← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 80

Sashe 47

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi
"Tambayarka nake fa"
"Momy mubar maganar"
"Naqi bari"
Momy tafada kai tsaye idanta tsaye a kanshi
Murmushi yake shima ya zuba ma ido
Momy tsaf ta fahimci abinda yake damunsa
Tace"My son fitinar ka yawa gareta,Allah ya rufa asiri"
Dariya ce ta subuce masa ya dinga yi
Momy itama dariya take tana girgiza kai
Yace"yau hutawa zanyi Momy babu inda zani"
"Gwara ka huta ai,amma dai dole da yamma kaje gurin Mubina ko"
"Eh Momy yanzu ma sabida ita na kashe wayana sabida tun ina jirgi take takuramin"
Dariya Momy tayi tace"soyayarku a ta mussaman ce"
"Wane irin ta mussaman Momy nifa Sam bata yi min ba wallahi Dan dai kawai Na faranta miki rai ne"
"Nima nasani Myson yarinyar tarbiya bata isheta ba ,amma in dai tana sonka zaka iya juyata kayi mata tarbiya"
Tabe baki yayi yace"wani babban abin haushi ma ,Hanifa kanwarta tana tan tana tada hankalinta sai faman shirme take min a waya wai yaya zanyi mata haka"
"Wace Hanifa kake magana"
Momy tafada cikin mamaki
"Kanwarta, itama wai sona take Mtsss
Momy tayi dariya tace"to Allah ya sawaqe,Allah ya kawomu wani zamani ni "yasu"
"Momy shashanci ne da iskanci kawai babu maganar zamani anan"
"Allah ya kyauta"
Momy tafada
Nan dai suka zauna hira sama -sama har wajejan sha biyu Na dare ,sannan Momy tace yaje ya kwanta
Yana shiga dakinshi ya kunna wayoyinshi nan da nan sakkoni suka rika shigowa, ko sauraron wayar baiyi ba sai da yayi Wanka yayi shirin bacci sannan ya fara duba sakkonin
Message din Mubina sun fi goma tsaki ya ja yafara duba sakkonin mutanenshi, wayarshi tafara kara sunan Mubina yana yawo kan fuskar wayar
Kin dagawa yayi har ta katse , ta kara kira a karo na biyu nan ma saura kiris ta katse ya daga batare da yace komai ba.
[06/06, 01:50] +234 808 996 5176: [03/06/2019 1:18 PM]
Binta Umar Abbale: [03/06/2019 9:22 AM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*104*
Mubina kamar ta fashe da kuka tace"Yanzu Nasir ni kake wulakantawa, nafi sati daya ina kiranka a waya Dan wulakanci kaki dagawa sai yanzu ka gadama"
Tsaki yaja yace"kinga Malam karki dameni, tunda dai na amince shikkenan kuma mai kikeso nayi miki ku so kike in aje aiki in tsaya dan kin kira waya ina sauraron shirme da shiri ririta, karki kara yimin makamanciyar magana irin wannan ya karashe maganar yana Jan tsaki a karo na biyu
Jikinta ne yayi sanyi sosai dama tasan za'ayi haka dashi
Itama sai tau fada tace" kasan bazan jure wannan rashin mutumcin naka ba wallahi
[03/06/2019 1:17 PM]
Binta Umar Abbale: Kashe wayar yayi kawai bai tsaya sauraronta ba zuciyarsa sai zafi takeyi ,sakkonin yake dudduba wani kiran ya kara shigowa wannan baby ce katse kiran yayi nan ma ya cigaba da abinda yakeyi , sai da yaga duba sakkonin sannan ya kira Sofia a waya cikin turanci suke magana, nan ya ke tambayarta yaya aiki dafatan komai babu matsala.

