← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 76

Sashe 63

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na ƙosa ki sami ciki irin na Baby. Ko banza ki yi ta nema na ni kuma da sunan taimako ina shan Shagalina."

KafaÉ—ansa na kaima duka ina faÉ—in" Ba Amin ba."
Shi kuma ya na min dariya har ya na maƙale murya yana tsokanata.

"Yallaɓai na. Uhm
Uhm.."

Kunya ta kamani na saka tafukan hannuna ina rufe fuska shi kuma ya na mini dariya. In na tuna lokacin har kunyar kaina na ke ji abu kamar cin tuwo na maida shi, ba na gajiya ni dai kawai a yi kuma da an gama sai na ji a lokacin nake son abin gaskiya ba zan so na samu ciki irin na Baby ba.

Haka dai Yallaɓai ya gama wanke wanke sai na ce ya cika ladanshi ya wanke wajen ya goge mini kitchen ɗin harara ta ya yi ya ce" Shi wannan ɗin ba ni da lada ne ko ba ki gode ba ne? Da sauri na ce" Na gode. Allah ya ƙara girma mai girma Tafidan Rano."
Kaina ya shafa ya na faÉ—in" Rayuwarki ta yi albarka É—iyar ga."

Ni da shi muka saka dariya gabaɗaya. Haka nan ya haƙura ya tayani muka gyara kitchen ɗin muka goge sannan muka koma ɗaki Yallabai  dai sai da ya aikata abin da ya ce wato mu ka haɗa wanka Musbahu na ta kiran shi baƙi sun iso amman shi ya na gida yana shagali.

  Tare muka fita bayan mun shirya na rufe gida bayan na ɗaukan ma Baby dogon wando kawai suna da kayan sawa a gidan Nene domin wani lokacin in sun je sun kwana ba duka kayansu suke dawowa da shi ba, ni kuma ba na damuwa saboda irin haka suna wucewa daga makaranta ba ni da haufin kayan da za su sauya.

Yallaɓai na sauke ni a Gwammaja ko shiga bai yi ba ya wuce office ya ce mini sai ya dawo
A can na samu Hauwa Munnira ce ba ta kariso ba. Gida cike da dangin Maman Farko sannan a bangaren ƴaƴa kuma su Anty Zulaihat da Nasara sune kan gaba su da su Anty Bahijja. Anty Zuwaira kuma da ya ke yar sabga ce ba ta zo ba ƙila sai yamma. Suwaiba, Jamila  da Hindatu duk suna nan  Safiya ma haka Hafsat ce tana Abuja ba ta ƙariso ba matar Muhammad Sani an ce sai Jumma'a za su taho tare da mijin nata.
Ummu Salma ma da ke aure a Bauchi da wuri ta zo, na zo ba daÉ—ewa Jawahir ta dawo daga makaranta sun samu hutun sati biyu.

A ɗakin Nene na sauka. Tunda nan ne ɗakin Uwar mijina. Ana mganar abincin da za a yi su Anty Bahijja suka ce a yi tuwo da shinkafa sai alale sannan za a yi zoɓo duk da akwai lemuka da ruwa da aka sauke sai Nama da aka ce za a kawo naman sa da na rago za a gyara a soya domin a yi amfani da shi ga baƙi masu zuwa. Sai can bayan azahar sai ga Muninira Halima ma sai bayan la'asar ta zo. Mu surukan gidan muka gyara wake tunda an farke shi ya fara ƙwari bayan mun gama an kawo kayan miya da yawa ni dai daman yar laushi ce su Hauwa na bari da gyaran kayan miya ni dai na gyara albasa Munira na yi min tsiya gyaran albasa kaɗai ne aiki a wajen? Na ce shi ne na ga zan iya. Hauwa dai an yi dama dama cikin gyaran kayan miya ina zan iya. Ba zan yi ba ada dai kam na yi amman ban da yanzu.

Sai wajen tara na dare Yallaɓai ya zo muka koma gida washegari ma Alhamis mun koma ranar nama aka gyara aka soya sai kum an tafasa kayan miyan da aka nuƙo. A ranar baƙin Rano suka iso har da Gimbiya a ciki ban ɗauka ma za ta zo bikin ba amman sai na ji ana mganar har da cuku cukun transfer ɗinta ya kawo ta bikin.
Sai can da mangariba ne ma muka haÉ—u muka gaisa. Baby dai ta kawo mini chaculate ta ce Anty Gimbiya ta ba ta, ba tun yau ba tana son su Jidda ba kyauttukan da ba ta yi musu tun tana gida ko bayan auranta da suka je honeymoon da mijinta Paris ta siyo musu kaya masu kyau da yarari.

