← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 76

Sashe 70

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar litini ya kama ukun salla tun asuba na tashi ni da Marwa waina za mu yi saboda zan kai Gwammaja zan kuma aika da shi Ɗorayi da Gandun albasa. Saude na kira waya na ce ta zo da safe ta taya mu aiki. Saboda ina da mataya ko kafin sha biyu na rana mun gama toya waina duka miya daman tun safe na haɗa ta. Yallaɓai ya siyo mana manshanu daman na zuba a cikin miyan ga kayan ciki ga naman rago sannan ga ƙashi. Miya sai tashin kamshi ta ke yi Yallaɓai na sauri zai fita Rano zai je za su haɗu da Uncle Abba da Tariq da suka zo sallah sai na zuba masa ya ci ya na santi sannan ya tafi amma sai da ya ba ni goron salla ta na 10k sabbin yan 200 goron salla da kuɗin kwalliya domin na yi masa ado kuma ya burgeshi.
  
  Muna gamawa su Marwa suka gyara gidan saboda rage kaya Yallaɓai na ce ya yi mini gaba da su Jidda zuwa Gwammaja da wainar su ni daga baya sai mu taho da Marwa. Saboda daman ranar a can muke yini sai washegari yinin salla na huɗu kowacce sai ta je gidan su. Saude ma kuɗin a daidaita na bata bayan na diɓar mata na su wainar sai kuma na bata na gidanmu a babban kula na waina sai ledan da na saka Nama da kayan fulawa na ce ta kai ma Gwaggo in ji ni. Ni kuma sai da na sake wanka na sauya kaya na saka leshin da Yallaɓai ya yi mini na yi amfani da mayafi da jaka da takalmi kalan adon leshin jikina na saka ɗan kunnayena masu kyau da yarari na fito na yi ras da ni na san duk in da na shiga ba wanda zai raina ni.
Da muka fito daga gida ba Gwammaja muka fara zuwa kai tsaye ba sai da na biya Gandun Albasa gidan su Mama na kai musu abincin salla da Naman salla sai kayan fulawan da na yi ban jima sosai a can ba duk na ga su Inna Mariya da sauran yaran su muka gaisa na yi musu rabon barka da sallah daman duk sallah ina kai musu abinci kuma ina zuwa tunda ni kaɗai ce mace a kano Amina ta yi nisa sai in wani abu ya faru ta zo. Ni ɗin ce na ke ƙoƙarin sada zumunci suma kuma suna da kirki duk abin da zai faru damu suna zuwa sannan Ya Auwal ma in ya zo garin ya kan je ya gaishe su kuma taimako dai dai gwargwardo ya na yi musu abin da bai gagara ba.

  A can Gandun albasa muka yi azahar sannan muka wuce Gwammaja. A can na iske su Hauwa da Munnira gida cike da ƴa'ƴa da jikoki. Domin kaf ɗin su yaran gidan sun zo sai dai waɗanda ke nesa irin su Jafar da Muhammad sani Yaya Usman daman sai yaran shi kawai ne suka zo. Su Anty Bahijja gabaɗaya suna nan da gayyarsu ban ga Gimbiya ba sai na ji Anty Maimuna na faɗin ta tafi Rano ɗazu da safe. Naja'atu ta zo amma ina gidan ta yi shirin tafiya gidan iyayen mijinta can za ta ƙarishe yininta Halima ma ta zo da yaranta ta yi kiɓa ita da jajariyarta mai kyau da ita har na ɗauke ta.
Lokacin da na zo Nene ta kwanta sai da ta tashi muka shiga muka gaisa na kai mata Nama da kayan fulawan da na zo da shi ta yi ta saka mini albarka.

"Sadiya Tafida ya kawo mana waina. Sannu da aiki Allah ya saka da alheri."

Na amsa da Amin haka Nene ta ke komai sai ta yi maka godiya. Daman su Hajiya iya duk na shiga mun gaisa na kai musu na su Naman salla, tunda haka na ke yi duk shekara sai dai Yallaɓai in ya je ya ji suna masa godiya nima haka suka yi ta min godiyar waina, Suwaiba har tana min tsiyan shi ya sa Yaya Tafida ya fara ijiye tumbi ashe daɗin girki na ne ina ta mata dariya. Maman farko ta ce ai ta diɓa ta boye za ta ɗumama ta ci da daddare wainar ta yi mata daɗi. Da ya ke shekara biyu kenan ban yi waina ba wancan shekaran tuwo na yi musu da miyar agushi wannan ne na ce bari na yi waina saboda a sauya baki.

Kowa ya ganni tare da Marwa sai ya ce Sadiya ina kika samo yar budurwa mai hankali da kunya haka? Saboda da yara sun ɓata ɗakin Nene za ta ɗauko abun shara ta share. Ga shi ta na son yara goye take ma da ɗiyar wajen Halima har Nene sai da ta yi mgana na ce ɗiyar Yayata ce Marwa na tuna ma Nene ai ta na zuwa gidana hutu kuma na sha zuwa da ita gidan nan.

  Nene cikin mamaki ta ce" Allah Sarki girman ɗan mutu ba wuya. Ita ce ta girma haka? Ina dariya na ce ma Nene wallahi ita ce. Nene ta yi ta saka albarka Anty Bahijja ta saka mana baki da tambayan a ina take karatu na ce a tsafe makarantar koyin aikin jinya sai ta taɓe baki ba ta yi mgana ba ni kuma ban damu ba sanin halinta akwai son ta ji ƙwaf kuma in an faɗa mata ta nuna kamar ba ta so ta ji ba.

