← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 80

Sashe 3

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wani bakinci da bacin rai ne yakama Ya'u ganin yadda ilu ya hakikance yana shirya masa qazafi domin shine zai zargi ilun a kan sace kudin in hakane sabida nasa kudin sun nunka na shi yawa Amma dubi Abinda yake fitowa daga bakinshi Dan rashin tawakkali!!
*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:56] +234 808 996 5176:
YARO DA KUDI*
WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)
Haka ilu ya kwana yanawa Ya'u bala'i gami da bakaken mangaganu karshe Dai Ya'u da yagaji shima yafara mai da martani ganin cin mutuchin da Ilu yake masa
Haka suka cigabah da rayuwa babu mai kula da Dan uwansa in gari ya waye ko wanne zai fita har kokinsa gurin kwanciya ne kawai duke haduwa Ilu ya dauki Ya'u da gabah sosai yayinda Ya'u yake bin sa sannu sannu yana mamakin halin ilu na rashin tawakkalinsa Yana masa magana shi domin yafi shi hankali!

Wataran Ya'u ya fito da safe domin tafiya cikin kasuwa sabida sun kwana da Aiki Sauri Sauri yake tafiya Cikin tsautsayi Yazo tsallaka titi wata mota ta kunnu kai ta yi gabah dashi!

Cikin Sauri Mutumin dake cikin motar ya fito cikin tashin hankali yana wa drevar shi fada yace Na Hana irin wannan tukin ganganci Nura wai mai yasa kake yin haka
Kafin Alhji huseen ya karasa gurin tuni Nura Drever ya je yadaga Ya'u yana masa sannu gami da duddubah jikinsa
Alhji ya karaso gurin yana fadi kamashi mutafi a sibiti a dubashi kana Neman ka jawo mana wanin tashin hankalin"
Ya'u ya mike da kafafunsa yana karkade jiki yace babu ciwo a jiki Alh kuyi tafiyarku haka nagode yafada cikin hausarsa da bata fita
Alh Huseen yace A'a dole zamuje a duba ka Aboki ka kwantar da hankalinka shiga mota mutafi
Shi ko Ya'u tsoro ne fall a zuciyarsa ganin Uban motan dake su ke ciki yace a yi haka yalla6e
Nura Drevar yace an yi angama Dan fillo ka kashiga mota babu Abinda zai same ka sai Alkairi
Babu yadda Ya'u ya iya haka ya shiga mota gabanshi na faduwa sanyi ne ya fara damunshi tuni yafara karkarwa Alh huseen yace Nura maza kashe AC din nan da sauri Nura ya cika Umarni Alhji ya kalli Ya'u yace meye sunan Malamin
Cikin nutsuwa Ya'u yace Zakari Ya'u sunana Alh
Masha Allah kai mutumin ina ne da'Alama Bako ne kai a nan ko ?

"Kwarai kuwa Alh Ni mutumin kasar Kamaru Yau wata Hudu a garin nan nafito nema Alh"
*kuyi hakuri dani*
*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:56] +234 808 996 5176:
Masha Allah Zakari Ya'u Allah yabada Abinda a kafito nema yanzu wace kasuwa kake zuwa ko in ce wane aiki kake yi ne?

Ko wane Aiki in yazo inayi Alh muna shiga kasuwa ni da Dan uwa Wanda mukazo tare muyi dako da Abinda ba'a rasa ba
Masha Allah haka A keson mutum mai himma zakari idan babu damuwa zan daukeka Aiki a gida Zaka dinga zama tare da Baban gida a bakin Get za Ku dinga lura da masu shige da fice ina fatan zaka Amince
Shiru Ya'u yayi yana sake sake cikin zuciyarsa
Murmushi Alh huseen yayi yace ko baka Aminta bane Malam Zakari"?

A'a Alh Na A mince Allah yasaka da Alkairi Allah yakara budi Amma zan gayawa Dan Uwana sabida shima yana Neman Aiki duk tare muke fadi tashi dashi"
Babu damuwa Ya'u Allah yashiga mana gaba ka Kwantar da Hankalinka dani domin ni tunda naganka naji ka kwanta min a raina Wallahi ina fatan duk manyanka sunanan lafiya?

