out malama"
Yafada yana nuna mata kofa
Maryam ta bude kofa ta fice batare kawai tana girgiza kai cikin takaici wulakancinsa
Momy na tsaye da hijab a hannunta tana kokarin sawa tace"yawwa dama yanzu nake kokarin in shiga in miki magana kifito mutafi naji shiru,nace Allah yasa bawani abin yayi miki ba"
Cikin kokarin danne abinda yake taso mata Na bacin rai tace "babu komai wallahi Momy nayi duk abinda kika Sani"
"Yawwa Allah yayi miki albarka"
Momy tafada
Sannan suka fita a tare
Momy ta daukesu a motarta har Malam Ya'u suka nufi asibitin
Mikewa yayi bayan fitarta ya nufi tolirt a gurgije yayi Wanka ya fito ya nufi inda kananun kayanshi ,ya kwana biyu bai sasu yau sai yaji yana sha'awarsu ,tsaf ya shirya cikin wani mugun wando jins mai mutukar tsada blue colour shart din ma haka ta matse masa j
iki sosai power dinshi ya fito ya gyara sumarshi tsaf sannan ya dauki agogonshi ya daura,ya nufi inda takalmanshi suke ,sai da ya sanya safa sannan ya saka wani mugun takalmi fadar kudinshi ma aiki ne ,sosai Yayi bala'in kyau ,sabida yadda dressing din ya karbe shi ,sabida yadda ya yi qiba jikinshi ya murje sosai ya fito ,ya nufi inda motarshi take shima babu inda yayiwa tsinke sai hospital din yanaso yaje ya duba marasa lafiyarsa ,sannan ya wuce can gurin Abbas domin cigaba da tsare tsarensu na bude sabon gurin shakatawa da zasuyi
[06/06, 01:45] +234 808 996 5176: [26/05/2019 9:51 AM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*90*
Alhamdullihi jikin Baban gida yayi sauki sosai ,yana zaune gefan gado su aunty a kusa dashi , su Momy sukayi sallama cikin dakin, Yaya Rabi ta amsa tana yiwa Momy sannu da zuwa, fuska a sake Momy ta karasa cikin dakin tace"A'a lallai jiki yayi sauki Baban gida Allah ya kara afuwa"
"Alhamdullhi kam jiki ya samu wallahi"aunty tafada tana bawa Momy gurin zama Momy ta zauna suna gaisawa da Yaya Rabi cikin mutumci , aunty ma suka gaisa cikin sakin fuska Yaya Rabbi ta kalli Maryam dake tsaye jikinta a sanyaye tace"ke kuma abinda kikayi kin kyauta cikin dare ki fita ,kisa mi ta nai manki ko duk kin daga mana hankali"
Maryam ta sunkuyar da kanta kasa ,domin bata da abin cewa,tasan in tafadi abinda ya faru ba yadda zasuyi ba
Momy tace"subahanallahi kamar yaya tafita cikin dare"?

Aunty ta girgiza kai cikin bacin rai tana kallon Momy tace"wai daga cewa in uncle dinta ya shigo taje tabashi hakuri kan irin rashin kunyar da tayi masa jiya,shine da ta fakaici idon mu taga munyi bacci shine ta gudu gida ,sabida tana ganin kyashin ta tsaya tabashi hakuri"
Momy tayi murmushi tace "Laifin mai tayi da har zaki titsiyeta kice lallai sai tabashi hakuri ,waya gaya miki anawa yara haka,?

