Sashe 25
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Ina ƴar dariya na ce" Zan faɗa in dai magana ta zo akan family planning ba na sauya magana ta. Ba tsarin iyali ne ba a so ba, ba kuma cewa na yi bashi da amfani ba, ammam ki sani bayan amfaninahi akwai rashin amfaninshi, ya na da kyau a yi ɗin tun da malamai ma suna faɗin a yi amman ba zan ba ma kowacce mace shawaran ta yi tsarin iyali ba ta haihu kamar biyar ba, saboda tarin ƙalubalen da ke cikin haka, in kika haihu kamar sau biyar ko da ya ninka adadin shekarunsa sau uku ne ba za ki damu ki ji kina son ƙarin haihuwan ba, sannan wani matsawar dangin miji duk ba za ki fuskanta ba. Ko kafin a farga Ƙila Allah ya ƙara ba ki wata haihuwar shikenan amman a irin yadda na yi nawa, akwai hatsari ba zan goya miki bayan ki yi ba. Ki yi ta haihuwanki zuwa gaba sai ki yi domin ki huta amman in kin aminta da shawarata fa kenan."
 Na ƙarishe faɗa ina kallon ta, sai na ga ta yi shuru kamar ta na nazari da sauri na ce" Ban fa hana ki ba. Ki yi in kina da ra'ayi amman ki sani ki shirya karɓan abin da nima na ke karɓa duk da bana yi miki fatan haka sannan kowacce mace da yanayin yadda abin ya ke karɓanta da kuma illar da ya kan nuna a jikinta. Ba lalle abin da ya faru da ni ya faru da ke ba, watakila ke ki fuskanci ƙalubalen ta wanni fannin dabam. Amman shawaran da zan ba ki shi ne, ki bari ki ƙara haihuwa kamar sau biyu zuwa uku sai ki huta."
 Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce"Shikenan bari na bari ko zuwa gaba. Shima fa Yayan na ki cewa ya yi bashi da matsala duk lokacin da na ji ina buƙata zai yi supporting ɗina."
 Mirmishi na yi kafin na ce"To wai daman su Maza ina ruwan su? Zai ba ki goyon baya mana. In matsala ta faru yana da zaɓi zai iya ƙara aure ke kuma fa? Kin cutu har abada in kuma danginsa sun matsa ya ce ai tsarin iyali kika yi kamar yadda Yallaɓai ya yi mini a wajen dangin sa. Da suka damu da rashin haihuwata bayan Jidda shi ya faɗa ma Anty Maimuna wai tsarin iyali na yi ya zo ya ba ni matsala ba shikenan ya gogamin baƙin fenti ba, da sun tashi gwaɓamin mgana sai su ce ai ba Allah ne ya tsaida min haihuwan ba ni na tsaida ma kaina. "
 Khaleesat ta yi dariya kafin ta ce" Ke da Yallaɓan na ki kuma? Baki na tura kafin na ce" Yallaɓan fa nawa. Wani lokacin ya cika abin haushi ne."
Dariya ta yi mini nima ina tayata. Nan muka lalace muna ta tattaunawa. Sai sallar la'asar muka tashi daga falo ita ta wuce É—akinta ni kuma na nufi in da na sauka.
Bayan na idar da sallah na kira Saude mu ka gaisa.
"Saude ya gidan ne? Fata komai lafiya ko?
Sai ta amsa mini da lafiya lau kafin ta ce"Anty yaushe za ki dawo? Kai tsaye na ce" Gobe in sha Allahu."
Fatan dawowa lafiya ta yi mini ni kuma na ce zan ƙara kiranta in su Jidda sun dawo daga makaranta.
Daga nan sai na kunna Data saƙonni na ta shigowa. Maganar Yaya Auwal na fara gani na yi saurin buɗewa.
"Zan shigo wannan weekend É—in fa."
 Cikin jin daɗi na rubuta masa Allah ya kawo shi lafiya.
"Kai da Laila da yara ne?
Yana online amman sanin halin shi da sai ka yi saƙo sai ya ga dama zai buɗe sai na fita, ina duba sauran saƙonnin sunan MA'U da na gani ta yi mini magana ya sa na yi tsaki na wuce ta, na ga an yi mgana a group ɗin gidanmu ban shiga ba domin ban ga an yi tagging ɗina ba kenan mganar ba ta shafe ni ba. Amina ce ta yi min mgana da cewa ta kira waya ta ba ta samu ba na ce mata network ne.
 Sai na fita na je bangaren Status ina ta dubawa. Rahilarmu na ga ta saka status har ina rawan jikin dubawa. Ya Muntari na gani ya na riƙe da jaririyar(Zainab Nihad) ba hoton ne ya ba ni dariya ba, sai rubutun da ta yi a ƙasa.
"Hubby na. Abu Zainab I love u."
 Dariyan da na saka har a sarari, na danna Viocenot ina ƙyaƙyata ma ta dariya kafin na ce"Rahila ma su Hubby, wai Ya Muntarin ne kuma ya koma Hubby? Daga Yaya Muktar ya koma Hubby."
Bayan nan na sakin mata VN ɗin. Sannan na riƙa jere mata sticker na shaƙiyanci.
A yammacin nan dai status É—in Rahila ne ya nishaÉ—antar da ni. Ba ta online, abin mamaki shima Ya Muntarin na ga ya yi sreenshoot ya saka a jikin sunanta My Baby.
Haka na ke ta dariya shima sai da na yi tagging É—in shi.
"Su Ya Muntari Hubby manyan ƙasa."
Ya na online ya turo mini Emojin dariya kafin ya ce"Ke ko? Sadiya dai ta raina Yayan nan na ta ko?
