← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 80

Sashe 31

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin Mamaki Mom din tace "banason rainin hankalin ka fa my son Baban gidan kake tambayar wanene"
Ya bata Fuska yana kokarin mikewa tsaye yace"Mom kije ki dubashi ke mana ,nifa duk abinda zai hadani da wa"yancan mutanen bana so"
"A'a kai yafi can can ta kadubashi kaji ko"
"Momy nifa likitan mata ne kawai bazan gane mai ke damunshi ba"
Hararsa Momy tayi tace"kasa ba fada ina fada ko My son"
Tafada ran ta abace
Ganin ranta ya baci yasa yace"Momy kije ganin zanzo Wanka zanyi shikkenan"
Momy ta mike gami da cewa "ok kafito yanzu Dan Allah yana jin jiki"
"Ok Momy"
Yafada yana kokarin shaga toleit
A nitse yayi shirinsa ya fito cikin Wani uban yadi piltex yayi mishi uban kyau sosai, bai sanya hula ba ,sai sumarshi da ya gyara sai daukar ido takeyi ,fatarshi kamar ka taba jini ya fito fara tas ,sai kwantaccan gashi baki sidiq da yabi lafiyar fatartashi,
Kunneshi makale da eirpix ya fito harabar gidan,ganinsu yayi ,sunyi cirko cirko a tsaye
[18/05/2019 10:44 AM] Bint U Abbale
: Ranshi ya baci ganin yadda suka zuba masa ido ,harda wancan banzan yarinyar ,a fili ya ja tsaki ya karasa gurin ,gami da mikawa Malam Ya'u hannu suka gaisa, Sama-Sama ya gaida auntt da sauran jama'ar gurin ,Nafi'u ya mika masa hannu su gaisa kamar yadda ya saba yi musu,nan ma bai wani sakarwa yaran fuska,kai tsaye ya kalli Malam Ya'u yace "ina Baban gida yake?"
Can gurin Baban gidan ya nuna masa yace"yana ciki a kwance"wallahi jiya ba muyi bacci ba ,ciwonshi ne ya tashi"
Tabe baki yayi bai ce komai ba ya nufi motarshi ,yana tafiya yace"ku dauko shi ku kawo min asibiti"
Ya bude motarshi kawai ya shiga Malam ya tafi da sauri yaje ya bude masa get din ya fice daga gidan ko kallonsa bai yi ba
Maryam kamar ta saka hannu a gurin tai ta kurma ihu haka takeji cikin zuciyarta wani irin zafi take mata lallai talauci bai yi ba, gata a tsaye ana wulakanta mata iyaye tun lokacin da uncle din ya fito take satar kallonshi ,tana lure da yadda yake wani ya mutse fuska yanawa iyayenta wani banzan kallo, gaskiya baza ta iya jure wannan bakin cikinba, dole zata nemi aiki domin ta sharewa iyayenta hawaye,wata zuciyar tace mata kin manta alkawarin dady akanki ,na auran Abdul gabanta ya fadi ,girgiza kai tayi tace dole muyi yarjejeniya da Abdul domin bazan bari iyayena su kaskanta ba
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [19/05/2019 11:04 AM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*68*
Momy tafito daga part din ta ta gansu tsaye har yanzu tace"A'a Nasir din bai fito bane"?

Aunt tace"ya fito yanzu ya fita yace a kai masa shi can asibitinsa"
Girgiza kai Mom tayi kawai tana mamakin halin danta, yuyawa tayi ta koma ciki ta sanyo hijab gami da daukar key din motarta ta fito ta sanya sucurutiy dake waje su saka mata Baban gida a mota,sannan su Malam Ya'u suka shiga tare da auntt da wata yayarta sai Maryam da su Nafi'u Momy taja motar suka fita daga gidan.

