Sashe 9
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Gwaggo ba ta yi shuru ba sai ta kara cewa" Ya gajiyan ku? Kun sha suna. ke ce kawai daman da Sadiya ba ku biyo ta nan ba ranar sunan"
Gum na yi da bakina saboda daman in dai Ma'u na magana ba na saka baki, can na ji ta na ce ma Gwaggo wai mun yi dare ne shi ya sa ba mu biyo ta gidan ba.
 Shi kuma Alhajinmu sai da ya yi rabin da shan shayinsa sannan ya kalli su Yusuf ya na faɗin"Ban yi muku ta yi ba, ko Maimuna ta haɗa muku shayin ne?
Alhaji Mustapha ne ya yi saurin cewa" Mun gode Alhaji."
Yusuf dai bai yi magana ba saboda na ji an kira wayarsa bai É—auka ba ina jin sai ya sakata a silet.
 Ficewa Gwaggo ta yi daga Falon zuwa ɗakinta. Ta bar mu daga mu sai Alhajinmu sai da ya gama shan shayinsa sannan ya kalleni yana faɗin"Dubu kai kofin can madafi"
 Ya faɗa yana mika min mug ɗin hannun shi da ya gama shan tea, sai na miƙe da sauri na karɓa na fita zuwa tsakar gida na tura kofar madafin tun da har Gwaggo ta sakaya ban ijiye ba sai na diɓi ruwa a katon botoki mai murfin ɗin dake cikin madafin na tara a sink na wanke shi, tunda madafin gidanmu ya daɗe da komawa na zamani na kife kofin saman cabinet ɗin kitchen ɗin sannan na fito na sakaya shi kamar yadda na ga Gwaggo ta yi.
 In da na tashi nan na koma na zauna. Sai sannan Alhajimu ya gyara zama ya na sanye da jallabiya mai ruwan madara kansa ba Hula sai furfuran da suka masa kwanya daga kansa suwa gemunsa da sajensa.
"Ma sha Allah, na ji daÉ—in yadda bayan na kira ku kuka amsa kirana. Allah ya yi muku albarka gabaÉ—aya."
Â
Muka amsa da Amin gabaÉ—ayanmu. Alhajinmu ya kalleni sai ya kira sunana da sai irin haka mgana mai muhimmanci ya ke kiran sunana bayan Dubun da yan kirani.
"Halima.."
Sai na É—ago na kalle shi lokaci É—aya ina mai amsawa.
"Na'am Alhajinmu."
Sai ya karkata kan Ma'u itama ya kira sunanta.
"Asma'u.."
 Itama ta amsa da na'am Alhajinmu
Sai ya cigaba da faÉ—in" Kusan dalilin da ya sa na ce ina son ganin ku wannan karon tare da mazajen ku?
Dukkanmu muka girgizanmu kanmu kafin mu haÉ—a baki wajen faÉ—in"A'a Alhajinmu."
 Kai ya gyaɗa kai kafin ya ce"To ba saboda komai ba ne sai dalilin bayan ni kuna da wasu shugabbanin da in kuka yi ba dai dai ba, za su iya yi muku faɗa akan ku gyara kamar yadda ni zan yi muku. Mazajen ku su ne alhakin duka rayuwarku da tarbiyansu yake hannunsu bayan na aura musu ku, shi ya sa wannan karon ganin wannan rigimar da sheɗan ya ba da gudummuwa wajen gina ta a tsakaninku da ta ƙi ci ta ƙi karewa na yi tunanin saka mazajen ku a ciki, saboda ba na so na faɗi na mutu a zaman makokina ke Sadiya da ke Asma'u a ce bakwa yi ma juna mgana akan abin da bai kai ya kawo ba."
 Sai ya dakata ya na nazarin mu, dukkanmu kan mu na ƙasa ba wacce ma ta ɗago. Sai ya karkata hankalinshi zuwa ga mazajen mu.
"Yusufa.
Cikin ladabi ya ce"Na'am Alhaji"
"Mustapha."
Shima cikin ladabi ya amsa da Na'am Alhaji.
 Sai Alhajnmu ya gyara zama ya na faɗin"Ban sani ba ko kun taɓa sanin tsakanin matayen ku ba a ga maciji? Ma'ana ba sa haɗuwa waje ɗaya su yi rabuwan lafiya? Wataƙila za ku iya fahimtar ba sa shiri da juna amman na san ba su taɓa zama sun warware muku lamarin yadda za ku fahimta ba.
 Wannan karon Alhaji Mustapha ya fara faɗin" Haka ne Alhaji. Ban dai san me ya ke haɗa su ba amman Sadiya ba ta zuwa gidana sannan ko haɗuwa muka yi ni da ita in dai ba ni na yi mata mgana ba. Ba za ta yi mini ba, na taɓa tambayan Ma'u ko akwai wani abu a tsakaninta da Sadiya ne amman ba ta ce komai ba"
 Ya karishe faɗa yana kallona, nima ko na ɗago muka kalli juna na kauda kaina domin ba ƙarya ya faɗa ba mun sha haɗuwa da shi gidan Anty Bahijja sai na yi kamar ban gan shi ba in har bashi ya yi mini mgana ba.
"Kai fa Yusufa? Ka taɓa fahimtar wani abu?
Cikin girmamawa ya ce"E. Na fahimci ba shiri tsakaninsu. Amman na É—auka faÉ—a ne kawai na Æ´an'uwa ba mai tsananin da zai haifar da matsala ba ne Alhaji."
