Sashe 21
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mirmishi na yi ban yi magana ba. Shi ya ta shi ya fara yin wanka sannan ya tasheni nima na yi wankan Sannan muka dawo muka sake kwanciya sai asuba muka tashi, Saboda ina da tafiya a gaba na da wuri na tashi.
 Lahadi ne yara suna gida, shima Yusuf din ya ce mini sai azahar zai tafi Rano. Ni na yi mana Breakfast muka karya gabaɗaya sannan na yi wanka na shirya Yallaɓai ya ce na tafi da wuri baya son na yi yammah a hanya..
Kaya kala biyu na haÉ—a a karamar akwatina Baby na ganin na haÉ—a kaya ta fara rigiman sai ta je, Babanta ne ya zauna ya na lallashinta.
 Na kira wayar Saude ban samu ba sai na kira na Balaraba mamanta, na faɗa mata zan yi tafiya Saude ta zo da wuri ta gyara gida ta yi ma yara abinci sannan in ba damuwa ta kwana da su kafin na dawo duk da nasan Yallabai zai kula da su ga jidda amman gwara dai na barsu tare da Sauden tun da shi sai dare yake dawowa Balaraba ta yi min fatan dawowa lafiya tace Saude ta je islamiya in ta dawo za ta zo in sha Allahu.
 Yallaɓai ya saka mini duka Report ɗina na asibitin da na ta zuwa a baya a cikin ƙaramar jakata ya turamin 30k a acct ɗina lokacin muna hanya shi da yara za su kaini tasha misalin sha ɗaya na safe.
"Na ga 30k Yallaɓaina. Ina godiya."
 Duk na san kuɗin sun yi kaɗan amman ban iya masa ƙorafi ba, ba halina ba ne.
 Ya na tuki su Jidda na bayan mota ya waiwaya yana kallona ina sanye da hijabi, na saka abaya da mayafi ya ce na cire na saka hijabi sai na sauya kaya zuwa atamfa doguwar riga.
"Ki yi hakuri Sadiya ba kuÉ—i a hannuna in akwai kuÉ—i a hannunki ki cika duk abin da kika kashe ki rubuta, in an biya mu zan biya ki duka kudaÉ—enki in sha Allahu."
"To."
 Kawai na ce masa, domin na saba jin in aka biyamu zan biyaki duka kuɗinki kuma an sha biyan shi ɗin amman sai ya manta da ni in na yi mgana sai ya ce kuɗin sun ƙare na yi hakuri a gaba zai biyani.
Ba su bar tasha ba sai da motar mu ta tashi, sit ɗin mutum biyu Yallaɓai ya biya min kada na takura, sannan ya biya kuɗin mota muka rumgume juna ni da shi, yaran ma haka suna ɗaga min hannu ina ɗaga musu motar mu ta bar tashan, sai bayam mun tashi ina ga shima ya tuka motar zuwa gida.
 Muna hanya ma na sake kiran Anty Khaleesat, tunda da safe ta kirani ta ce yaushe zan ta so, na ce mata zuwa sha ɗaya na rana lokacin da na ce mata mun taso Yaya Hamza na gida har ya karɓi wayar ya na faɗin" Na ɗauka Yallaɓan na ki ne zai kawo ki?
 Ina dariya na ce"Haka ya so, amman ya fara wani aiki kuma ka san ana bukatarsa sai na ce kawai ya yi zamansa ni na je na dawo"
 Sai ya ce ai shikenan Allah ya kawo mu lafiiya. Na amsa musu da Amin sannan muka yi sallama.
Â
 Kafin mu sauka Zariya ban san sau nawa Yallaɓai ya kirani ba, na sauka ma a kwangila Zariya ya sake kirana na ce yanzu zan samu Adaidaita zuwa anguwan da Gidan Yaya Hamza ya ke. Gra kusa da bankin Gt Bank in da yake aiki.
****
 Ina zaune a falon gidan Yaya Hamza rashe rashe ina cin abinci shinkafa da miyar Naman rago da Anty Khalesat ta yi min, ita ta na zaune a saman kujera ta ba ma Amna nono muna hira sai ga kiran wayata da ke saman kujera a cikin jakata tun da na iso na watsar da su saman kujera ban bi ta kai ba.
Na iske Yaya Hamza a gida amman ban daÉ—e da zuwa ba ya fita ya ce wani abokin aikinsa mahaifinshi ya rasu za su je Ta'aziyya.
Khaleesat ta fi kusa da jakar ita ta matsa ta É—auko jakar ta, bude ta É—auko wayar.
"Waye?
" Wata wai Sameena Tafida Rano."
Mirmishi na saki kafin na ce Allah Sarki da hannuna na hagu na miƙa hannu na karɓi wayar.
"Wace ce? Ƙanwar Yallaɓai ce?
Sai na girgiza mata kai, kafin na ce"E, a'a. ÆŠiyar marigayi Tafidan Rano ce."
 Ɗaga kiran na yi da fara'arta kamar yadda muka saba mace ƙwara ɗaya da muke mutumci sosai daga gidan Marigayi Alhaji Yusuf Tafidan rano, duk cikin su da ita kaɗai na saba kuma na ke zumunci ko Gimbiya da muke da lambar juna ba ma waya iyaka ta dai in mun haɗu a gidan Nene ko Rano gaisuwan fatar baki ce.
"Matar Baba."
Haka ta faɗa daga bangarenta ina dariya na amsa mata mu ka gaisa da tambayan yara. Da ta ce min ta zo sunan Halima na gobe ba ta ganni ba an ce ina Zaria. Daman na san za ta zo tunda Halimar ƙawar ta ce.
