← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 80

Sashe 11

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Mom din takara Maimaita tambayar,sannan tace"Allah Momy babu Abinda yayi tafada A fili a zuciyarta tana Jan Istigifari.

Taci gaba da cewa ,Dama Dama Wannan Abokin nashi ne,sai tayi shiru takasa karasawa,
Ina jinki ya kikayi Shiru Momyn tafada"
Shine Yake kulani Momy nikuma bana so tafada kanta a kasa,
Momyn tace"To ae kina da gaskiya Mutuncin "ya mace tsare kanta babu ruwanki dashi ko ya kulaki ,gaisuwa kawai na lamunce kiyi dashi kinji ko kuma zanyiwa Nasir magana tunda ba kyaso tayi masa magana duk inda ya ganki Kar yakara shiga lamarinki"
Gabanta yafadi jin Abinda Momyn take fada,
Da sauri ta dago kai tace"A,a Momy ba sai kin yiwa Ancle maganar ba Dan Allah"
Harararta Momyn tayi kadan tace"ae dole in yi mishi magana yajawa Abokinshi kunne domin a kanki zan iya batawa dashi"
Sunkuyar da kai tayi tana Murmushi kadan tace"Dan Allah Momy mubar maganar bana so ki batawa Uncle rai"
Dariya Momyn tayi gami da Mikewa daga kan daddumar da sukayi sallah A kanta tace" in dai a kanki ne ran Nasir zai baci kuwa ,
Mikewa tayi ita ma tabi bayan Momyn suka sauka kasa ,a tare Maryam din na kokarin fita da niyar tafiya bangaransu Momyn ta dakatar da ita,tace Lallai sai ta tsaya sunci Abinci tare ,ba yadda ta iya haka ta bi bayan Momyn can dainnig in da kayan Abinci ke jere iri iri na haduwa na Alfarma,
Momyn ta hada Mata komai tsaf ,Cikin nutsuwa Maryam tafara cin Abincin suna hira da Momyn kadan kadan ,sai da Momy ta tabbatar da Maryam ta koshi sannan ta kyaleta ta tafi bangaransu.

Lokacin da tashiga shashin nasu Ana sallahr isha'i Aunty da su Nafi'u duk sallah suke ,sabida haka Alwala ta daura ita ma tabi sawun su.

Aunty na idarwa tafara hidimar Zubawa yara Abinci ,ta kalli Maryam dake zaune kan dadduma bayan ta idar da sallah tana Addu'a ,"kefa a zuba miki ?

Nasan dai kinci gurin Momynki ko?

Daga kai Maryam tayi A nutse tace wallahi kuwa Aunty a koshe nake Amma da safe naci dumame dama yafi dadi"
Tabe baki Aunty tace Allah ya kaimu . mai kika tsaya yi a ne a can?
,,,,,,,*
[14/03, 12:41] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

YARO DA KUDI*
WRITTEN BY*
~*Binta Umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~
To masha Allah Mom tace dama ae ni haka nakeso duk da nasan ba laifin ki bane dama nashi ne.

Bata ce komai ba ta karbi key din kanta a qasa ta kama hanyar fita daga farlour n Nom tace kiyi sauri ki gama mybe yanzu ki kanshi domin Lokacin shigowar ne yanzu mussaman yafita tun safe nasan dole zai dawo ko Dan yin Wanka ,sannan
Cikin nutsuwa tace in sha Allahu zan yi sauri Momy ,
Yawwa Allah yayi miki Albarka Maryam
Amin tace ta kama hanyar fita daga Farlour nan
To ko da Maryam ta bude shashin Uncle din Abin yayi mugun bata mamaki ganin yadda ko ina yake a hargitse babu gyara A fili tace gayu an sanku ba'a San makwancinku ba ta6!

