Sashe 65
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan wata ɗaya da bikin Yaya Usman. Kuma a yanzu dai muna cikin watan ramadan ne har mun yi azumi takwas. Da azumi ya gabato Yallaɓai bashi da kuɗi a hannu ya samu kwangilan aikin nan na kaduna akwai kuɗin shi da ya saka a ciki, to kuma ya saba duk shekara ana yi masa kunin sadaka Maman Saude sannan yana rabama yaran dake ƙarkashin sa kuɗi ko kayan abinci.
 Wannan karon ma da bai da kuɗi kayan abinci mu a ciki ya ce. A ɗibar ma Mutakka da gidan su Saude. Yaran shi na Office kuma kuɗi ya ba su, sannan gidanmu kuma 30k ya ba ni na kai musu da ƙwai da yawa da dankalin turawa wanda Uncle Abba ya kawo mana an cire ƙwai a gidan gonan shi Dankalin ma shi ya kawo mana buhu a ciki na dibar ma gidanmu da Muttaƙa.
Nene ma Uncle Abba ya kawo mata kwai da kayan gona muma ma mun shaida su kwaiba da mangaro har muna kyauta. Muttaƙa ma Hauwa ta ce ya samu alheri tunda shi kaɗai ne bai kai su karfi ba. Geron da Mijin Mimisco ya raba ma su Yallabai a ciki ya ce na diɓar ma su Gwaggo sauran kuma a ka kaima Balaraba na kunun Sadaka. Duk da daman a gidanmu ba mu da matsala komai akwai Yaya Hamza da Yaya Auwalu da suke da ƙarfi sun wadata su da komai, sai dai ihsani da kyauttawa namu amatsayin su na iyayenmu.
Mijin Amina ma ya aiko da kuÉ—i sauran alherin da aka samu ta bangaren su Yaya Balki an tura shi can Yashe wajen su Baba Sani. Ko Mijin Ma'u mota guda ya kawo na kayan abinci Baaba ai tana cikin alheri shi ya sa Yaya Aina ta ce a can kura Baaba ce yar gaban goshi to tana da Æ´a tana auren mai kuÉ—i kuma ana aika musu da alheri. Ni Rahila ke faÉ—a,mini har dangin Babanta da azumin nan ta kai musu alheri.
Gimbiya ta dawo wajen Nene da zama saboda aikinta. Sun je Abuja tare da ƙanin mahaifinta Tafidan Rano an raba gadon dukiya ta samu gida biyi anan Abuja da kuɗi masu yawa na tumanin takaba dukkansu huɗun rabon su kenan. Su gwara su da ƴaya ita bayan tumin takaba ba ta samu komai ba. Yallabai na ji suna waya kan tana son a saida gida guda ɗaya a siya mata a fili anan kano kuɗin ta kuma Mota ta ke son siya. Da ya ke komai sai ta yi shawara da shi abin da ya ce kar a yi ta bar shi kenan wanda ya ce a yi kuma shi take yi. Ta ɗan yi facaka da ƙudin bayan Mota ta siya manyan suturu da gwala gwalai, har su Jidda ta siya ma Takalma da dogayen riguna daga Dubai oder ma ta yi, sai yan uwa suka yi mata faɗa suka ce ta fara tunanin kasuwancin da za ta fara tunda kuɗin gado kamar ruwa su ke za su ƙare ba tare da ta yi komai da su ba.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/FAtGNQc8Y8pB008TuxFJVo
Eaman ScholarSphere.
Where ideas Take Shape.
WHAT WE DO.
ASSIGNMENT
PRESENTATIONS.
ARTICLES
PROJECTS.
BOOK
AND MANY MORE.
CANTACT US THROUGH.
02347067793152
MOTTO:
"Pathways of Knowlodge Academy, Nurturing minds, illuminating Futures"
*🅿ï¸18*
Azumi ya raba tsakiya, mun gama goma na marmari mun shiga goma na wuya kamar yadda hausawa ke faÉ—i.
Yau in muka kai azumi mun kai sha biyar kenan, a duka shekarun da muka kwashe da aure ni da Yallaɓai na saba duk watan ramadana Yallaɓai ba ya kaiwa dare a waje a gida ya ke yin buɗe baki tare damu haka ya sabar mana kuma nima haka na saba.
 Amma wannan azumin sai al'amarin ya ɗan sauya. Saboda ya samu kwangila gina ma'aikatan nan na kaduna gabaɗaya ma'aikatan shi suna can kaduna shima yana zuwa har ya kwana ma kafin ya dawo sai ya zama na in baya gari sai dai mu yi buɗe baki tare da yara. Ranar da muka kai azumi na sha uku ya dawo daga Kaduna na yi masa har kunin tsamiya da ya ke matuƙar so, amman bai shigo gidan ba sai wajen tara na dare. Na kira shi a waya na ji ko bai dawo daga kadunan ba ne? Sai ya ce mini ya dawo ya na Gwammaja da ya faɗa mini haka har a cikin raina ban yi zargin wani abu ba, sai da ya dawo na kawo masa abin buɗe baki bai ci abinci ba,kunin ma kaɗan ya sha ya ce mini cikin shi ya cika a lokacin sai da na yi mamaki sanin Yallaɓai ba ya iya cin komai a waje sai ya dawo gida barin ma da azumi saboda ya san ina gida na shirya masa abin buɗe baki kamar yadda na saba.