Basu jima suna magana ya kashe waya,
Ya dade kafin bacci ya dauke shi, biyar saura Na asubah ya tashi har an idar da sallahr asubah duk jikinshi a mace yakeyin komai, tun jiya da Momy tafada mishi labarin auran Abdul da Yarinyar jikinshi yayi sanyi nan falo ya zauna yana Jan carbi Momy na sama bata sakko ba Har bacci ya dauke shi bacci mai tartare da damuwa da wahala gami da gajiya
Momy ta sakko kamar ko daushe cikin kwalliya, ta tsaya suna magana da Uwani mai aiki, Uwani tace" naga uban gidana yana bacci a farlo ,Momy ta cikin sauri ta juya tana kallon farlon Nasir ta hango kwance cikin kujera bacci yake sosai da sosai
Wani irin tausayinsa ne ya kama Momy sai ta zauna kusa da kafafunsa tana kallonsa cikin tausayi da kauna irin ta uwa da danta , shi kam bai San ma abinda yake faruwa bacci mai nauyi ne ya daukeshi.
[03/06/2019 2:21 PM]
Binta Umar Abbale: Sai wajan karfe tara da rabi ya tashi , yana bude idonshi ya saukesu kan Momy, cikin mamaki ya mike zaune yana mika ya kalleta gami da cewa "Momy bacci nayi anan"?

"Bacci kayi sosai Myson" Momy tafada tana kallonshi
Agogon hannunshi ya kalla yana mamakin yaya Akayi bacci ya daukeshi a nan batare da ya shirya ba
"Momy bari in yi wanka " yafada yana mikewa
"Sai ka fito My son"
"Ok Momyna"
Cikin sauri ya kammala komai ya fito ,Momy tace"kazo ka karya yau nasa Uwani tayi maka kunun gyada gashinan yaji madara"
"Ok Momy"
Kai tsaye daining din ya nufa Momy ts hada mishi yaji madara sosai tace"ko in zuba maka abinci ne"?

"A'a Momy kunun ma ya isa"
"Kadaure kaci ko yaya ne"
"Momy wannan ma ya'isa kinsan yanayin cikina yanzu sai ya rikice
"Amma dai yau karkayi ciye-ciyen kayan zaqin nan don Allah"
Momy tafada gwanin tausayi
Dariya yake yace"insha Allah Momyna"
Mikewa yayi yana gyara links din hannunsa, yace"zan wuce Momy amma kafin in tafi zan shiga asibitin in ga abinda yake faruwa"
Momy tace"to Allah ya kiyaye hanya a gaida "yan uwa da abokan arziqi, har waje ta rakoshi Giss yana tsaye yana jiran fitowarsa,
Yayi sauri ya karbi wata karamar dake hannun Nasir din , ya bi bayanshi inda motarshi take Momy sai addu'a take ta zabga masa , Tony ya bude masa motar ya shiga da Sauri ya rufe ya zagaya ya bude mazauninshi ya zauna gami da kunna mota suka fice daga gidan
Maryam ce take bin titi a nutse tana sanye cikin atamfa riga da zani mai kalar ja tayi amfani da mayafi kalar atamfar, takalmin dake sanye a kafarta mai tsine ne sosai sabida haka a nutse take tafiya, Maryam najin takaicin tafiyar nan sabida kafin ta fita babban titi akwai tafiya , sosai yawanci dama duk da motoci suke fita in ba lalura ba babu Wanda zaka gani yana tafiya da kafa cikin Estet din tunda guri ne Na wane da wane, so take ta fita babban titi domin ta samu Napep , tayiwa Momy Alkwari zataje yau hospital din, amma in taga da wulakanci bazata jura ba
[06/06, 01:51] +234 808 996 5176: [04/06/2019 9:18 PM]
Binta Umar Abbale: [04/06/2019 7:26 PM]
Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*105*
Tun daga nesa ya fahimci ita ce sai yace ma Tony yaja motar a hankali har suka iso daf da ita, Nasir ya bawa Giss umarni ya fita yayi mata magana da yawonshi, batare da bata lokaci ba Giss ya bude Mora domin cika umarnin da aka bashi.