Yanzu shi duk gayunshi dakinshin haka yake lallai
Bata kara tsinkewa da Abin ba ma sai da ta shiga bedroom dinshi taga kaca kaca komai a hautsine kayanshi barbaje kan bed dinshi wasu a qasa wasu a kan kujera takalma a haushine duk da gurin ajiyarsu suke mirrow dinshi kaca kaca turarurruka ne masu Dan karan tsada a zube a gurin gami da mayuka sun fi kala a shirin wasu har sun fado kasa,
Toilet din tabude ta shiga ,Wai Abin sai a hankali da'alama tunda ya tafi Momy ba sosai take sawa a gyara dakin ba domin bacin da yayi,, yayi yawa gajerun wando nane sunfi kala goma gasu Nan a zube cikin Abin Tara wanki da'Alama kullum sai ya balle sabo ganin ledodinsu a gurin ,
Nan da Nan ta Tara ruwa tafara Aikin toilet din tsaf ta'hada kayan wanki dasuke gurin ,kananun kayan kuwa ta zuba su cikin ijin wanki ta kunna shi ,sannan ta ciga da Aikinta ,duk wasu tarkacan su gwangwanin turarurrukan Wanka gami da kwalayen sabulai da sauransu sai da takwashe tsaf cikin wani katon duzbin' tafito dashi can harabar gidan,
Ta koma ta matse kayan da ta zuba cikin Abin wanki ta shanyasu tsaff jikin hangar dake manne a toilet din ,takashe injin,gami da qara wanke toilet din tas sai da ta tabbatar da yayi mata yadda take so sannan tafito tafara Aikin bedroom din cikin Nutsuwar ta
Hijab din jikinta ta cire ganin yana hana ya Aiki kafin ta Ankara tafara jin kiran sallah magariba Cikin sauri ta karasa shimfida bed shirt din ta jera fililon kan tsaff ta karasa kan Mirrow din tafara gyara ka yayyakin dake Kai tsaf ta jere su gwanin sha'awa ta share dakin Tass tafitar da duk wani Abu Mara muhimanci gurin takalmanshi ma tsaff ta gyara masa dakin sai fitar da wani irin qamshi yake mai dadi ,Cikin sauri tafito farlaur din hannunta riqe da wata katuwar Leda da ta zuba tarkacan da ta sharo a dakin ,shaf ta manta da hijab din ta a dakin sabida yadda take sauri kar ta rasa Sallahr magari ba Dan gaskiya maryam bata qara'i Lokacin sallah nayi take gabatar da ita Allah ya huwace mata wannan,
*Allah kasamu a danshinta*
Turus tayi gabanta yana wani mugun duka ,ganin su da tayi a zaune su hudu da Alama shigowarsu kenan Dan ko Alama bataji shigowarsu ba,Nasir ya na kokarin bude dakin suka buga karo,da'ita da sauri ya dago kai hannunshi dafe da goshin Cikin Mamaki yaga Maryam tsaye ta zuba masa idanunta Wanda ya tsana a rayuwarshi,
Da mugun sauri ya koma da baya yana sakin ajiyar zuciya domin ya zata mafarki yakeyi Wanda ya sabayi nata duk daran duniya,yafara nunata da hannu bakinshi na rawa yaga za furta ko kalma daya,
Ganin Abinda yakeyi yasa tace Auncle nice Maryam fa Momy CE tace in zo in gyara maka shashinka yanzu na gyara maka ciki nan nakeso in gyara a nutse take maganar,
Anwar!!

Anwar!!

Ya kwala masa kira Cikin mugun bacin rai!!

Da sauri Anwar ya karaso gurin ,yace kai A boy wannan kira haka kaifa dadi na dakai a kwai takurawa wallah....

