← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 80

Sashe 37

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tsaf tagama hada komai tafito jikinta sanye da katon hijab dinta kamar yadda ta saba,ta aje kayan dake hannunta kusa da Malam tace"Baba bari inje mu gaisa da Momy ko"
"To babu Laifi "
Malam yafada yana bin ta da kallo
Kai tsaye part din Momy ta nufa
Momy na zaune kan kujarar daining ita dasu Nafi'u sun shirya tsaf , Uwani mai aikinta tana hada musu breakfast ,Maryam tayi sallama
Momy ta amsa mata fuska a sake tace"Dota shigo mana kika tsaya nan"
Kanta a sunkuye ta shiga ciki farlo sosai ta karasa gurin Momy din ta durkusa har kasa tana gaida ta
Momy tace"Nima yanzu nake cewa Nafi'u ya gama karyawa yaje ya kirawo min ke"
Murmushi tayi batace komai ba
"Ina fatan kin karya ko"
Momy tafada tana kallonta
"Eh Momy na karya ga abinci can ma nayiwa su aunty"
Momy tace"ai da baki bawa kanki wahala ba ,tuntuni nasa Uwani tayi musu"
"Laa Momy ai babu komai sai su hada da nawa"
Dariya Momy tayi tace"to shikkenan sai ki jiramu mu gama karyawa a nutse sai mu tafi"
"To Momy"
Maryam tafada gami da mikewa taje ta zauna cikin daya daga cikin kujerun farlo
Ko minti uku batayi da zama ba Nasir ya shigo farlo
Idansu ya tsarke guri guda
Da sauri ta dauke kai ta mayar kan kayuwat TV plasma dake manne a farlo din, ta cigaba da kallonta
Fuska ya hade sosai yana namakin mai yakawo yarinyar nan da sanyi safiyar nan , zuciyarsa yace mybe ko Momy ce ta jajibo ta yasan halin Momynsa da kwashe kwashe
Kai tsaye Tv ya je ya kashe batare da ya saurari gaisuwar da su Nafi'u suke masa ya shige dakinsa dake farlon
Baki a sake Momy take binshi da kallo tana namakin abinda yake nufi, girgiza kai tayi kawai tacigaba da cin abincin ta
Bai fi minti biyu da shiga ba sai gashi ya fito yana ya mutse fuska hannunshi rike da wayarsa yana daddanawa ya tsaya daga bakin kofar dakinshi yana kallon Momy yace"Momy wai Dan bana amfani da room din nan sosai shine ba'a gyara min, yanzu inaso in shiga toilet na tadda ko ina kaca-kaca"
Hararasa Momy tayi tace "sannu Ubana kashigo ba ka kula kowa ba shine yanzu zakazo ka titsiye ni da tambaya"
[25/05/2019 10:06 AM]
Binta Umar Abbale: Please Momyna kisa a gyara min dan Allah ,Wanka nakeso inyi zan fita"
Yafada yana karasowa inda take zaune
Momy tace"ko jiya sai da nasa, Kyauta, mai yimin goge goge ta gyara maka dakin kai dai kawai kace zakayi min iyayi"
Dariya yayi kadan abinda ya Dade bai yi mata ba ,yana kallonta yace"Momy kinsan halina banason kazanta,wallahi tunda na shigo Farlon nan nakejin karni na tashi nake kamar zanyi amai wallahi"
Ya karashe Maganar yana ya mutse fuska
Kowa yayi zagi a kasuwa yasan da Wanda yake ba Maryam kadai ba ita kanta Momy ta tsargu da Nasir din domin tunda take dashi bai taba yi mata irin wannan maganar ba ,kasancewar a ko da yaushe ko ina na gidan cikin kamshi yake sabida Allah da yayi Momy a kwai San kamshi.

