Sashe 41
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Tun daga wannan ranar Ma'u ta zama yar gida ko na ce tafi ma wasu yan gidan sakewa tun da tama da masu tsaya mata. Da ya ke Rahila tafi mu girman jiki ni kuna siririya ce ina da tsawo ba can can ba amman yanayin fasalin jikin mu ɗaya da Ma'u. Mama ta saka na tsinta kayana na ba ma Ma'u saboda sune za su yi mata kafin Alhajimu ya siya mata wasu kayan saboda wanda ta zo da su duk sun yage an zubar. Sannan Yaya Murja ta yi mata tsifa suka rakata gidan kitso.
Komai fa nuna mata suke yi ga shi ba ta cin Tuwo sai dai in tuwon shinkafa ne miyar ganye. Ba ta cin dambu ba ta shan fate tsirfa dai kala kala kuma an É—aure mata gindi. Duk ranar da aka yi É—aya daga cikin su sai dai a siya mata wani abun ko kuma a dafa mata wani abun ta ci ita yar gata.
Islamiyarmu aka fara saka ta. Sai da aka yi albashi Alhajinmu ya saka ta a makarantar mu ta Goverment Girls Junior Secondary School Diso. Kuma abin mamaki da irin sunan da muke amfani da shi. ASMA'U SULAIMAN YASHE. lokacin da Yaya Abubakar ya kai ta makaranta za a saka sunan Babanta mahaifi sai ta kalli Yaya Abubakar ta na faÉ—in"Ba sunan Alhajinmu za a saka mini ba?
Shi kuma Yaya Abubakar bai yi shawara da kowa ba ya sanya mata sunan Alhajinmu wanda dashi ta ke alfahari har gobe kuma har abada.
 Sai da ya dawo gida ya faɗa Alhajinmu kuma bai ce don menene ba. Ba aji ɗaya aka sanya mu ba mu muna A ita kuma ta na B. Anan ne ta haɗu da Shema'u da daman halinsu yazo ɗaya. Rahila ce ke wani rawan jiki akan Ma'u amman ni sai na iya kirga ma maganarmu yadda ba ta mini mgana nima ba na yi mata kowa harkan gabansa kawai ya ke yi. Tun kafin kowa ya lura ni na fara lura da makircin Ma'u saboda ni ke kula da duka motsinta a gaban mutane saliha ce sai a makaranta in ka ganta tare da ƙawarta ba ka ce ita ce ba. Ban taɓa nuna ta a makaranta na ce ƴar uwata ba ce saboda ni ba ni ma da ƙawaye Rahila ce kaɗai na ke tare da ita. Amman ita Rahila mai jama'a ce kowa nata ne ni kuma ko ana son ƙawancen dani ba na ba da fuska ki gaji da naci ki haƙura ba islamiyan ba bakon ba.
 Sai ya zamanto komai za a yi mana a gida guda uku ne tare da Ma'u. Ta zama yar gaban goshin Yaya Abubakaar shi ke koya mata karatu baya shigowa hannun rabbana sai ya yo mata tsaraba. Sannan Yaya Murja yadda take ƙaunar Ma'u ko ni yar uwanta ba ta sona haka. Alhajinmu ma gata yake nuna mata shi da su Gwaggo. Tun ina mamaki har na daina na sadakar da Ma'u ta samu tasiri mai yawa a zukatan yan gidanmu.
Baaba Hasiya ta zo ta duba Ma'u bayan ta yi wattani huɗu a tare da mu. Lokacin tun ba mu gama zama cikakkun mata ba na ji Baaba na yi ma ƴarta huɗuba da cewa" Kin samu rayuwa mai inganci Asma'u. Ki kwantar da kanki ki yi ma Yaya Sule da Gwaggo biyayya domin ita ce matar Fari. Wancan Rukayyar ba ta gabana. Sannan ki samu cikin yaran nan na Yaya Sule Maza wani ya yaba dake sai ki yi auran ki kin ji ko?
 Ina laɓe ina jin su kuma ba niyyata na yi laɓe ba na zo shiga ɗakin ne na ji suna mgana na tsaya. Ban ankaraa ba sai ga sun fito. Baaba Hasiya daman in dai ta zo a ɗakin Gwaggo ta ke sauka ba ta sauka a ɗakin Mama na taɓa jin tana faɗa ma Alhajinmu a wani zuwa da ta taɓa yi wai Mama mai farar ƙafa ce tun da ya aure ta al'amarinsa ya ja baya tun da ga Lokacin na san ba ta ƙaunar Mama kuma mun taɓa zuwa Yashe a ɗakin Hajiya ta yi ma Mama rashin kunya har Hajiya Dubu na yi mata faɗa ina ƙarama a lokacin amman na ƙasa mantawa da abin.
"Ke lafiya? Ko laɓe kike yi mana"
Baaba ta katse ni tana hararata. Sai na kalleta kafin na kalli Ma'u sai kawai na ga ta yi mini wani kallo kafin ta ce" Daman Baaba ba ta sona. tun da na zo gidan nan."
Sai kawai na saki baki ina kallon Ma'u Baaba kuma ta fara tafa hannu ta na faÉ—in" To ai sai ta kore ki. Shegiya mai mugun hali to Asma'u zama daram in ji mai naguda."
 Maganarta ya jawo hankalin su Mama da Gwaggo Ranar Lahadi kowa na gida.