Can da dare ma tare na ganta da su Jidda da yaran Naja'atu. Sai ranar jumma'a Ango ya iso gida. Sai ihun ango Æ´an uwa ke yi masa yana kamewa kusan Soja da tsare gida a ranar ma Tariq ya zo shi da Faridarsa. Muhammad Sani da Nafisa tun da safe suka iso shi Jafar ma da matar shi Nauwara ma sun iso ranar duk da Kaduna za a É—aura auran amma dai ya zo gida shima.
zuwa kuma yamma komai an kammale shi.
Za a yi waina amma an ba da ne a yi sai dai Tuwon da miyan anan gidan za a yi shi kuma Alalen Anty Bahijja ta ce namu ne mu surukai mu za mu yi tsakani ga Allah ta na son ɗora mana wahala. Hauwa da Muniira na bar ma jagoracin su da ya ke a nan gidan suka kwana ni kuma gidana na koma na kwana na ce musu in sun ga ban zo da wuri ba kar su jira ni su fara aikin daman sun san halina ba da wurin zan zo ba. Jidda nan ta kwana tare da yara sa'aninta ita kuma baby ta na tare da Gimbiya Yallaɓai ke faɗa mini ta kira shi a waya ta faɗa masa ta tafi da Baby gidan Naja acan za ta kwana.

Da safe sai da na sha barcina na gajiya. Yallaɓai ma a gida ya barni na dai shirya shi cikin wata dakakkiyar shadda mai ruwan ƙasa har da babban riga hula da takalminsa bakaƙe haka ma agogon fatan dake hannun shi na fesa masa turare na bishi da Allah ya kiyaye ba da motarsa ya je ba shi. Da shi da Tariq motar Uncle Abba za su bi zuwa Kaduna.
Motar shi kuma Muttaƙƙa zai tukata zuwa Kadunan shima ɗaurin aure 11 ne na safe tun takwas suka ɗau hanya.

Ni ina gida ma sai wajen goma da rabi na fita. Rahila ta kira ni ta ce za ta zo na ce sai ta zo domin ni ban gayyaci kowa ba Yaya Balki ma da ta yi mini mganar muna da biki ba gayya na ce ni ban yi gayya ba.
Sai dai in sun zo domin Allah Gwaggo daman ta ce sai bayan biki za ta je Allah ya sanya alheri.
Ma'u daman na san za ta zo balle Uwar ɗakin nata ne yan gaba gaba. Ko da na je su Hauwa sun gama alale Munnira na ta harara ta na ce su yi haƙuri na tsaya shirya Yallaɓai ne.

"Au to me Yallaɓai? Mu ma ai muna da mazajen da za mu shirya amman ba mu je ba sai ke mai Yallaɓai a 'a yallaɓiya"
Munira ta faɗa ta na mai ƙara ɓalla minibharara.
Ina dariya na ce" To ai ban hanaku ba. Da kun tafi kuma"

Hauwa ta ce" Mu tafi Anty Bahijja ta tsire mu ko? Daman da ba ki zo ba ta ce Munirra ta É—au girman tun da ke ba ki daraja girman da Allah ya ba ki."
Ina dariya na ce" Ran Munirra ya daÉ—e. Zan zama mai yi miki biyayya."
KafaÉ—ata ta daka tana dariya. Hauwa ke faÉ—a mini Nafisa ba ta da lafiya ta na ta amai ba ta yin komai ba na ce yanzu haka ciki gare ta. Nauwara kuwa gidansu ta gudu har na zo ba ta dawo ba.
  Shashen Marigayi Hajiya Karima muka gyara muka zauna tunda sauran duk ya na cike da jama'a Shashen Nene duk mutanen Rano ne Hajiyar Tafida ma da safe ta iso. Ni daman na yi wanka na a gida Jidda na nema na bata kayan da za ta saka da takalmi da mayafi saura na Baby ne an ce ba su dawo ba. Faridan Tariq kuma suna da ƴan uwa acikin gari can ta je ta kwana bayan ta dawo itama muna tare. Sameena ma sai a ranar ta so ashe ba ta nan ta je can Niger wajen dangin mijinta duk muna tare da su anan ɗakin.

  Karfe sha ɗaya da mintina goma Nasir ya kira Munnira ya ce an ɗaura aure acan ma cikin gida an kira su Anty Bahijja sai suka fara guɗa suna ta iface ifacen murna. Sai wajen sha biyu muka sake wanka muka saka ankom mu. Ni na yi kitso amman ban yi ƙunshi ba saboda wacce ke yi min kunshi ta yi tafiya kuma wacce ta yi ma su Hauwa na ga kunshinta bai yi min ba sai ban yi ba.
Mu aka bari da wahalan raba abinci shi dai na yi saboda Mimisco ce ta kirani da kanta ta yi mini mgana shi ya sa na yi abin da ta ce.

Kafin bayan azahar kowa ka gani ya ci kwalliya sannan wasu sun ci sun sha ko na ce ana kan cin da sha ɗin. Sai a lokacin su Baby suka dawo an saka mata wani leshi mai duwatsu dogowar riga sai da na natsu na fahinci anko ne irin shi ne a jikin Gimbiya da Naja'atu da ƴayanta sun kuma saka musu ƙananun hijabi a saman kansu har takalmin su baki mai igiya iri ɗaya ne.  Baby na ta murna ta nuna mini na ce kaya sun yi kyau na kuma yi ma Gimbiyar godiya ta na mirmishi ta ce mini bakomai.
  A she ban sani ba har da Jidda sai can wajajen La'aaar na ga Jidda ta sauya atamfa ta saka kayan itama tana murna ta ce mini Anty Gimbiya ta yi mata na ce ta gode.
Chapter 63 · 0% Book details