← Book details Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 80

Sashe 30

Yaro Da Kudi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Take da jama'a duk suna jira a fito dashi domin suyi masa rakiy
a zuwa ma kwancinsa na gaskiya ,sai jaje sukewa juna suna ta fadar alkairinsa, dayawa daga cikinsu hawaye suke sharewa domin sun gaza daurewa sabida sunsan ba karamin rashi sukayi ba,
Addu'oi Ya'u ya dukkufa yana ta tofawa Nasir ,duk domin ya samu zuciyarsa ta sanyaya, cikin hukumcin ubangiji ya bude idonshi ,ya na binsu da kallo daya bayan daya, kimanin minti biyu,ya mike tsaye cikin nutsuwa ,aunty tayi saurin riko hannunshi,sai Malam Ya dakatar da ita ,yayi mata alamar ta rabu dashi, kai tsaye dakinshi dake farlo ya nufa ,ya bude ya shiga gami da rufo kofar,Momy tabishi da kallo zuciyarta ,tana tsinkewa
Toleit ya bude ya shiga ya dauro alwala ya fito ya kwabe kayan jikinshi, ta cire sarkokin da suke wuyanshi,hade da barimar dake manne a fatar kunnenshi,ya bude katuwar siff dinshi,ya ciro wata jallabiya fara kar da ita ya sanya a jikinshi bayan ya sanya gajeran wando,ya dauki carbi mai ma dan nai
Lokacin da ya fito anfito da dady,"yan uwa suna ta yi mishi addu'a Momynshi na gurfane gaban gawar tana kuka sosai da sosai, cikin jarumta yazo ya janyeta ya zaunar da ita kan kujera, bai cewa kowa komai ba,yafara kokarin daukar dady,ganin haka yasa jama'ar da suke gurin suka mike dama shi suke jira ya fito yayi masa addu'a ,sai suka kama masa makarar ya Dora a kafarshi, suka fita bakinshi dauke da addu'oi iri-iri yana nai mawa dadynshi rahamar Allah.
[16/05/2019 9:05 PM] Binta U Abble: Nan Aunty ta zauna ita da saura jama'a suna ta tausar Momy,kwata-kwata ta manta da Maryam da a ka kai mata ita ranga ranga,sai ganinta sukayi tafado farlo din tamkar zautacciya sai zare ido takeyi dama ga su tubarkallah,
Ta rika bin ilahirin farlou n da kallo, cikin zuciyarta take fadin Allah mafarki takeyi ba gaske bane abinda ta gani cikin mafarkin ta.

Mata tagani zazzaune ko wacce cikin hijabi ga carbi a hannu,da kyar!

Ta samu ta furta,kalarmar da ta fito daga bakinta, Tace"aunty wai da gaske dady ya mutu,wani mummunan mafarki nayi,
Kafin aunty tace komai,Momyn Mubina ta daka mata tsawa ,cikin tsantsan kyama tace" waye sa'anki a gurin nan da zakizo kina mana maganar banza da wofi ko an fada miki ana wasa da mutuwa ne,shegu mayu!

Kun kasheshi kun huta ,mutsiyata, kawai masu mugun abu, sarakan surkulle, Allah wadaran talaka Wanda zaka dauko shi daga rana kai ya mai da kai cikinta, dukiyar Alh kukewa to Baku da gado da ita ,ehe!!

Maryam tayi tsaye bakin kofa tana ji da kallon ikon Allah, ita kwata kwata magangan nun Momy Mubina sam basu dameta ba,illah jin ciwon rashin dady da radadin yadda takasa bin umarninsa na auran tilon danshi wato ancle din ta,har ya koma ga ubangiji ,yanzu ita yaya zatayi da rayuwarta,gashi tanaji a gabanta dady ya bar wasiyar cewar a daura mata aure da Abdul latif duk da tasan ,ba haka yaso ba a zuciyarsa ya mutu ne da burin ganin ya aura Mata Uncle
Hajiya Rakiya wato mahaifiyar Abdul kenan ta rika watsa aunty mugun kallo na tsana, sai tabe baki takeyi,sabida dama can ita macace mai mutukar izza gami da taqama,ta tsani talaka Sam!

A rayuwarta shiyasa ko inuwa bataso ta hada dashi, macace "yar mulki ko shi Mahaifin Abdul din hakuri yake da'ita.
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [17/05/2019 4:00 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*
*76*
Maryam ta zube nan bakin kofar kuka ya kufce!