 Alhajinmu sai ya sauke numfashi kafin ya ce"Kowa ma haka ya ɗauka daga farko farko. Amman suna ƙara girma lamarin na su na ci gaba, tun suna yara har suka girma na aurar da su gare ku, suka hayayyafa suka zama iyaye sun tashi daga yara sun koma uwaye waɗanda ba zan ce ba su san ciwon kansu ba. Sun sa ni tunda Tarbiya ne ma a ƙarƙashin ikon su, daga lokacin ne na fara fahimtar lamarin ya wuce tunanin zai tsaya anan ina tsoron kada su mutu su bar ƴaƴansu cikin muguwar gaban da sheɗan ya kulla a tsakanin su."
 Dalon sai ya yi shuru, Alhajinmu kuma bayan ya yi shuru na wani lokaci kafin ya cigaba da faɗin"Ba yau ne na saba sulhu tsakanin Halima da Asma'u ba, tun yan'uwansu na yi musu ban sani ba har ya fi karfinsu suka dangana da ni, na yi nasihan da ban baki sai sun ce sun bari amman ba a daɗewa sai an zo an faɗa mini sun haɗu kuma sun yi faɗa. Wannan zaman saboda dalilin faɗan ne da suka haɗu shekaranjiya a gidan sunan ƴar Rahila. Murja ta zo har gida nan ta na faɗa mini a gaban mutane ke Halima kika yi ta ma yar uwanki ɗiban albarka, ita kuma an ce Asma'u haƙuri take ba ma Sadiya amman dai sun sanar dani faɗan dalilin ita ƙawar Asma'un ce da ta je sunan ƴar Rahilan"
 Yusuf ya ce"Subhanallah"
Shi kuma Alhaji Mustpha ya kaÉ—a kai kafin ya ce"Asha. Abu bai yi daÉ—i ba."
Ni ko kaina na ƙasa a raina ina mamakin Yaya Murja, ko miye riban ta na zuwa ta karantama Alhaji komai?
 "Wannan dalilin ya sa na ce zan saka ku a ciki. Gani ga ku zan tambayesu ɗaya bayan ɗaya menene haƙikanin matsalansu da ko da yaushe suka haɗu sai sun yi faɗa? Ko sun manta su ƴan uwan juna ne dangi ɗaya? Ko ke Sadiya kin manta matsayin Asma'u a gare ki ne? Ko ke Asma'u kin manta matsayin Sadiya a gare ki ne?
 Ya ƙarishe faɗa ya na bin mu da kallo, kowaccen mu ta kasa ɗagowa saboda nauyin idanuwan Alhaji a kan mu.
 "Ke Sadiya ke ce Babba da ke zan fara. Ɗago ki kalle ni"
 Ba ni da mafita illa ɗago kaina ina kallon Alhajinmu cikin muryansa a kaushashe da ɓacin rai ya ce"Halima na san halin ki, kina da tsiwa da mgana sannan ke ce daman ko faɗa aka yi dake ko an yi sulhu ba kya hakura ki yi ta gaba saboda daman gaba ba ta yi miki wahala. Ki faɗa mini gani ga Asma'u da mijinki wani irin abu ne Ma'u take yi da ba ki so? Ki faɗa mana sai ta ji ta ba ƙi hakuri ta kuma ɗauki alkwarin za ta daina yi miki saboda ku samu zaman lafiya"
 Shuru na yi na wani lokaci kafin na ce"Alhajinmu ba fa ni kaɗai na tsani Ma'u ba. Itama ta tsane ni tun zuwanta gidan nan ba ta sona nima ba zan maka ƙarya ba ba na sonta Alhaji. In kuma ana son a samu zaman lafiya to Ma'u ta daina bin hanyata ni daman ba ta gabana domin na fi ƙarfinta Alhajinmu ka raba tsakanina da Ma'u don girman Allah."
 Na karishe faɗa har ina haɗa hannu alamun roƙo, gabaɗaya ni suke kallo har Ma'u sai kawai na ga ta fashe da kuka, ban ko razana ba domin kaɗan daga cikin makircin Ma'u kenan.
Yusuf kuma ni ya ke kallona, saboda ya san halina ina da taurin kai, in na kuma ce na tsani abu to da gaske na ke yi ba na son shi.
"Innalillahi ni ko Sadiya me na taɓa miki a rayuwa da kika tsane ni haka?
 Kai tsaye na ce" Ban sani ba. Ke za a tambaya abin da na yi miki kika bi kika addabi rayuwata kina yi mino bita da kulli a wajen iyayena da ƴan'uwana wannan bai isheki ba kin fara yi min ta bangaren dangina mijina wannan bai isheki ba sai kin je kina yamaɗiɗi da ni cewa planning na yi shi yasa har yanzu na ke neman haihuwa ido rufe ban samu ba, har wannan matsiyaciyar ƙawar na ki ta kalli tsabar ido na tana gaya mini mgana."
 Na ƙarishe faɗa cikin tsawa domin nima raina ya ɓaci. Tuna abin da ya faru da a gidan Rahila kaɗai kan haifar mini da ƙuncin zuciya.
 Daga Alhajinmu har su Yusuf shuru kawai suka yi suna kallon mu. Ma'u ta na kuka ƙaryan da ta saba na yaudaran mutane ta fara rantsuwa ta na faɗin" Wallahi tallahi in kin yarda dani Sadiya ban san a ina Shema'u ta ji wannan labarin kuma, a gabanki na yi mata mganar ban ji daɗin abin da ta yi ba, saboda haka ya sa ko yau ta zo gida ta na faman bani haƙuri ban saurareta ba. Har a waya tana ta kirana ban ɗauka ba domin na faɗa mata ba ke ta tozarta ba ni ta tozarta domin abin da ya yi ki shi ya yi ni Sadiya da ni da ke bamu da bambamci"