Sashe 4
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya na sauke sannan na kalleshi idanuwana sun yi laushi kamar zan yi kuka.
Daƙatawa ya yi da cin abincin ya na mai ƙure ni da ido kafin ya kira sunana cikin yanayin da yakan kirani a duk lokacin da ya ga na shiga damuwa.
"Sadiya."
Na kalle shi amman ban amsa ba cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce" Me ke damun ki ne? Tun fitowata na lura da yanayin ki ya sauya."
Da sauri na yi mirmishi kafin na ce"Haba. Bakomai fa kawai ina tunanin kiran me Alhaji ke yi mana ni da kai?
Ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya saka hannu ya rike min hannuna guda É—aya yana faÉ—in"In dai kan wannan ne karki damu ba komai, ina tunanin kawai kila Alhaji na son ganin ki ne, kin san fa ke dubu ce."
Ya faÉ—a da sigan zolaya duk dai ya sakani dariya kuma sai da na dara, ya manta ko wancan satin ni da yara acan muka yi ni sai dare ya je ya É—auko mu. Amman ba na son na kawo masa mganar Ma'u shi ya sai na bar shi a hakan na san halin shi in har bai ga na saki ba ba zai fita gidan ba ko ya fita to cikin damuwa ne shi ya sa na saki jiki muka karya muna mganganumu na soyayya da muradi kamar yadda muka saba.
Bayan mun gama tare muka koma ciki ya wanke bakinsa nima na wanke duk da ban yi wanka ba. Yana riƙe da hannuna har falo ya ɗauki laptop ɗin sa na karɓa da wayarsa na rike masa shi kuma da key ɗin motarsa a hannu na rakashi har haraban gida na saka masa kayan a gaban mota bangaren mai zaman banza shi kuma ya je ya buɗe get sannan ya dawo ya rumgumeni muka sumbaci juna sannan ya sake ni yana faɗin"Karki damu in na dawo gida da wuri sai mu je mu ga Alhajin ko?
Sai na gyaɗa masa kai, na buɗe masa gaban mota ya shiga ina ɗaga masa hannu yana ɗaga mini har ya fita daga gidan ya tsaya sai da ya fito ya rufe get ɗin ya ɗaga mini hannu nima na ɗaga masa a fili na furta"Allah ya dawo mini da kai lafiya yallaɓai na."
Cikin gida na koma na zauna a falo kawai rumgume da cussion ina tunanin rayuwa, na ɗan lokaci sannan na tashi na koma ɗaki na yi wanka na yi shigar doguwar rigar wani material mai maroon da baki sai na saka baƙar hula, ina cikin shiryawan na ji ana buga get daman na ce Saude ce ganin shuru ya sa sai ta kira wayata ina ɗauke da wayar na fita zuwa can haraban gidan na buɗe mata kofar, wata yar budurwa ta shigo tana a faɗin.
" Anty hala barci kike yi ne ina ta bugu ba ki ji ba?
Kai tsaye na ce"A'a na yi wanka ne ina kan shiri ne."
Gaisheni ta yi na amsa ina faÉ—in" Ya su Balaraban ? Ta amsa min da lafiyan lau suna gaisheni.
Ina gaba tana bin bayana har cikin gida falo na biyu na shiga bayan na kalli Saude ina faɗin"Akwai sauran abin ƙaryawa a dining ki ci sannan ki fara aikin"
Da to ta amsa min sannan na shige ciki na rufe ƙofa. Saude kenan mai zuwa tana mini aikacen aikacen cikin gida. A can anguwan mu na Ɗorayi ta ke, makota suke da gidanmu.
Saboda ba na son zaman shuru ya sa na kunna Tibin a tashar MBC3 ina ga Baby ta kunna sai ban sauya ba suna haska cartoon ina kallo saboda yara. Ya É—an fara É—aukan hankalina kiran wayata ya katse ni ina duba mai kira sai na ga RAHILANMU ce ke kirana.
Karamin tsaki na ja har sai da ta katse ban ɗaga ba sai da ta ƙara kira gabda za ta katse sannan na ɗaga bayan na saka a amsa kuwwa a fusace ina faɗin" Wai me zan yi miki tun jiya kike ta faman kirana?
Daga can bangaren Rahila ta ce" Kai Sadiya daman kina ganin ina kiran ki shi ne kika ki É—auka? Kai tsaye na ce"To me zan yi miki?
Rahila ba ta ji haushi ba ta ce" Yi haƙuri na ga jiya ba ki dawo ba ne Sadiya."
Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce" To na zo na yi miki mene Rahila? Ai Ma'u na nan za ta iya miki abin da ni ba zan miki ba ma."
Daga can bangaren Rahila ta ce"Haba Haba Sadiya wai ke abu ba ya wucewa a wajem ki? Jiya nan fa Ma'u har da kukanta ta ce ita wallahi ba ta ji daÉ—in abin da ya faru a tsakanin ku da shema'u ba a gabanmu fa har da yaya Murja ta kira ki baki É—auka ba, me kike so a yi miki Sadiya.?
Karamin tsaki na ja kafin na ce" Munafuka kawai,."
Rahila ta ce"Don Allah Sadiya ki daina wannan ƙiyayar ga Ma'u. Yar uwanki ce fa."
Rahila ta magana kamar na kifa mata mari ta cikin wayar haka na riƙa ji.
Wai Ma'u ta na kuka a gabansu Yaya Murja, takaici ya hana ni mgana ina jin Rahila na ta wa'azin ta na fama akan na manta komai na rumgumi Ma'u.