Ni sam banga laifin ta ba ,Dan yaro ya tsare kare martabar iyayenshi sai ace yayi laifi ,karki kara yin haka Suwaibah wannan ba hukunci ba ne"
Malam Ya'u yana tsaye jikin gadon da Baban gida yake kwance ,ya sauke ajiyar zuciya yace" nima abinda nakeso ince mata kenan abinda tayi bai yi dai-dai ba ,jiya misalin uku shaura Na dare naganta ta shi go gidan a furgice,hankali na ya tashi sosai ,duk Na tambaye ta dalili shine take fada min
Yaya Rabi tace"kwarai hakan ba dai-dai bane wallahi kar kiso kiga yadda hankalinmu ya tashi jiya
Sai da asubah da nace ta kira Babanta ta sanar dashi halin da ake ciki ,shine fa yake cewa gata a gida mu kwantar da hankalimu"
Momy tayi ajiyar zuciya tana kallon Maryam din tace "kar ki kara aikata irin haka,yanzu inda wani Abu ya sameki Na tsautsayi kice mai,Allah ya kiyaye ameen"
Maryam tace"insha Allah Momy bazan karaba"
Momy tace"ga kayan kari nan Rabi"
Yaya Rabi tace" to angode Hajiya Allah yakara girma ya jikan magabata"
Nan Momy tasa a ka hadawa Baban gida abinci a kabashi sannan tabashi magani da kanta,suna hira kadan kadan,Nasir ya shi go cikin dakin Dr Sofia na bayanshi hannunta rike da wasu takkadu
[26/05/2019 10:18 AM]
Binta Umar Abbale: Sama-sama ya gaida su aunty hankalinshi na kan Baban gida,Dr Sofia kuwa babu wanda ta gaida a cikinsu sai Momy ,to Momy Sam bata kawo komai ba , sabida tasan yarinyar dama can ba wani hausa takeji ba sai turanci amma dai duk da haka inda mutumci yadda ta gaida ita ta gaida sauran da suke tare
Aunty ma jikinta ne yafara sanyi sabida ta lura da irin kallon raini da Dr Sofia take musu ita da Yaya Rabi,amma sai ta daurewa zucuyarta tace ko Dan yarinyar ba musulma bace shiyasa batasan darajar Dan adam ba.

Maryam ko taci alwashi sai ta ci mata mutumci ko da me take takama wallahi bazata raina mata iyaye ba,tana addu'ar Allah yasa kafin su gama zaman asibitin wani abu ya hadasu da'ita sai ta wulakantata
Dama gashi tana jin haushin yadda take wani shishshigewa Nasir din Dan wani lokacin tana lura jikinsu har haduwa yakeyi
Ya karasa bakin gado yana duba shi sosai Ya kalli aunty kadan yace"anbashi magani ko"?

Aunty tace"eh yanzu Momy tabashi"
Shiru yayi kawai ,ya dauke idonshi daga kan Baban gida ya dora kan Momy ,fuskarshi kamar ko da yaushe yace"Momy ina ganin zan sallameshi tunda ya dawo normal So sai ya cigaba da karbar magani a gida ,sabida ni banaso ana cika min asibiti kullum"
Duk cikin turanci yake maganar in banda ita Momy din da Dr Sofia da Maryam babu Wanda ya fahimci abinda yake fada
Cikin turancin Momy tace"Why My Son mai yasa kake haka ne suwaye mutane ,ni ko kuwa iyalan wannan bawan Allah ,uhumm!

Wulakanci fa babu kyau"
Ya mutse fuska yayi kadan yana duba a gogo yace" Momy bafa haka nake nufi ba please kinsan komai nawa a tsare yake ,wallahi kwata kwata tunda suka shigo hospital din nan daga jiya zuwa yau komai ya sauya,gwara kawai su koma gida ,sai in cigaba da kula dashi"
Dr Sofia tasa baki ita ma cikin ya mutse fuska cikin turancin ta tace"yes Bama bukatar hayaniya a wannan guri Momy sabida duk yawanci marasa lafiya suna bukatar huto da kwanciyar hankali"
"Momy tayi kwafa tana kallonta rai a bace tace" wato koya min yadda aikin asibiti yake zakuyi ko kuwa tun kafin a haifeku nake wannan aiki"
"Sorry Mom ba haka bane , kiyi hakuri in maganar tayi miki ciwo ,in babu damuwa abar mana Mara lafiyar shi kadai kawai bama bukatar "yan jiya ,sabida a kwai masu kula da..

"Ya'isa"!
Chapter 38 · 0% Book details