Maryam gabanta yayi wata muguwar faduwa ganin Giss ya tari gabanta domin baza ta taba mancewa da wannan fuskar ba ,gabanta yana faduwa tace"Lafiya malam kazo ka tare min hanya"?

Cikin yanayi hausarshi yace" oga ne ya bada Umarnin haka"
Cikin mamaki ta tsaya tana kallon motar , ahankali glass din motar yake yin kasa fuskar Nasir ta ban yanna, ya dago kanshi gami da kallonta, ita kuwa gabanta ya rika faduwa tamkar qirjinta ya tsage
Kai tsaye yace"ina zaki je"?

"Ina zakije"?

Maryam ta maimaita maganar cikin mamaki!

Fuskarshi ta kalla taga ya hade fuska tamau!

"Ai kena a kayi"
Maryam tafada kai tsaye
Banzan kallo yayi mata gami da cewa" makaryaciyar banza da wofi, zaki tafi gantali kin dai"
Yafada yana mata wani kallon gani-gani
Maryam ranta yayi mugun baci amma sai ta dake kawai ta kama hanya zata wuce batare da tace komai ba
Nasir yayiwa ma Giss alama ya shigo su tafi dama so yakeyi ya bata mata rai kuma yayi nasara
Haka Tony yazo ya wuce ta fuuuuuu da mota,
Zuciyarta ta dinga wani zafi, tanaji kamar ta juya ta koma gida kawai amma in ta tuno tayiwa Momy alkwari sai zuciyarta ta karaya
Haka ta fita babban titi ta samu Napep ta hau kai tsaye (N Alhussen Specialyst Hospital)
A waje tace ya sauke ta tafito tana gyara zaman mayafinta sannan ta bude handbag din ta tafito da kudinshi ta bashi, sannan ta wuce ciki
Tana shiga taga motashi a harabar gurin a aje Tony a jingeni da ita ,sai gabanta ya ruqa faduwa da tasan nan zaizo wallahi da babu abinda zai kawo ta ,tasan yau za'ayi wulakanci a asibitin
[04/06/2019 8:32 PM]
Binta Umar Abbale: Kafin tagama tunani sai ta hangi Nasir din ya fito tare da Dr Sofia da wasu "yan mata uku a bayansu, kai tsaye gurin motarshi suka nufa sai tayi saurin kauda kanta tana diri-diri kamar ta ruga a guje
Mamaki ya kamashi ganinta a asibitin zuciyarshi yace tazo kenan.

Ganin sun tsaya suna magana ne yasa ta karasawa gurin da suke din cikin turanci tace"sunana Maryam Arma Ya'u
Ta mika Dr Sofia hannu suka gaisa
Dr Sofia ta rika tunanin kamar ta San wannan fuskar sabida kwata-kwata kammanin Maryam din bace mata sukayi
Dr Sofia ta duba takkadun da suke hannunta tana duba sunan domin sai yaga kamar sunan daya, tabbas hakane, tadago kai tana kallonshi gami da cewa "ita ne wannan kenan"?

Daga mata kai yayi kawai yana kokarin barin gurin batare da ya kalli inda Maryam din take tsaye ba kai tsaye motar ya shiga Giss yabi bayanshi Tony yaja suka fice
Kallon kallo ake tsakanin Maryam da Sofia domin sai yanzu Sofia ta gane Maryam din
Cikin turanci tabasu umarnin da su biyo bayanta
Haka suka bita har Maryam din
Nan Dr Sofia tabawa "yan matanan biyu uniporm ko wacce tasan matsayinta, sannan ta kalli Maryam a qasqance
Tace" Ke kuma zaki na mana goge goge da aike-ake a nan in kinga zaki yi to ,za'a biyaki naira Dubu hamsin"
Shiru Maryam tayi tana tunanin kaskancin yayi yawa wato ita ce zata zama Clenar a asibitin bayan tana ganin akwai masu goge -goge a hospital din ba
[04/06/2019 9:17 PM]
Binta Umar Abbale: Cikin turanci tace" Ok, yaushe zan fara aiki"?
Chapter 47 · 0% Book details