Sai tayi shiru da bakinta domin bataso ta kara wata maganar Nasir din ya kwabo wata maganar tasan zuciya batada kashi dole wata rana Maryam din tafara mai da martani kamar yadda tafara ramawa jiya a asibiti
Minti biyu farlo yayi tsitt Maryam sai kokarin danne zuciyarta takeyi ,sabida yadda take jin kamar ta tashi tabar gurin ,tana jin kunyar Momy ne kawai kuma tana ganin mutumcin ta, amma ranta ya yi mugun baci da wulakancin da Nasir yake mata idanta ya Tara kwalla sai kokarin mayarwa takeyi ,kawai tajiyo Muryar Momy tana cewa Maryam Dan Allah shiga ki gyara masa dakin kafin mu gama kinji ko"
"Don Allah"
Tafada maganar cikin zuciyarta
Yanzu Momy ce take hadata da Allah
Allah sarki Momy ,albasa batayi halin ruwa ba
A nutse ta mike tsaye tana gyara hijab din ta juyo ,fuskarta a sake tace"to Momy karki damu yanzu zanyi abinda kikace insha Allahu"
[25/05/2019 2:00 PM]
Binta Umar Abbale: "Yawwa Dota Allah yayi miki albarka"
Momy tafada cikin farin ciki yarinyar tana burgeta sosai ,tanada hankali kwata-kwata bata biyewa Nasir din da abinda yakeyi
Cikin nutsuwa ta nufi bed din ,Nasir ya dago kanshi dake sunkuye yana kallon wayarshi ya bita da kallo yana ya mutse fuska ,yace"ke!"
Maryam ta juyo a nutse tana kallonsa
Yace "kar ki kuskura kiyi min binkice a daki domin a kwai muhiman abubuwana a ciki , duk abinda na nema narasa to sai kin biya ni"
Shiru Maryam tayi a tsaye tana tunanin ta shiga ko tafasa tunda zargi ya shigo ciki
Momy tace"wai mai yasa kake hakane my Son mai Maryam tayi maka kuma kake mata wani zargi na daban"
Shiru yayi baice komai ba ya cigaba da danne dannensa a waya babu abinda ya dameshi
Momy tayi kwafa kawai ranta a bace tace"Dota yi hakuri kinji ko ,kar ki dakata ta halinshi kiyi domin ni"
Maryam tayi dariya mai ciwo race"Momy karki damu ai uncle yana da gaskiya , kar inje inga wani abu nasa mai muhimanci in share ko in zubar, kwata-kwata raina bai baci ba"
Momy tasan Maryam din dannewa tayi kawai sabida kawaici irin nata,sai tace "to shikkenan Maryam je kiyi sauri ki kammala muwuce ko"
Maryam ta wuce dakin ranta yana mata suya tarasa inda zata sa ranta sabida yadda takeji a yanzu zata iya fito na fito da Nasir din ko dame yake taqama Kuwa
Babu wani datti a cikin dakin na kuzo mu gani ko ina tsaf in banda bedshit din da yayi datti kadan kasancewarsa mai kalar haske ,cikin sauri ta dauke shi gami da zare rigunan filillikan tabude sif ta Ciro wani sabo a ledarsa ,ta shimfida tsaf, sannan ta wuce toilet din shima babu wani datti
Sai jirwayen sabulu na Wanka shima ba sosai ba asalima in banda kamshi babu abinda yake tashi a ciki na irin kalolin sabulan da yake amfani dashi gurin Wanka da wanke sumarsa
Tsaf ta wanke ta sanya turaran wuta Na ban daki ,sannan tahada masa kananun wan dunanshi da vest dinshi a cikin abin wanki ,afili tace "wallahi bazan wanke ba masa Dan iska kawai,Dan rainin hankali"
Ta fito tana Jan tsaki kai tsaye kofa ta nufa domin fita daga dakin,suka ci karo dashi,zai shi go
Maryam tayi baya da sauri tana dafe goshinta sakamakon yadda suka gabza karo,ya shigo dakin yana bin ta da wani mutsiyacin kallo Na kaskanci ya mayar da kofar ya rufe yana bin dakin da kallo ,fuskarshi a hade
Bata kalleshi ba ta sanya hannunta a Karo na biyu tana kokarin bude kofar
Taji ta a kulle gam!

Sai ta waigo tana kallonshi fuskarta a murtuke
Kallon kallo sukeyi minti biyar tukkuna yace"kika kuskura kika fadama mahaifinki abinda yafaru jiya wallahi sai na kaiki inda baza ki iya dawowa ba kin tafi kenan"
"Kashe ni zakiyi Kenan"?
Chapter 37 · 0% Book details