Allahu A kabar Ai Allah yayi musu Rasuwa Alh kwananmu Uku a nan garin Annoba ta sauka a kyauyanmu ta barkewar ruwa wacce ta tafi da rayukan Al'uma da dama cikin su har iyaye da "yan Uwa
Allahu Akabar Hakika duk mutumin da ya mutu ta wannan tafarkin yayi shahada tabbas munji wannan labarin watannin baya da suka wuce Allah ya gafarta musu Dan Annabi
Ka kwanta da hankalinka dani ni zan riqe da Amana in Sha Allah
Ya'u yaji dadin karramarwar da Alh huseen yayi masa cikin zuciyarsa yana ta godewa Allah bakinshi yaki rufuwa yana ta godewa Alhji Huseen
To ko da Dr yadubah Ya'u babu Abinda ya sameshi sai "yar kujewa wacce ba'a rasa bah haka yahada masa magunguna kana suka fito
Alh yace Maza Nura ya kaishi ofis ganin lokaci yana Neman wucewa bayan ya ajeshi ya kalli Ya'u dake cikin Mota a zaune yace yanzu Nura zai mayar da kai gida kaje ka huta tukkuna ka bar maganar zuwa kasuwa idan Allah ya kaimu gobe Nura zai zo ya dauke ka ya kaika gidan nawa
Nagode Alh Allah yasaka da Alkairi
"Alh Huseen yaciro kudi Kimanin dubu Hudu zuwa biyar yabawa Ya'u yace kaci Abinci dasu zuwa gobe Allah yasawaqe
Sai godiya Ya'u yake bakinshi yaqi dai nawa sai da Alh yace masa ya'isa haka ya kalli Nura yace kuje Kawai Allah ya stare
Cikin A zama Nura ya juya kan Mota domin cika Umarni Cikin Murmurshi Alh yadagawa Ya'u hannu yace A sauka lafiya Malam zakari Ya'u
Shima nasa hannun yake daga masa Cikin Farin ciki yana ta zubah godiya bakinshi yakasa dai nawa!
*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:57] +234 808 996 5176:
*YARO DA KUDI*
*WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)
Ko da Ya'u ya sanar da ilu halin da 'ake ciki babu Abinda yafito daga bakin ilu sai Wallahi kaje a ka siyar da kanka baburuwa ni bada sa hannu na kuma daka ke cewa ko zanzo muje gidan mutumin tare ni babu inda zani kaje kai garin kwadayinka zaka rasa ranka"
"Ya'u yace babu komai Amma yanda na lura da mutumin yana da imani bashi da mugun hali Dan da yana da mugun hali lokacin da ya bugeni zai ce da mai tukashi a motar suyi tafiyarsu Amma abin mamaki ya tsaya ya kaini Asibiti ya sai mun magunguna kaga ma kudin da yabani yace inci Abinci zuwa gobe"
Ganin irin kudin da Ya'u yafito dasu cikin Aljihunsa yasa gaban ilu faduwa domin a wancan zama in kudin masu yawa ne dadin dadawa kuma dukkanisu basu taba ruqe kudi irin wannan bah
Gaban ilu nafaduwa ya matsa can gefe yana kallon Ya'u yace kai kai Ya'u a INA kasamu wannan kudin Laillai anyi cinikin kan ka an baka kudin Wallahi kaima ban yadda dakai Ba Au da kai za'a hada baki a siyar dani ilu duk ya gigice sai daga murya yake yanaso yatara musu jama'a yacigabah da cewa Laillai dole kabar shagon nan ko in Tona maka Asiri Wallahi bantaba zaton haka halinka yake bah Ya'u
Ganin yadda ilu yake tada jijiyar wuya tasa Ya'u yafara kwantar da Murya yace ka tsaya ka fahimceni ilu babu cuta a tsakinana dakai ka tsaya murafawa kanmu Asiri mutumin nan zai tai makemu ne bashi da niyyar cutarmu
INa! ilu ya kasa fahimatr Ya'u Dan haka baran baran sukayi ganin yadda yake Dada wayar masa da kai yakasa fahimta sai shima yabude masa wuta was he gari baran baran suka rabu lokacin da Nura Drevar yazo daukarsa babu irin sharrin da mugun Alkaba'in da ilu bai jefi Ya'u dashi duk yanajinsa yai masa banza koda suka bar Unguwar Nura Drevar ya kalli shi yace wai yaya kuke da wancan mutumin ne Malam Ya'u naga sai zaginka yake
Ajiyar zuciya Yayi yace Shine Abokin tafiyartawa Wanda nake gayawa Alhji jiya babu yadda banyi dashi Ba ya ki fahimtata Dariya Nura yayi kadan yace ai sai ka rabudashi tunda yaqi ya gane bashi da rabo ne kawai
Allah ya sawaqe shine Abinda ya'u yace ka wai yaja bakinshi yayi shiru yana mamakin irin rashin mutumchin ilu!
Chapter 3 · 0% Book details