Lokacin da suka isa asibitin Nasir yana teater room ,yana duba mara sa lafiya , kwata -kwata ya manta da wani Baban gida ,tare suka fito da Dr Sofia tana cikin kayan aiki cinyoyinta duk a waje kasancewar siket din dake jikinta karami ne iya cinya (mini) gashi antsaga shi ta baya, kanta yasha karin gashi sosai kafarta sanye da wani takalmi mai mugun tsayi fuskarta manne da tubarau ,kwata kwata bata jin hausa ko daya ,duk abinda sukeyi da turanchi sukeyi Dr Sofia ta Dade tana kaunar Nasir tun lokacin suna karatu , shi a lokacin baya ta tata shiyasa yanzu da yayi mata maganar yanaso tazo tayi aiki a sabitin sa yasa ta'amince da sauri tana burin Allah yasa yafara sonta,shima
Duk da cewar tasamu aiki mai tsoka amma tana ganin aiki da Nasir wani ci gaba ne a rayuwarta
[19/05/2019 2:49 PM] Binta Umar Abbale: Fuskarshi a sake yake zagaya feshen din sa , yana tambayar su yadda suke jin jikinsu,alhmdullhi kowa lafiya ,tare suka fito Dr Sofia sai shisshige masa takeyi shima fuskarsa a sake yake amsa mata
Momy ta kalleshi tace"ka kyauta Nasir tuntuni muna zaune muna jiranka ko kana ciki kayi banza da mutane"
Murumshi yayi kadan ya karaso gurin yace"Mom kiyi hakuri kinji bana son kurafi kince lallai sai ni ne zan dubashi bayan kema likita ce"
Hararsa tayi kawai ta dauke kan ta
Dr Sofia taje ta durkusa tana gaida Momy cikin turanchi Momy ta rungume ta tana amsawa cikin sakin fuska,
Dr Sofia ko kallon su Maryam bata yi balle ta gaida su Malam.

Maryam zuciyarta sai zafi take mata
Nan take Nasir yasa a ka dora Baban gida a wani gado yace a kaishi wani daki gashinan zuwa
Malam Ya'u ya mike da sauri zai bisu Nasir ya buga masa tsawa cikin izgili yace"bama bukatarka a gurin ,ka tsaya a matsayin ka"
[06/06, 00:47] +234 808 996 5176: [20/05/2019 10:45 AM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*79*
Maryam ta yi masa wani banza kallo a nutse ta ce"in kun shiga ku to ku hana Allah ikonshi ,domin duk abinda kake takama kana dashi na ilimi ko kudi ko wani abin daban Allah ne ya baka ,kuma zai iya bawa kowa ,sabida haka duk inda mutum yake yana da daraja da baiwarsa , ba muce lallai sai ka duba Baban gida ba ancle a kwai lokitoci a duniya masu tsoran Allah gami da yin abu dominshi, ka sani ta lauci ba hauka ba ne da zaga rika zagar min iyaye a gabana ,in kai bakasan darajar naka ba ni Maryam nasan darajar iyayena domin sune kashin bayan samar dani"
Ta karashe maganar tana wani huci!

Dagani kasan a cikin mugun bacin rai take.
[20/05/2019 1:37 PM] Binta Umar Abbale: Aunt ta tsinka mata mari ,rai a bace tace "yaushe kika zama haka, uncle din kikewa rashin kunya, Na lura dama ko gai dashi bakiyi ba , to maza ki bashi hakuri ko yanzu in miki dukan tsiya a gurin,
Momy taji dadin abinda Maryam tayiwa Nasir din domin ita ma ta gaji da rashin mutumcin da yake yi wallahi,dan haka aunt take wa fada a kan me zata mari Maryam din ai gaskiya tafada.

Maryam kuwa kuka takeyi wurjanjan kuma taki cewa komai ballantana tabawa taje ta bawa uncle din hakuri,Wanda tuni ya wuce cikin dakin da Baban gida yake kwance,yana mamaki wai yau shi yarinyar take mayarwa da magana sabida wuyanta ya isa yanka tabbas taci darajar dady din shi ,amma duk da haka sai ya kaskantar da ita,
A yanzu dai bashi da lokacin kulata balle ya mayar mata da martani
To ba wani abin ne yake damun Baban gida ba illah ciwon suga ga Jininsa ya hau sosai,nan yayi masa taimakon gaggawa Dr Sofia na gefanshi tana saka masa ruwa , kan kace kwabo bacci ya dauki Baban gida , Nasir ya kunna masa Ac dai-dai misali ,sannan suka fito tare da Dr Sofia tana binshi sai kace jela.
Chapter 31 · 0% Book details