 "E. wallahi na zo gidan Yayana zan kwana. Gobe ina da ganin likita a asibitin Shika in sha Allahu."
 "Lafiya kuwa? Ko ba lafiya ne?
Da sauri na ce"Lafiya ƙalau zan dai ga likita ne kawai. Kin shigo garin kenan?
Sai ta amsa min ina ma jin hayaniya, daga karshe ta ce yaushe zan dawo na ce mata gobe in sha Allahu sai ta ce za mu haÉ—u ita sai jibi za ta koma Rano.
Sai da muka yi sallama na ijiye wayar a gefena.
 "Ban ga ne wata Sameena ba. "
"Da wuya ki santa. Rahila ce ta san ta, ɗiyar wannan aminin mahaifin su Yallaɓai? Wanda ya rike tafidan rano lokacin ya na raye, amman bayan ya rasu an ɗora ƙaninsa, ita wannan da muka yi wayar autan su ce Sameena, kin ga kamar ƙanwa take a wajen su Yallaɓai."
"Oh na gane su, lokacin haihuwan Baby na ga duk sun zo na ji ana cewa iyalan gidan marigayi Tafida ne."
Ina gyaɗa kai na ce" Su fa, ai Yallaɓai na ya zauna gidan sosai tun yana matashi, kuma uwargidan Marigayi ɗin Hajiyar Tafida ƙawar Nene ce tare suka yi yarinta ƙawaye ne sosai. Yadda Yallabai ya faɗa min a bikin Nene marigayi Tafida ya ga Hajiyar ya ce yana so har ta kai su ga aure suka tara zuru'a. "
"Allah Sarki.."
In ji Khaleesat, ni kuma ina cin abinci na ce" To ita wannan da muka yi waya ɗiyar Amaryansa ce, Hajiya Kaltume."
 Ita dai Khaleesat da ba wani sanin su ta yi ba sai dai ta bi ni da Allah Sarki kawai. Sai da na ci na koshi sannan na shiga ɗakin da aka sauke ni na yi alwala na yi sallar azahar da la'asar sannan na kira Yallaɓai bai ɗauka ba sai na kira Saude ta ba ni su Jidda muka yi mgana.
 Daga nan sai na kira Dr Fadil, shima bai ɗauka ba sai na ƙyaleshi, ina duba wayar sai na ga ashe ma Hauwa ta kirani sai na kirata daga baya.
 Daman na san za ta ce ba ta ganni gidan Halima ba na ce mata ina Zariya ba da ni za a ci wannan sunan ba, sai ta yi min fatan dacewa muna ma waya Dr Fadil na kirana sai na katse nata na ɗaiuki nashi.
Mun gaisa ko da na faɗa masa sunana sai ya ce ai ya gane ni Abba ya tura masa lambata. Na faɗa maaa na shigo Zariya ina gidan Yayana sai ya ce gobe da safe ƙarfe goma zai shigo asibitin na tabbatar da na shigo a wannan lokacin sai na kira shi, da haka muka yi sallama.
 Ba gaji saboda zaman mota, gado na haye ina jin kamar ba zan iya tashi ba. Khaleesat ta leƙo ni ta ganni kwance sai ta ce na huta kawai itama tana ciki tana gyara kaya ne.
 Gidan Yaya Hamza flat ne daidai na zaman mutum ɗaya haya suke yi amman yana gina nashi. Yayansu biyu duka mata, tana goyon na biyun mai sunan Mama Ruƙayya Amna(Tasleem) ta na gidansu Jawahir ɗin ta je hutu.
 Har na fara barci na ji kiran wayata na ɗauka cikin muryan gajiya, da barci.
Jin na isa lafiya ya sa Yallaɓai ya ce na huta sai mun yi magana anjuma.
 Ban tashi ba sai gabda mangariba, na yi wanka na saka riga da wando, ni daman kaya irin atamfa damuna suke yi, plazo na saka da T.shirt.
 Daman na ɗauro alwala ina shiryawa na tada sallar mangariba, tun ina sallar ake kiran wayata sai da na sallame na ga wai Ma'u ne.
Tsaki na ja na ƙi ɗauka kira biyu sannan ta ƙyaleni, amman da na kunna data sai na ga saƙon ta.
"Ban gan ki a gidan Halima ba. Ina fatan lafiya ko?
Daƙyar na iya ce mata lafiya lau, daga haka ban ƙara ba sanin da na yi gulma ce ai na san ta ji labarin na je Zariya, tunda Yallaɓai ya ce ya faɗa ma Anty Bahijja ba zan je sunan Halima ba zan je Zariya ganin likita kuma ina da tabbacin Ma'u ta ji labari.
Ni da kaina na kira Rahila a waya muka sha hira na ce mata ga ni a gidan Yaya Hamza.
" Kai Sadiya, ko ki jirani mu zo tare in na yi arba'in"
Kamar tana ganina na harareta kafin na ce"A'a sai dai na tsaya ki yi hamsin"
Sai ta kwashe da dariya, zolayata take yi tasan ai abin da ya kawo ni.
"In sha Allahu Sadiya za ki ƙara haihuwa da ikon Allah."
 Kamar zan yi kuka na ce"To Amin. Amman kin ji daɗin ki Rahila. Da ba ki yi planning ba, ba ki haɗu da side effect ba gashi nan kina ta haihuwanki yayanki huɗu bayan ma kin yi ɓari sau ɗaya."