"Ka ci wani abu ne a can Gwammaja?
Tambayar da na yi masa a lokacin kenan. Shi kuma kai tsaye ya ce mini Nene ce ta matsa masa sai da ya tsaya ya yi buɗe baki. Na ɗan yi mamaki saboda hakan bai taɓa faruwa ba ai Nene ta san ya na da mata me ya sa za ta ce sai ya yi buɗe baki a wajenta? Amma sai wata zuciya ta kitsa min kyakyawan Niyya cewa ita ɗin uwa ce a gare shi ta na da wannan damar kuma abu na rana ɗaya. Sai ko a fuska ban nuna masa damuwata ba na basar da komai ya wuce sannan ya faran tamin rai da ya ce da Asuba na ɗumama masa kuninshi ya na so ya yi sahur da shi.
 Haka ko aka yi da asuba bai ci komai ba kunin na ɗumama masa ya sha da buredi ni kuma da yara muka sha tea sai na soya mana ƙwai muka haɗa da shi. Ranar kuma da wuri ya dawo gida muka yi buɗe baki tare ana kiran sallar isha'i ya yi alwala ya tafi masallaci bai dawo ba sai da ya tsaya ya yi sallar tarawihi kamar yadda ya saba ni kuma ni da yara daman muke yin namu a gida.
Sannan da rana kuma da ba na komai sai na yi ta karatun Qur'ani tunda duk watan Ramadan in ya zagayo sai na yi sauka kamar yadda na saba.
*****
Saude tana zuwa da safe ta yi min yan aikace aikace sannan ta É—an rage mini aikin yamma tunda kafin la'asar ta ke komawa gida sauran aikin kuma ni na ke yi Jidda na kama min É—an abin da ba a rasa ba.
Yau alale na yi mana mai kifi da ƙwai sai na yi mana zoɓo, Yallaɓai ya aiko da kayan ciki sai na yi ferfesu shi kuma sai na dafa masa ruwan tea da ya ji kayan ganyen shayi na citta saboda ya na so duk dare Yallaɓai zai sha kafin ya kwanta. Muna da kayan marmari sai na ce Jidda ta raba biyu sauran kuma su yi fruit salat ni da Yallaɓai kuma sai na yayyaka mana tunda shi ya fi son cin su a haka. Bayan mun gama haɗa komai na bar ma Jidda gyara Kitchen ɗin amma bayan na haɗa duka kayan buɗe baki a falon su Jidda in da muke zama gabaɗayan mu a saman cafet mu yi buɗe bakin tare.
Wanka na je na yi, saboda na gaji kuma yau É—in nan ina É—an jin azumin nan kaÉ—an ina fitowa wanka ana kiran salla daman ina da Dabino a É—aki na yi buÉ—e baki Jidda ma na san ta yi na ta Baby dai daman azuminta rabi da rabi ne in ta É—auka da ta yi rabi sai ta fara kukan yunwa Babanta kuma ya ce ta ci abincinta da cewa ta yi rabi gobe ma in ta yi rabi É—aya kenan. Sai da na saka wata doguwar rigata na Atamfa sannan na ta da salla daman na É—auro alwala ina cikin sallar na ji ana kiran wayata sai da na idar na jawo na duba sai na ga Amina ce sai da na shafa salatin da fara sannan na kira ta daga baya.
 Mun gaisa ne ta yi mini barka da shan ruwa. Mu ɗan tambayi lafiyan juna kafin mu yi sallama Amina akwai ƙokari tunda aka shiga watan Ramadan duk bayan kwana biyu sai ta kirani ta yi mini barka da shan ruwa ita da Rahila suna da wannan ƙoƙarin a gidanmu. Ni ma dai farkon watan na kira duka yan gidanmu na yi musu barka da shigowa watan Ramadana wata mai albarka har Ma'u sai da na kira ban wareta ba wannan karon sannan Alhajinmu ma mun yi waya dashi sau uku kenan shi da Gwaggo saboda tun ranar da muka kai azumi na uku da na je gidan kai musu saƙon Yallaɓai ban ƙara komawa ba washegari kuma na je Gwammaja na gaishe da Nene tun daga kuma ranar ne ban ƙara fita ba.
 Wayar ta ɗan dauke min hankali na buɗe data ina ganin masu turamin saƙon Happy iftar group ɗin Gidanmu na shiga na ga Ya Abubakar ya turo addu'a daman shi ke da wannan ƙoƙarin Ya Hamza ya yi tagging ya ce Allah ya ba da lada. Sai ni ma na yi Tagging na ce Amin tare de cewa fatan mun sha ruwa lafiya? duk ba sa kusa da wayarsu tun da an sha ruwa ana can ana hada hadar buɗe baki sai nima na fita daga nan na ɗan duba saƙonnin private sai na ga Munnira ta yi min mgana da cewa Matar Yallaɓai sai na tura mata da amsa da cewa matar ƙanin Yallaɓai sannan na saka mata emojin dariya na fita. Datar na kashe na ijiye wayar saman gado sannan na cire hijabin jikina na ninke ina mamakin me ya tsaida Yallaɓai har yanzu bai dawo ba? Tunda Office ya je bai ma fita da wuri ba sai bayan da a ka yi sallar azahar.