Ganin ɗakunan su Nene cike da ƴayansu zuwa jikokinsu sai mu surukan gidan muka tsame kan mu zuwa ƙasa shashen su Jawahir ba ta nan ma tun safe an ce ta tafi can gidan kakaninta na bangaren uwa ita da Adnan. Da ni da Hauwa da Muniira muka zauna acan muna ta hira muna shewa. Muna ƙara ma junan mu sani kan abin da bamu sani ba. Muna mgana kan kayan gyara ne Munnira ke faɗin rabon ta da wani gyara tun haihuwan Mufeedan ta.

Cikin mamaki na kalleta kafin na ce" Ke kam Munnira me ya sa me ki? Mufeeda yanzu ai ta shekara uku ko Hauwa?
Na faɗa ina kallon Hauwa wacce kafin ma ta bani amsa Muniiran ta karɓe da faɗin" Shekaranta uku da wata biyu."
Jinjuna kai na yi kafin na ce" Ki ce waje duk ya yi tsatsa. Gaskiya ba ki kyauta ma Nasir ba."
Na faɗa ina hararanta ita kuma tana dariya kafin ta ce" Ke ni fa gani na ke yi duk ba sa wani yi asara ne. Kuma ni in dai ba shi zai ba da kuɗin a siya ba sai na ke ƙyashin fidda kuɗina na siya wallahi."

  Mamakin Munnira ya kamani daman har yanzu akwai mata masu tunani irin na Munnira? Ko dai ta yi ma kalmar gyaran mummunan fahimta kamar yadda wasu matan suka yi ma kalmar. Ban samu zarafin mgana ba Hauwa ta karɓe mganar da cewa" Haba Munnira ke da kan ki ma? Mata ai yanzu sun waye kowa ta san abin da za ta sha ya gyara ta ba wai kuma wanda zai zama cuta gare ta ba. Kuma kin manta hausawa na cewa in kana da kyau sai ka ƙara da wanka? Kina da yaƙinin tun gyaran da kika yi da haihuwan Mufeeda ya na nan a jikin ki? Haba ai yakamata dai ko yaya ne ki ɗan ƙara gyarawa ko dai baki sha komai ba yan kayan marmarin nan da za su ƙara miki cika da Ni'ima."

  Daga ni har Munnira baki muka saki muna kallon Hauwa. Sai da ta gama bayaninta ta ga irin kallon da muke yi mata sai ta ji kunya ta kauda kai tana faɗin" Me ya faru kuke kallona? Ko ba gaskiya na faɗa ba."
Ina ɓoye mirmishina na ce" Kin faɗi gaskiya Hauwa uwargida a gidan Mutaƙƙa shi ya sa har gobe bai kallon kowa sai ke ashe sirrin da kika riƙe kenan? To mu ma a ɗan gaya mana sirrin mana ko Muni?
Na faÉ—a ina kallon Munnira da ta kwashe da dariya har ta na bani hannu muna tafawa cikin dariya ta ce" Shegiya Hauwa ta zama yar gari. Maza gaya mana sirrin."

Hauwa na dariya ta ce" Shawarwarin ku ne fa, sannan daga Rano akan É—an aiko mini da gumba da sauran abin da ba za a rasa ba. Sai wacce Sadiya ta haÉ—a ni da ita na kan É—an siya mganin infection sai kaza in na samu kuÉ—i kuma Alhamdulillah ina ta ganin canji."

  "Allah Hauwan Mutaƙƙa ?

Na faÉ—a ina kallonta sai kawai ta É—aga mini kai. Tare muka saka dariya Munnira har ta na É—aga kafa saboda dariya kafin ta ce" Ke Sadiya yaushe Hauwa ta yi baki haka? Kuma abin É—anwaken zagaye ne? Hauwa kaÉ—ai kike so ta gyara ban da ni ko?
Ina ɗaga hannuna sama na ce" A'ah ita ta min mgana ta ce tana so saboda ranar tana gidana aka aiko min da saƙon. Sai ta ce min tana so sai na haɗa su kema in kina so ai ta kwana gidan sauƙi waya kawai za a yi mata."
Munnira sai ta gyara zama kafin ta ce" To wai kuma yana yi sosai?
Na kalleta ban yi mgana ba Hauwa ce ta ba ta amsa da cewa" To ai ke tunda kin riga kin saka wasi wasi ko kin siya ba zai yi miki aiki ba."

"Ko?

Haka ta ce tana kallon mu ni ko sai na gyara zama ina faÉ—in" Gaskiyan Hauwa. Kuma son kuÉ—i ne ba zai barki ki yi gyaran ba karki kashe kuÉ—i ko? Zauna Nasir ya samu wasu Æ´an kudaÉ—e ya nemi chanji lokacin za ki yi bayani ne."
Tana dariya ta ce" Haba. Ai ya yi ƙanƙanta da Mata biyu. Yallaɓai dai ke kan hanya daman ana ta cewa tunda Yaya Usman ya buɗe hanya Yallaɓan ki ne zai biyo baya."
Chapter 70 · 0% Book details