Kafin ya karasa idonshi yayi tozali da Maryam tsaye jikin kofar dakin nasir kanta a sunkuye tana wasa da hannuta ,bata son kallon Nasir ganin irin wulakantancan kallon da yakeyi mata,
Gashi babu hijab a jikinta a takure ta ke jinta,sai maqe jikinta takeyi jikin kofar,
Wani murmushi Anwar ya saki yana Sosa Kanshi sai wani kallon kurrula yakewa Maryam tamkar ya lasheta
Tsaki Nasir yaja ,yace ga tsuntsu daga sama ga tanan dama kana nemanta kaga ba sai kasha wahala ba yafada tana yi mata wani Dan iskan kallon raini ,cikin wata muguwar tsawa gami da kyara yace kauce min anan Fockyou mother fourkar!! yafada yana wani tsale tamkar zai kai mata duka,da sauri Maryam ta kauce ta bashi hanya jikinta yana kyarma ,ya zo ya wuce yana wani ya mutse fuska tamkar yaga kashi ,ya kakalo yawo ya taufa mata ajiki ya shige dakin gami da banko kofa,
Jikin kofar ta makale tana takure jikinta ganin yadda Anwar ya ke kusantar ta yana kokarin Rungumeta,
,,,,,,,*
[16/03, 07:01] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*YARO DA KUDI*
WRITTEN BY*
~*Binta umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~
~*MRS AHAMAD GWADABE*~
~*DEDIGATED TO: MY FAN'S*~
Ya karaso daf da ita yana mata wani kallo irin nasu na "yan duniya sai lasar baki yake yi tamkar wani tsuhon maye,
Hannunta ya kama ya riqe cikin nashi yace baby kin hadu fa wallahi babu karya ina son ki kina so na kema?

Yafada yana kanne mata ido daya,
Kauda kan ta tariqa yai ganin fuskarsa dab da tata ,tayi shiru bata ce komai kokarin ta kawai yadda zata gudu daga hannun waddanan Azzaliman,
Sai yafara hade ta da jikin kofar dakin Nasir din da take makale ya sanya hannuwanshi duk biyun yana lalubarta, Bige hannun tayi tana kokarin fashewa da kuka,ya kara mai da hannunshi jikinta a karo na biyu
Sai tafashe da kuka cikin kuka" tace Uncle ka fito ka tai make ni zai keta min haddi ni back"yar iska bace"
Kafin ta rufe bakinta suka fadi rigib!

Ita da Anwar din sakamakon bude kofar da Nasir yayi babu zato ,
Tana kan ruwan cikin Anwar din tana kokarin tashi daga kansa yayi da shi kuma ya sanya duk hannuwanshi biyun ya ruqunqume ta kam!

Tamkar wani Dan dambe haka Nasir yayi kansu a hautsi ne ya daki kafar Anwar da wani mitsayacin takalmi mai ta yoyi da yasanya a kafarshi yanzu domin Wanka ya sakeyi gami da sake wani dressing din domin sake fita,
Ya San ya hannusa guda ya dauke Maryam daga kan Anwar din yana zaginta da turanci ya fidda hannu ya dinga gaura mata tafi tamkar Wanda Allah ya Aiko shi,
A kasalance Anwar ya mike yana kokarin kwatar maryam daga Hanunsa, Ya kai masa wani kutofo,yayi taga taga zai fadi ya tsaya da kafaunsa
Da sauri Abbas da Abdul latif wadanda kecan falo suka karasa gurin domin hayaniyar da sukaji kadan daga can bedroom din Nasir Dan a zatonsu ma ko fada ne ya hautsine a tsakaninsu su biyun.

Ya kara daga hannunsa zai kara kai mata mari Abdul latif ya riqe hannun yana masa wani irin kallo,
Bai ce komai ba ya mai da idonshi kan Maryam dake takure idon ta na zubar da hawaye,
Fizge hannusa yayi yace da Allah malam sakar min hannu wannan "yar iskar yarinyar ni zata nuna wa iskanci Dan Ubanta a dakina za ta kwanta a jikin wannan Dan iskan yafada yana nuna Anwar dake zaune da jiki a mace domin ya Riga yagama kwadaituwa da yarinyar,
Cikin mamaki Abdul ya maida idonshi kan maryam a karo na biyu ,yace" Maryam mai yakawo ki dakin nan ina kuma hijab din ki?

Cikin kuka tace Momy ce tace nazo na sharewa Ancle dakinshi nayi masa gyaragare wallahi,
Ajiyar zuciya ya sauke yace "zo ki wuce ki tafi kin ji ko" dakin Nasir din tayi niyar komawa domin dauko hijab din ta,
A zabure!
Chapter 11 · 0% Book details