Baaba sai ta fara kuka tana faɗin labe ta kama ni ina yi musu ta na fitowa ta ganni shine ta fara min faɗa na yi mata rashin kunya har ina zagin Ma'u ina cewa ta zo cin arziƙi ba gidan ubanta ba ne"
 Ban mantawa maganar har sai da ta kai kunnen Alhajinmu. Yaya Murja har ta na marina saboda ta dunguremin kai na ce Allah ya isa ta mare ni. Yaya Abubakar ya saka ni kneel down ban ji ba ban gani ba. Ni kuma ban ƙaryata su ba amman na yi ma Ma'u wani kallo ganin tana yi mini dariya. Alhajinmu ya yi min faɗa fata fata abin da bai taɓa yi min ba yana ƙara jadadda mini Asma'u ba bare ba ce ƴ'a take kamar kowa.
 Ina ji ina gani Ma'u ta zo gidanmu tana mini iko. Sai ta takale ni da faɗa ni kuma ban gane makircinta ba sai na tanka ta shikenan in aka zo jin ba'asi sai ta marairaice ta fara kuka tana faɗin na ce mata in ta gaji ta koma gidan ubanta kafin Ma'u ta rufe shekara a gidanmu har gwammatina a wajen Alhaji ta hambarar da shi da makircinta kowa ba ya faɗin abu mai kyau akaina ko abu ya haɗamu sai ace Ma'u ce mai gaskiya ni ce mara gaskiya.
Har Rahila ce mini ta ke yi" Don Allah Sadiya ki daina takurama Ma'u a cikin gidan nan. Ban ga abun da ta tare ki miki ba."
Itama goyon bayan Ma'un take yi kenan daga lokacin na fahimci gwara na miƙe na kwaci kaina domin ba ni da mai goyon bayana ko Mama ce na je na faɗa mata sai ta ce ni ce ba ni da gaskiya ba mai cewa a tsaya a bincika. Mutum ɗaya ne bai taɓa goyin bayan Ma'u ba shi ne Yaya Hamza lokacin da ya dawo hutu mun taɓa wani dambe da Ma'u akan ina zaune a ƙofar ɗakin mu ina gyaran jakar makaranta ita kuma ta fito wanka. Ga hanya na bata amman da ya ke makira ce sai da ta ga ba kowa a tsakar gidan sai ta takani za ta wuce ni kuma na miƙe na jawota ta baya wajen ta tsaya sai kafartaa ta turguɗe sai ga ta a ƙasa amman yarinyar nan sai ta fasa ihu ana taruwa ta ce ni na saka mata kafa ta faɗi.
Lokacin an saka ranar auran Yaya Murja ita ta saka mini hannu Yaya Hamza ya tsawatar  ashe ya na daga can ƙofar ɗakinsu ya na ganin abin da faruwa.
 "Yaya Hamza Sadiya ta ɗora ma Ma'u karan tsana tun daga ranar da Alhajinmu ya kawo ta gidan nan saboda ta ganta ba ta son tashin hankali."
 Kai tsaye ya kalleta kafin ya ce"Ita ta ce miki ta tsane ta? Ya za a yi ta tsane ta sai dai in akwai abin da take yi mata ne wanda ba ta so."
Yaya Murja za ta yi mgana ya ɗaga mata hannu kafin ya ce"Ki daina ɗaukan bangare ɗaya a matsayinki na babba ki zama adala. Ina can daga ƙofar ɗaki na ga abin da ya faru. Ke ce ba ki da gaskiya ta ba ki hanya amman saboda tonon faɗa kika takata ta miƙe ta jawo ki sai aka yi rashin sa'a kafarki ta turguɗe kika faɗi ko ba haka aka yi ba?
Ya faɗa ya na tsare ta da ido. Duk rashin kunyarta sai ta sadda kai ƙasa ta kasa mgana shi Yaya Hamza akwai tsare gida ba irin Yaya Abubakar ba ne shi kamar wani mace yake jin kansa.
Kai tsaye ya ce Ma'u sai ta bani hakuri dolenta kuma ta bani a kausashe ya kalleta kafin ya ce" Kar ƙi kara takalanta. Ni na san Sadiya ba ta faɗa ba a taɓa ta ba. Ku zauna lafiya da junan ku.'
 Sai ta gyaɗa kai. Ni kuma sai ya riƙe hannuna zuwa ɗakinsa yana lallashina. Tun daman akwai fahimtar juna a tsakanimu. Ina kuka ina faɗa masa makircin Ma'u sai abin ma ya bashi dariya cikin dariyan ya ce" To ke ma ki riƙa ramawa mana. Ki daina bari ta na samun galaba a kan ki."
Shi mamaki ya ke yi Æ´ar Ma'u ta iya makirci tunda ya ganin ma idanuwansa.
 Zaman Yaya Hamza a gida sai na samu lafiyan Ma'u. Tsoron shi take ji ko maganarsa ta ji yanzu za ta shiga taitayinta. In ya na waje ba ta iya wani motsin kirki har sai ya gama hutun shi ya koma tun kuma daga lokacin nima na gane in ta yi mini abu na rama kafin ta kai ga haɗa min makircin ni
Na haɗa mata amman ba ya tasiri tun da ni daman na yi ƙaurin suna sai ya kasance Ma'u ta riƙa cin nasara akaina ko a makaranta in na ganta tare da ƙawayenta suna nuna ni suna dariya barin ma wannan shegiyar ƙawar tata mai kama da biri Shema'u na tsane ta har acikin raina.