Emojin dariya na tura masa sai na jin kunya sannan na ce"Wace Sadiya ta raina Ya Muntari. Allah ya bar Ƙauna Hubbyn Rahila ta."
 Ni kaɗai a ɗaki ina ta dariya ina tuna wani zamani a can baya har gobe ban manta lokacin da Ya Muntari ya zo gidanmu ba. Mama Allah ya jiƙan rai ta ce" Ya sunan ka ɗan samari."
"Muntari. Muntari sunana Hajiya."
Sai na ji wata dariya ta ƙara kamani har ina buga hannuna a saman cinyata, lokacin da Rahila suka fara soyayya da Ya Muntari ba wanda ya sani, wata rana kawai ya shigo gidan kowa na gaishe shi, da kuma sunan da muke kiran shi kenan Ya Muntari.
"Barka da dawowa Ya Muktar."
"Yauwa Sannu Rahilatu."
Sake baki na yi ganin yadda Rahila ta wani sunne kai tana dariya, shi ma ya na mata wani kallo. Ba zan manta ranar ba ina bakin famfo ina wanke wanke ita kuma tana bakin madafi ita da Ma'u suna gyaran wake.
 Ga mamakin sunan da ta kira shi. Ga wani kallo da suke ma juna. Tun daga ranar fa Rahila, ta daina kiran shi Ya Muntari sai dai Ya Muktar har faɗa mun sha yi da ita, in na ce Ya Muntari.
"Kai Sadiya. Ba fa Muntari sunan shi ba. Ba ki iya cewa Ya Muktar, muktar ne fa sunan kuke ɓata masa da sunan tsoffi wai Muntari."
 In ta ce haka sai na balla mata harara sannan na ce"Ke kika san Muktar. To da bakin sa ma ya ce sunan shi Muntari ko Gwaggo?
 A lokacin Rahila ta riƙa tura baki kenan ta na ƙunƙuni. Ta yi ƙokarin sauya sunan Muntari zuwa Muktar amman bai sauyu daga bakina ba, da gayya ma ma ke faɗa Ma'u dai da ya ke makira ce har wani ƙalƙala take yi wajen faɗin sunan.
"Ya MUKTARR."
Makircin Ma'u fa haifaffan ne, ta tsotsa a nono ne shi ya sa in ta buga acting ke yi mata kyau.
 Haka Khaleesat ta zo ta same ni ina ta dariya. Domin mun yi dogon charting da Ya Muntari yana tamnbaya ta laifin me suka yi tun ranar suna Rahila ta ce ban dawo ba, na fa san Rahila ta faɗa masa dalili zai yi min wayau su na maza ne ni ko na ce ya tambayi matarsa ta san dalili.
 "Ke da waye kike ta dariya haka? Ko Yallaɓan ne?
 Ina mirmishi na ce"Wani Yallaɓan? Wai wannan Hubby na Rahila ne."
Ina faÉ—a ina dariya Khaleesat ta kwashe da dariya kafin ta ce"Au kema kin gani? Nima yanzu na gani ina ta dariya a raina na ce Rahila manya ta Muntarin ta."
 Miƙewa na yi daga kishigiɗen da na ke ina faɗin" Ta fa kashe wannan sunan. Muktar ko Hubby."
Na faÉ—a ina kwaikwayon bakinta ni da Khaleesat har muna tafawa saboda dariya, Ita kuma faÉ—i ta ke yi" Ni ya na burgeni ba shi da damuwa. Ga barkwanci kuma ya na son Rahilatun nan ta bakin shi ba."
 Jinjina kai na yi kafin na ce"Ai Muntari na ƙaunar Rahilatu."
"Sadiya ba ki da dama, na shigar ma Rahila. A bar yankan mana Hubby ahto.'"
 Ni dai ina ta dariya. Sai kuma mu ka cigaba da hiran Rahila da Ya Muntari muna cin dariya. Kukan Amna daga bedroom ɗinsu ya sa Khaleesat ta bar ɗakin da sauri ta fita ba daɗewa mijinta ya dawo sai ban ƙara ganinta ba sai dare wajen dinner.
"Sadiya Ya ya? Fatan dai ba matsala ko?
Yaya Hamza ke tambayata. Bayan mun haÉ—u a Dinining muna cin abinci.
"Ba wata matsala. Yanzu dai ta yi min transfer zuwa Aminu kano ta haÉ—a ni da wata consultan."
Da kai ya amsa kafin ya ce" Tunani mai kyau.'" Daga nan
bai sake mgana ba. Shi ya fara tashi kafin ya goge bakin shi da Tissue sannan ya kalleni ya na faÉ—in" Yaushe za ki wuce? Ina kallonsa na ce" Gobe in sha Allahu"
"Ba ki bari weekend mu shiga kanon tare"
Kai na girgiza kafin na ce"Ya Hamza. Yara su kaÉ—ai a gida Yallabai kuma ba ya zama in ya fita tun safe sai dare."
 Ya na wucewa falo ya ce"Wasu yara? Yallaɓan dai amman Jidda yarinya ce? Shekaranta nawa?
"13 in to 14 fa Ya Hamza. "
"Ehem.."
 Ya ce kawai alamun maganarsa ta farko dai itace Yallaɓai dai ina dariya khaeesat na faɗin" E, mana Yallaɓai dai take yi ma kewa kar ta ƙara kwana ta barshi shi kaɗai."
 Mirmishi na yi kafin na rage murya ina faɗin"Da shi ɗin ma, mata ba ta yi kewar mijinta ba? Miji mai kama da dubu irin Yallaɓai na."
Harara ta zuba min kafin ta ce"Mu kuma na mu mazajen masu kama da bolar sharar ki ko?
Ina dariya na É—aga hannu ina faÉ—in" Ba ruwana.".