← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 76

Sashe 11

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Rufe min ba ki, ki kuma tsaya dakyau ki saurareni. Ga uwarki nan ta zama shaida ga mijin ki nan ya zama shaida, daga yau ina mai ba ki umarni a matsayina na mahaifinki, ki ijiye duk abin da ke cikin ranki game da Asma'u ki rumgumi ƴar uwarki. Sannan ki yi zumunci da ita ki je gidanta in abin farinciki ya same ta ki taya ta murna. Sannan ki je a lokacin jaje domin ki ta ya ta jimami. Sannan in ku ka  haɗu ke za ki fara yi mata magana, ki bi ta a inda ta ke ku gaisa cikin zumunci da ƙaunar juna. Gargaɗi na ƙarshe a gareki shine ki bi umarnina ya zama wannan shi ne zama na ƙarshe da zan yi a kan wannan mganar, na ƙara faɗa miki ki yarda makaman yaƙin ki ki bi Asma'u sannan ki yi zumunci da ita, in kika saɓa ma ko ɗaya daga cikin umarnina zan yi fushi da ke fushi mai tsananin da ba ki taɓa tsammani ba Halima. Saboda haka in kina so ki rabauta har a ranar gobe ƙiyama ki yi gaggawan bin umarnin da na ba ki."

  Alhajinmu na mgana ina jin kamar zuciyata za ta faso ƙirjina ta fito tsabar baƙin ciki tuni kukana ya ɗauke. Saboda ban ga amfanin ina zauna ina kuka saboda Ma'u. Na yarda ta yi nasara a kaina kamar ko yaushe.

  Muryanta na rawa na ce"Na ji Alhaji in sha Allahu zan zama mai bin Umarnin ka."
Na faÉ—a ina sauke numfashi saboda na ji kamar numfashina na shirin kwacewa.
 
  Alhajinmu ya gyaɗa kai kafin ya ce" Kin yi kyan kai. Ki sani ko da rana ɗaya na ji labarin kin bambanta Asma'u da Rahila ki sani kin ɓata mini sannan zan daɗe ban iya kallon ki ba, zan daɗe ina miki kallon wacce ta gagare ni."

  Da sauri Gwaggo ta ce" Haka ma ba zai faru ba. Sadiya kara ba ma Alhaji haƙuri."

  Kaina na ƙasa na ƙara faɗin" Allah ya huci zuciyarka Alhaji. In sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba."
Na faɗa ina ƙokarin danne abin da ke taso mini daga ƙasan zuciyata.

  Sai ya saussauta fushin sa jin har Yusuf ya rankwafa ya na neman min afuwa har da Ma'un da mijinta sai Alhajinmu ya jinjina kai kafin ya ce" Bakomai. Na tsorata ne sabo da halin rayuwa. Ka da na faɗi na mutu na bar baraka daga zuru'a ta, na ji daɗin da kika hangi kuskuranki kika kuma yi aniyar gyarawa. Ki yi ma Asma'u sallama  ta amsa miki tare da musabaha yanzu a gabana Dubu."

  Ban yi musu ba na juya ina miƙa ma Ma'u hannu lokaci ɗaya ina yi mata sallama. Ta miƙo min hannunta ta na yi min wani irin mirmishin da ni kaɗai nasan ma'anarshi lokaci ɗaya tana amsa sallamata tare da sarƙe hannun juna. Ni ma sai na yi mata mirmishi kwatankwancin mirmishin da ta yi mini, ai ba Ma'u kaɗai ita iya bariki ba nima na iya tunda na fahimci ta na cin nasara a kaina ne ta hanyar amfanin da makirci.

"Ki yi hakuri Ma'u. Ki yafe mini sharrin sheÉ—an ne."

  Haka na faɗa ina mai gayyato mirmishi da rahama a saman fuskata, ko ta yi mamaki ba ta nuna ba sai ta waske,  kafin ta ce"Bakomai. Na ji daɗin haka Yar'uwata."

  Daga zaunen na matsa na rumgumeta, sai da ta yi wani sansarairai kafin ta rumgume bayana ta na ɗan mirmishi nima mirmishin na ke yi sannna muka saki juna bayan mun kalli juna kowaccenmu ta yi mirmishin da bai kai zuuci ba.

  Gwaggo ta yi hamdala Alhajinmu ma haka ya ɗora da cewa" Na ji daɗin haka. Allah na gode maka da korar min sheɗanin da ya shigo cikin zuru'ata. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya, ku kuma na ƙara ɗora muku nauyi ku yi musu gyara in sun yi ba dai dai ba. Sannan kuma ku gaya musu su sada zumunci a tsakaninsu saboda samun falala wajen ubangiji irin ta masu sada zumunci."

  Suka amsa ma Alhaji da In sha Allahu. Ganin har sha ɗaya ta yi na dare sai ya ce mu ta shi mu ta fi gida mun bar yara su kaɗai a gida.

  Dukkanmu a tare muka yi ma Alhajinmu da Gwaggo sallama muka fita, muna gaba ni da Ma'u su kuma mazajen namu suna bin bayan mu.

  Ni ce na fara kallon Ma'u dai dai mun fito kofar gida, ƙasa ƙass na ce"Kin iya acting kyan shi ki faɗa harkan film za ki ci kuɗi sosai"
Dariya ta yi kafin ta ce"Ko Sadiya? Ke ma ashe kin san na iya acting sosai."
Sai na gimtse fuska kafin na ce"Kin sha yin nasara a kaina Ma'u kamar baya yau ma kin ci nasara. Amman ina mai ba ki tabbacin daga yau ba za ki ƙara samun nasara a kaina ba har abada."