Mata sosai take yi har da majina,a nan Nasir ya cimma ta, da ya lura ita ce a gurin ka wai ya sanya kafarsa yayi ball da ita,ya yi shigewarsa ciki batare da ya waiwayo ba, ihu ta kurma lokacin da kanta,ya bugu da bango ,ta dafe gurin hawaye wani na bin wani ,dakinsa ya shiga ya fito rike da dadduma ,babu Wanda ya kula a cikin mutanen da suke farlo din ya sakai ya fice Maryam tayi sauri ta bashi hanya ganin yadda ya taho gadan gadan ,
Haka dai akayi zaman makokin dady Auntt da Maryam suna kunsar Bakin ciki gurin mutane domin kowa ya daura mutuwar dady din a wuyansu,gefa guda kuma ga wasiyar da dady ya bari cewar kar su bar gidan,
Nasir kuwa wani irin ya dawo mai shiru shiru sai ya yini ya kwana bai kula kowa ba har Momyn sa tare da "yan uwanta da suke kara kaina a gidan tun safe yake shiryawa ya fice ,kwata kwata yanzu ya dai na saka kananun kaya kullum cikin doguwar Riga yake"yar saudia kanshi da hula irin ta Larabawa sai ya dawo tamkar wani balarabe,kullum zaka Ganshi a masalaci ,nan yake zama yayiwa dadynshi addu'o yana zubar da hawaye, yau tsawon kwanaki goma shabiyar da rasuwar dady din Momy bata ga ko da murmushin sa ba ko magana zai mata ,bata wuce kalma biyar ko kasa da haka ,kwata-kwata baya yin doguwar magana kullum fuskarshi a murtuke abokanshi sunzo mai ta'aziyya mussaman Abbas da Anwar sunji mutuwar dady sosai kadai Anwar in ya tuno rashin kunyar da yayiwa dady din sai jikinshi yayi sanyi,to ko su kansu in sun zo Nasir din baya sakar musu fuska haka zasu karaci shirmensu su tafi,
Bayan sadakar arba'in yafara aiki a asibitinshi domin shine burin dadynshi,yanzu duk abinda yasan dady yana so kafin rasuwarshi shi yakeyi ta mai da gidan fursuna da gidan marayu gurin zuwa bayayin sati daya batare da yaje ba tsakaninshi da Malam Ya'u kuwa gaisuwa ce itama sama sama baya taba yadda wata doguwar hira ta shiga tsakaninsu shi kuwa Malam Ya'u yayi ta janshi da magana wani sa'in yana jinsa yake shareshi Allah sarki Malam baya gajiya da hidima dashi
[17/05/2019 5:14 PM] Binta U Abble: Tun ranar da dady ya mutu rabon da ya sanya Maryam a idonsa, kwata-kwata baya son su hada hanya sabida yadda ya tsane ta tsanar da yake mata ta yanzu taci uwar ta da, shiyasa yake gudun haduwarsu domin yana ganin zai iya kasheta a yadda yake jin zafinta a zuciyarsa,shi gani yakeyi itace silar mutawar dadynshi
Allah sarki Momy duk tayi sanyi itama zuwa yanzu ta fawwala wa Allah komai su Nafi'u da miftahu kullum suna gurin ta suna de mata kewa duk ranar da basu shiga bangaran nata sai ta aika Uwani mai aikinta ko lafiya, wani lokacin kuma suna makaranta,
Auntt ta dauki zafi da Maryam sosai lokacin da mijinta ya warware mata dukkanin abinda ya faru kafin rasuwar dady ,ta dinga yi mata fada sosai da sosai tunda ga ranar Maryam ta dai na ganin dariyarta
Maryam duk jin ta takeyi a takure kullum tana dakinta tayi kuka har ta gode Allah kullum cikin bawa auntt ta hakuri takeyi,aunty tace indai kika ga na hakura to sai kinje kin bawa uncle dinki hakuri,sannan nima zan yafe miki,
Maryam taci alwashin baza ta taba zuwa tabawa uncle hakuri ba sabida ai bai fita jin radadin mutuwar dady ba ,yadda takejin dady a ranta ,gani takeyi tafishi son sa da kaunarsa ,sabida haka ita a ganinta ita ce ya cancanci a bawa hakuri bashi ba
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [18/05/2019 10:31 AM] Bint U Abbale
: *YARO DA KUDI*
*77*
Yanzu duk wasu abubuwa da yakeyi a da marasa kyau ya rage yi ,sallah cikin jam'i bata wuce shi , duk abinda yakeyi lokaci nayi zai nufi masjid ya rage saka kananun kaya, sosai yana saka kayanmu na hausawa, askin da yake kanshi yasa an gyara masa Sosai yanzu ya dawo cikkaken mutum amma duk da haka akidarshi tananan ,ta turawa yana yawan sauraron wakokinsu ,zuwa club ma ya rage ba sosai yake zuwa ba, duk dai wani abinda yasan dady dinshi yanaso kafin rasuwarshi yana kokari ya yi abin , Son matanshi kuma wannan ma tun daga mutuwar dady din bai kara kwanciya da wata yarinya ba,sabida yanzu duk "yan matan nashi tsoro yake basu yadda kullum suka tunkareshi zasu ga fuskarshi babu Rahama ko ta kwabo ,baby ce kamar mayya kullum sai ta bishi asibiti taje ta isheshi da iyayi ,baya ko sauraronta
Yau ta kasance ranar Sunday ce , yana part dinshi a kwance bacci yakeyi Momy ta shiga tana tashinshi , tashi yayi yana dan ya mutse fuska Momy ta karaso ta zauna bakin gadon tana kallon Dan nata tace"My son wannan baccin naka fa yayi yawa dubi time yanzu daya shaura ,ina ta zuba ido shiru baka shigo ba"
Mika yayi yana kallon agogo yace "Wallahi Mom gajiya ce a jikin nan nawa ,kin san tunda nafara aiki bani da lokacin kai na wallahi , yau din ma dole zan fita a kwai wasu mata da nayiwa aiki zan je na dubasu duk da cewar Dr Sofia na kula min dasu amma zuwan nawa yana da muhimanci"
"Hakane Son ai ladanka na gurin Allah, duk Wanda yazo ka taimakama sa ko da kudi ko babu ,kasan wannan shine burin dadynka dama"
Taci gaba da cewa yanzu ma aikin lada zakayi ,Baban gida ne gashi can ciwonshi ya tashi ,muje ka dubashi
Kallon Momy yayi yana murtuke fuska yace"waye baban gida"?
Chapter 30 · 0% Book details