A fusace na ce"Allah ya tsari Sadiya da ta rumgumi Ma'u. Kamar yadda ba na kaunarta itama ba ta ƙaunata amman kun kasa ganewa, shi ya sa har da Alhajimu kuka haɗa ni, ku kuka sani ga ku ga Ma'un nan tunda kuka zaɓe ta shikenan amman in dai ta na waje ina waje sai dai ɗaya ya hakura ya bar ma ɗaya."
Rahila ta ce"Ni ban gaya ma Alhaji ba sai dai in su Yaya Murja ne."
Baƙi na taɓe kafin nace"Koma waye ku kuka sani. Ai an taɓa yar gwal dole a je a kai ƙarana wajen Alhajin mu mana"
Rahila ta sauke kai tana faÉ—in" To ki yi hakuri Sadiya don Allah."
Kamar ba zan yi mgana ba sai can na ce"Uhm"
Rahila ta yi dariya kafin ta ce"Sadiyar Dubu tawa, ga naman sunan ki a hannuna fa."
Kai tsaye na ce" Ban so. Ki haÉ—a ma Ma'u duka ki aika mata."
Ban ba ta ma zarafin mgana ba na yanke kiran ina ƙara jin takaicin kaina da na tsaya ma ina sauraranta alhalin nasan Rahila ta fi shaidar Ma'u sama da ni da muke jini ɗaya.
Ƙwafa na yi a raina ina tunanin in muka je gaban Alhajinmu zan fito masa a mutum kawai gwara ya raba tsakani na da Ma'u kowa ya yi sabgarsa zai fi alheri.
*Janafty.*
*25/09/2024*
*11.03am.
*Wednesday 07/05/2025*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY).*
*FATAN ALHERI GA AMINIYATA AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH), ITA ÆŠIN TA DABAM CE A WAJENA. NA GAISHE KI*
*NA GAISHE DA IYAYEN ÆŠAKINA*
*ZAINAB INUWA(AUNTYSIS)*
*HAJIYA LUBABATU MUSA*
*KHADIJA SALISU YUSUF(UMMINA)*
*HAJIYA HABIBA ABUBAKAR IMAM*
*ANTY AISHA AHMAD IYA*
*ANTY ZAINAB ABDULWAHAB*
*HAJIYA HALIMA ÆŠALHA SHEHU.*
*ANTY HADIZA MAHE MUHAMMAD*
*ANTY HAIRI*
*ANTY FADILA KABIR*
*ANTY FIDDAUSI KABIR*
*FATAN ALHERI NA GODE*
*JINJINAN TURKEN GIDA ZUWA GARE KU*
*MARYAM JUMARE.*
*MARYAM(KITTY)*
*HAFSAT HAFNAN(SAHIBATU)*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z
*🅿ï¸02*
Ina zaune a wajen Rahila ta ƙara kirana sai na danna mata busy. Ina mai ƙara sakin tsaki ni kaɗai ƙara miƙe kafata na yi a saman kujera mai zaman mutum biyun da nake zaune akai ina mai ƙara jin wani takaicin na ƙara cika min zuciyata. Rahila ba ta haƙura ba sai da ta ƙara kirana har wajen sau uku ina kashewa sannan daga ƙarshe sai ta turamin saƙo.
Na ba ma Hubby saƙon ki da zai fita, zai biya gidan Bulo ya ba ma Musabahu. Zai kawo miki ko kuma in ya haɗu da Yallaban na ƙi ya bashi ya kawo miki. Ki yi haƙuri."
 Ba saƙon ne ya ba ni dariya ba sai Hubby da na ga Rahila ta rubuto mini shi ne ya sa ni tsintsirewa da wata dariya mai sauti wanda har sai da Saude da ke kichen ta leƙo tana faɗin"Lafiya Anty?
Ina dariya na É—aga mata hannu ina faÉ—in"Bakomai Saude. Ci gaba da aikin ki."
Sai ta amsa min da kai ta maida ƙofar kitchen ɗin ta rufe ta bar ni nan zaune ina ta faman dariya. Wai Yaya Muntarin ne Hubby kai in na tuna da sunan ma sai na ji wata ƙarin dariya ni dai ban taɓa katarin Rahila ta kira shi da wannan sunan ba. Baban Islam na san tana kiran shi dashi ko Yaya Muktar ɗin da ta lankayamai amman yau shi ne karon farko da na taɓa jin ta kira shi da sunan Hubby.
 Ina dariya ina tuna wani zamani a can baya ina jin na kasa riƙe dariyata. Har sake karanta saƙon na yi ina dariya a fili na furta" Tab! su Rahila masu Hubby manya."
Saƙon Rahila shi ya tafi da kaso mafi girman ɓacin rai na, har na ji zuciyata ta yi sanyi, ban jima a falon ba na miƙe dauke da wayata ta kitchen na bi saboda daga kichen ɗin akwai ƙofar da za ta sadani da ƙofar koridin Bedrooms ɗina.
 Saude na gani a rakuɓe kamar wata bakuwa tana cin doya, a tsugunne ba ta san ma na shigo ba a saman kanta ta ɗago kawai ta ganni harara na ɓalla mata kafin na ce" Wai ban hana ki wannan ɗabi'ar ba Saude? Nan gidan baƙon ki ne? Cin abinci a tsugunne kamar an hana ki zama a in da kika ga dama?
 Da sauri ta ɗago tana faɗin" Yi hakuri Anty, daman na ga ina sauri ne shi ya sa ban zauna ba." Ƙaramin tsaki na ja kafin na wuce ina faɗin"Ke dai kika sani, ki kuma cire hijabin nan saura na fito na ga kina aiki dashi kamar wata yar gudun hijira ki ga yadda za mu kwashe da ke a cikin a gidan nan."