Sashe 29
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya na sauke kawai a raina ina fatan kafin komai ya ƙare Allah ya kawo wata mafitar. Tunanin yin Tuwo ya kawo mini acikin raina sai na duba naga ina da kuɓewa ɗanya da Gwaggo ta ba ni wacce ta taho da ita daga Yashe ne sau ɗaya na yi amfani da ita tunda Yallabaina ba ma'abocin cin tuwo ba ne sai bayan lokaci lokaci haka.  Ban yi kai tsaye ba sai da na koma ɗaki na kira Yallaɓai na na ce masa yau Tuwo na ke so na yi ko yana so na dafa masa wani abincin ne?
 "Sadiya na daɗe ban ci tuwo ba. Ina marmarin shi."
Amsar da ya bani kenan. Sai na yi mirmishi kafin na ce"To zan ɗora tuwon yanzu. Ka taho min da ƙashi ko Nama wanda zan yi miyan dashi."
Sai ya amsa min da toh, tunda yau ba Rano ya je ba Office ya je.
 Da ƙarsashina na koma kitchen na ɗora ruwan Tuwo a saman Gas. Yara kuma na yi tunanin su sha wani abun kafin na gama girkin, ina cikin tunanin su sai na ji buga get na san sune tunda shidda saura a lokacin. Ni na je na buɗe musu kofa har Salisu ya tafi bayan ya sauke su. Tare muka shigo cikin gida da su ina tafe riƙe da jakar Baby da lunch box ɗin ta.
 Bayan sun sauya kaya na ce su zo su sha ko goldemorn ne tunda corflex ya ƙare shima sai kwali kafin in gama abinci Baby ce ta biyo ni kitchen ɗin ta na faɗin" Umma me kike dafawa?
Kai tsaye na ce"Tuwo."
"Tuwo?
 Ta faɗa ta na kwabe fuska. Sai ta bar ni ina ta mata dariya daman na san ba ta son tuwo sai na lallasheta na cewa ina da sauran miya zan ce ma Yallaɓai ya taho da buredi sai ta ci dashi jin haka yasa ta yi tsallen murna. Ko kafin mangariba na gama Tuwo tunda na shinkafa ne har na mulmule a leda Jidda ce ma ta taya ni ɗaurewa a ledan muna yi ina nuna mata in da ba ta yi dai dai ba ta na gyarawa.
 Miyan na ɗora daman na yi greting ɗin kayan miya daddawa daman ina da dakakkiya ban mantawa Inna Mariya ta aiko mini dashi. Sai na ɗan zuba ruwan da yawa saboda ban san lokacin da saƙon Yallabai da zai iso ba. Tare da yarana muka yi sallah a ɗakinsu na zauna muna karanta azkar tare sakamakon na daɗe ban yi musu karatu ba ya sa na ce kowacce ta ɗauko Qur'ani mu yi karatu.
 Na biya ma Jidda na ta Baby ne muke yi lokacin da Yallaɓai ya shigo ɗakin na yi mamakin ganinsa yau da wuri haka. Ya na tsaye bakin kofa sanye da wani farin yadi kansa da hula ta zanna mai kalan aikin jikin yadin. Mirmishi a saman fuskarsa ga leda a hannunsa ɗayan hannun kuma key ɗin mota da sai wayarsa.
"Sannu da zuwa."
 Na faɗa ina kallon shi lokaci ɗaya nima ina maida masa martanin mirmishin. Baby ce ta tsshi ta isa wajensa ta na masa oyoyo Jidda kuma daga zaunen ta ce"Sannu da zuwa Abba."
Ya amsa lokaci ɗaya yana ce ma Baby" Kar ki ɓata jikin ki." Ya faɗa ya na nuna mata ledan hannun shi.
Miƙewa na yi na isa wajen shi ina faɗin" Ban ɗauka za ka dawo yanzu ba. Na ma za ta Musabahu za ka aiko."
 Kai ya girgizamin kafin ya ce"Kawai na ga ba wani aiki ne shi ya sa na ce bari na dawo gidan kawai.'
Ya faɗa ya na miƙamin ledan na karɓa lokaci ɗaya ina kallon Baby da ke riƙe da hannun babanta."
 "Je ku gama karatun Baby."
 Kumatunta ya shafa kafin ya ce"Je ki. In an gama karatu ki zo ki karɓi tsarabanki."
Jin haka yasa ta wuce da gudu ta na dariya muka bita da kallo gabaɗayanmu cikin ƙauna gaban Jidda ta koma ta zauna ta ɗauki Qur'aninta ta na karantawa da karfi.
Ni da Yallaɓai muka fita ina gaba ya na bin bayana shi ya rufe musu ƙofar.
 Tare muka shiga har kitchen ina buɗe naman.
"Ko da na je duk sun gasa sai wannan na samu na 3k ne zai isa?
Yallaɓai ya faɗa ya na sunkuyo da kansa ta ɓarayin wuyana. Kai na jinjina kafin na ce" Zai yi mana. Miya ce ba yawa sosai."
 Sai da na saka naman duka a cikin miyan ina juyowa Yallaɓai ya rumgumeni ta baya lokaci ɗaya ya na faɗin" Yau ko ɗan hug ɗin oyoyo ba a yi min ba ko?
Ina mirmishi na ce"To ka jira ka ga ban yi maka ba ne? Na faÉ—a ina wucewa wajen sink in da na buÉ—e famfo na tara hannuna ina wankewa shima sai ya sunkunyo da kansa ta wajen wuyana lokaci É—aya ya zuro hannayensa duka biyu ya kama nawa yana murzawa a tare ruwa na zubar mana.