  Cikin reni ta ce"Kai don Allah? Da gaske?
Ban tsaya sauraranta ba na ƙarisa jikin motar Yusuf,ganin sun kariso suma ya sa na ɗaga murya ina faɗin" Sai da safe Ma'u. Alhajin Ma'u mu kwana lafiya a gaida yaran."

  Shi ya amsa min cikin sakewa, ita kuma Ma'u sai ta bige da mirmishi kafin ta ce" A gaida min da yarana Sadiya." Kai na jinjina mata a saman leɓena na amsa.
Mu muka fara yin gaba sannan su, a juctiion muka rabu mu muka É—au hanyar Lodge road, su kuma suka É—auki hanyar Rijiyar zaki in da gidan Alhaji mustapha ya ke.

  Tun da muka ɗau hanya ban yi magana ba. Hawaye na ke yi a ɓoye ina sharewa da gefen jijabina jikina. Yusuf sau ɗaya ya yi min magana na ce ya rabu da ni, sai ya maida hankalinsa kan tuƙi amman rabi da kwatan hankalinshi na kaina ganin yadda hawaye ke kwaramyamin wani na korar wani, ba wanda zai iya fahimtar yanayin baƙin cikin da na ke ciki, Ma'u ta daɗe ta na gigita duniyata ba tare da an sani ba amman komai ya zo ƙarshe. Na fahimci ni nake ba ma Ma'u daman da ta ke cin galaba a kaina to in haka ne zan dakile wannan damar zan toshe mata duk wata hanyar da za ta ƙara kuntatamin.

  Sanda muka isa gida ko jiran Yusuf ban yi ba, na yi shigewata cikin ɗaki na barsa yana leƙa ɗakin yara. Bedroom ɗin mu na shiga na faɗa kan gado na saki kukan da na ke ta riƙewa tun dazu har da fitar da sauti.

  Ina ji Yusuf ya shigo ganin ina kuka ya sa ya nufeni da sauri ya na faɗin"Haba Sadiyata, ina raye kike kuka? Ko za ki yi kuka ba za ki yi kuka a saman kafaɗata saboda na ji daɗin lallashin ki ba?

  Ya faɗa ya na mai hawa gadon ya tarairayoni jikinsa, sai na faɗa masa muka durkushe saman gadon ina wani irin gunjin kuka shi kuma yana ta ɗan tapping ɗin bayana alamun lallashi bai hana ni kuka ba sai da na yi ya isheni sannan ya ɗago fuskata ya saka hannuwansa ya na share min hawaye lokaci ɗaya yana faɗin.

  "Ya isa. Ki daina kuka ka da kanki ya fara ciwo. Shii.. is ok kin ji ko?

  Haka ya ke faɗa, cikin sanyin murya, buɗe idanuwana da suke rufe ina kallonsa  da jajayen idanuwana kafin na ce" Ka yarda da cewa Ma'u makira ce? Ka ga fa ta haɗa ni da mahaifina a gabana na kasa wani abu Yusuf, ta haɗa ni da kowa nawa.'
Sai na ƙara fashewa da kuka ina faɗin" Na rasa me na yi mata ta ke yi min haka? In saboda fasa auranta da Yaya Hamza ne ban yi nadama ba, saboda in da na bari da tuni ta haɗa mana yaƙi a gidanmu. "

  Shi dai yana ta faman ba ni, ba ki ya na cewa na yi hakuri na daina kuka tunda Alhaji ya yi min faɗa na bi umarninsa.

  Ƙura masa ido na yi kafin na ce"Haka ne zan bi umarninsa. Bakomai."
Daga haka na tashi daga saman jikinsa na sauka daga kan gadon lokaci É—aya ina cire Hijabin jikina.
Fita na yi zuwa toilet ina wani tunani a cikin raina. Ba haka zan zauna Ma'u ta cigaba da cin galaba a kaina ba, tunda har ta riga ta samu magoya baya, ni kuma daman ba ki na yasa ko ina da gaskiya na ke zama mara gaskiya gwara na yi amfani da fatar bakin nawa domin ka da Alhaji ya sake yin fushi da ni gwara na cigaba da tafiyar da Ma'u kamar yadda nima ta ke tafiyar da ni.

*Janafty*
*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY).*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z

*🅿️4*

Sanda su Ma'u suka ɗau hanyar gidansu da ke Rijiyar zaki. Zaune ta ke a bangaren mai zaman banza, kamar ba ita ce ta gama kuka wurjajan ba. Wannan karon mirmishi ne da Annuri ke fitowa daga ƙarƙashin zuciyan Ma'u kuma har ya ke iya bayyana a saman fuskarta.
Mijinta Alhaji Mustapha na tuki, sai ya waiwayo da hankalinsa zuwa kanta a tunaninsa har a lokacin ba ta bar kuka ba, amman ga mamakinsa sai ya ganta zaune tana mirmishi. Cikin mamaki ya ce"Har kin huce kenan Hajiyata?

  Kallonsa ta yi ta na ɗan mirmishi kafin ta ce"Me ye a ciki? Ba fa komai Alhajina. Farinciki na ke yi yau Sadiya ta kalleni a matsayin ƴar'uwa. Zuciyata na cike da farincikin da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba."

  Ta ƙarishe faɗa fararan haƙoranta na bayyana a waje. Ma'u Fara ce farinta mai irin ja ja ɗin nan ne, taNa da fadin fuska sannan ba ta da tsawo kuma tana da ɗan jiki, sai kibar ta yi mata kyau sosai.
Chapter 11 · 0% Book details