"Nima a wanke min hannun mana Sadiya ta."
 Ya faɗa cikin raɗa sai na yi yar dariya na karɓi hannun ina murza masa na wani lokaci kafin na kashe famfon ƙaramin Towel ɗin da ke kitchen na ɗauka ina goge masa hannunsa. Nima na goge nawa hannun sannan na yi masa rumgumar da ya yi min ƙorafi shi kuma ya ɗago ya sumbaci goshina.
  Ta falo muka fita na ɗauko masa wayarsa da key ɗin mota muka wuce cikin ɗaki. Wanka ya ce zai yi amman da ruwan sanyi saboda garin akwai zafi zafi mun fita damina an fara zafin nan na fiddan dawa. Shi ya shiga wanka ni kuma sai na koma kitchen ina duba miyata da na saka mata kalolin maggi. An kira isha'i Yallaɓai bayan ya fito wanka ya saka Jallabiya ya tafi masallaci ni kuma da yara muka yi a gida. Da zai shigo ne ya shigo da ice cream ɗin da ya siyo ma Baby ita kuma Jidda wani bickit mai madara mai ɗan karan daɗi lokacin har na kaɗa miyata na gyara kitchen ɗin ina jin shigowarsa na faɗa wanka.
 Har na gama shiryawa yana falo tare da yara. Ni kuma sai na tsuke cikin riga da wando. Wando ya kamani ta sama amman ya na da buɗewa ta ƙasa rigar ma tana buɗewa ta ƙasa. Wandon baki ne rigar fara sai na yi amfani da bakar hula a kaina ban fesa turare jiki kuma na shafa humra har da jan baki na saka na yi ɗas da ni ina fitowa falo wajen ya ɗauka da kamshi. Jidda na kira ta tayani ɗaukan kaya zuwa Dinning. Baby ta samu ice cream tuni ta manta da mganar Biredi ni kaina na manta ban kira Yallaɓai ban ba a lokacin.
 Gabaɗayanmu muka haɗu a saman dining ɗin ban da Baby da ke can falo ta na kallo. Da kaina na saka ma Yallabai guda biyu na zuba masa miyar da ta ji naman rago Jidda ma ta saka ɗaya ta ce ya isheta nima dai ɗayan na saka saboda na ci abinci a gidan Halima.
"Sadiya ta. Kin yi kyau.''
Haka Yallaɓai ya faɗa yana kallona da mirmishi a saman fuskarsa. Fari na yi masa da ido kafin na ce"Thank you Yallaɓan Sadiya."
Jidda na cin tuwon ta ba ta ɗago ba amman ta yi mirmishi. Yallaɓai ya kalleta kafin ya ce"Hajiya Nene ko Umma ba ta yi kyau ba?
Da sauri ta ce" Ta yi kyau sosai Abba." Ya na ƴar dariya ya ce"To ai shi ne na yaba kuma sai na ga kamar ta cancanci tuƙwaici ko?
 Jai ta gyaɗa masa ta na mirmishi ina jin su ban ce komai ba sai da na ji ya ce"Kar ki damu zan ba ta kyakyawan tuƙwaici"
Ɗagowa na yi ina hararanshi kafin na saka kafata na taka masa kafa sai ya janye yana dariya. Jidda dai ta gama cin tuwonta ta ɗauki filet ɗin ta bar mana Falon sai da ta fita na kalle shi kafin na ce" A gaban Jiddan ka ke mganar tuƙwaici?
Kai ya gyaɗa kafin ya ce"To miye a ciki? Ai ba ta san irin tuƙwaicin da kike karɓa ba madam"
Wani kallo na yi masa da ya sa sai da ya ƙware yana shan ruwa na yi masa gwalo ina dariya amman sai da na saka hannuna ta bayansa ina shafawa ganin ya sarƙe da yawa. Wani ruwan na sake zuba masa na bashi ya sha sannan ya ɗan lafa masa.
 Kallona ya yi kafin ya ce" Ki riƙa bari sai mun shiga ɗaki sai ki yi mini wannan kallon kin ji ko?
Ina dariya ban yi mgana ba shi kuma ya ce" Saboda tsaro ba."
 Murguɗa masa baki na yi shi kuma sai ya kaɗa kai kafin ya ce"Murgaɗa da kyau za ki yi bayani ne yarinya in na fara gyara miki service ɗinki har da garambahul."
Marairaicewa na yi ina faɗin" Mai jan mota ya tokare boda yau Yallaɓai."
Kai tsaye ya ce"ko jan jirgi ne yau sai na gyara miki service É—in ki."
Dariya na yi shi kuma yana faÉ—in" Yi dariya da kyau."
Ni ko na ce to kuka zan yi? Ya na min wani kallo ya ce" A'a shi wannan ki bari sai anjuma."
 Kafarsa na taka ina faɗin" Yallaɓai cikin shagwaɓa "
Da sauri ya miƙe yana faɗin" Yau wannan shagwaɓar taki ba amfanin da za ta yi miki "
Tiolet ɗin falon ya shiga ya wanke bakin shi da hannunshi bayan ya fito ya wuce kan kujera ya zauna ya dauki remot ya kunna TV ni kuma sai na tattara komai na maida kitchen ɗin ina gyara wajen daga can zaune Yallaɓai ya ce.
"Ki zo mu yi hira. Hiran saurayi da budurwansa."