← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 76

Sashe 8

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Kai tsaye ya ce"E  hakan ma ya yi. Allah ya sa a dace."
Na amsa masa da Amin.
Mun shiga anguwan É—orayi kawu Abba ya sake kira ya ce sun yi mgana da abokin nashi Dr Fadil shi likita ne a bangaren zuciya amman ya ce ya yi ma wata Dr Nayami mgana musulma ce amman ba bahaushiya ba ce, ya É—an yi mata brief na matsalata ta ce zuwa sati mai zuwa za ta iya bani appiotment in har ya tabbata zai kira Kawun ya sanar dashi.

  Jin haka ya sa sai na ji daɗi kamar na je ta shaida mini zan iya sake samun wani cikin haka na riƙa ji.  Daidai lokacin Yallaɓai na gyara parking a kofar gidanmu da ke anguwan Ɗorayi.

*TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU  #1k NE KACAL,  AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
09069067488.
08032773332.

*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*

*Janafty*
*03/10/2024*
*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z

*🅿️03*

Gidanmu na nan a farko layin shiga anguwar ÆŠorayi. Yanayin fasalin gidan babba ne sannan tun daga waje za ka fahimci tsarin gidan na tsohon É—an boko ne.
Domin Alhajinmu  kafin ya yi Ritire(Ritaya) sai da ya riƙe mukamin babban darakta na kamfanin wuta na jihar kano(KEDCO). Bayan kasancewarsa manomi. Kuma gidanmu na da ga cikin rukunun gidajen da suka daɗe a anguwar tun da sama da shekara ashirin duk da ko mu kanmu muna da wayau lokacin da muka dawo gidan tun a wancan lokacin zamani na kwance. Sai dai yanzu lokaci bayan lokaci yana samun ƴan gyare gyare da kwaskwarima daga su Yaya Hamza.

  Ni na fara fitowa daga Motar. Yallaɓai na kuma an kira wayarsa ya tsaya a mota ya na mgana.
Kofar gidan namu tar da hasken wuta gabaɗaya ma anguwa akwai hasken ƙwakwayen da suke kofar gidajen wasu mutane dake cikin rukunin anguwan ta Ɗorayi.

Gidanmu na ke kallo ina tuna wasu shuɗaɗɗun al'amura da suka faru damu a cikin gidan masu daɗi da akasin su. Yallaɓai ne ya katse min tunani da cewa" Kin ga ko na manta ɗazu musabahu ya zo offishina ya bani saƙo ya ce in ji Yaya Muntari mijin Rahila."

  Sai a lokacin na ɗago ina kallonsa ya fito daga mota ya na nuna min kullin abu a baƙar leda, yadda ya ga na taɓe baki ya sa ya san tabban nasan da saƙon.

"Bar shi a motan kawai."

  Bai yi musu ba sai ya koma cikin motar, ina hangensa daga waje ya buɗe akwatin motar ya jefa sannan ya fito yana ƙoƙarin rufe motar hasken wata mota da ke tunkaromu ta kashe mana ido daga ni har shi sai da muka saka hannuwammu muka kare fuskokin mu dashi.

"Kai. Waye wannan da ba zai rage filita tunda ya shigo cikin anguwa ba."

  Na kasa magana ne saboda mamakin ganin motar ba wucewa ta yi ba, kusa damu itama ta gyara parking, tun kafin ma na ciki su fito na shaida su waye tun daga cikin motar akwai hasken fitila.

"Ma'u ce.."

Haka na faÉ—a a cikin raina dai dai san da ta buÉ—e murfin mota ta fito shima mijinta ya fito daga can bangaren direba.

"Alhaji Mustapha ne, da Ma'u ashe."

  Yusuf ya faɗa ya na sakin mirmishi, na kalle shi wani abu ya yi mini tsaye a zuciyata. Lalle Alhajinmu wato zaman yau bayan ni da Ma'u har da gayyar mazajen mu kenan?

  Kara haɗe rai na yi, ganin Ma'u na nufoni shi kuma Yusuf ya nufi Alhaji Mustaphan shi adole ya ga ɗan'uwan mijin yayarsa. Ƙaramin tsaki na ja dai dai lokacin da Ma'u ta ƙariso kusa da ni ta na faɗin"Sadiya kema Alhajinmu ya kira ku ne ke da Injiniya?

  Ta faɗa lokaci ɗaya ta na ɗora hannunta saman kafaɗata. Sai na ji kamar ta ɗora min cuta da sauri na kauce ina yi mata wani irin kallon ke ki kiyayeni. Ita kuma ta na bi na da wannan munafukin mirmishin nata na yaudara.

  Ƙoƙarin sake matsowa kusa da ni take tana yi min mirmishinta da ba alheri a cikin sa. Tsaki na ja mai karfi na juyawa na fara tafiya zuwa ƙofar da za ta sada ni da cikin gidanmu na ji muryan Ma'u da ɗan karfi ta na faɗin"Haba Sadiya. Ke shike nan abu ba ya wucewa a wajen ki? Na yi ta ba ki haƙuri fa?

  Sai da na kai kofar gidan sai na juya ina kallonta sai na ga har su Yusuf ma sun dawo da hankalunsu kan mu, dariyan gefen ba ki na yi. Ni ai sai dai na rubuta littafi guda akan maƙircin Ma'u daman ta yi ne domin hankulansu ya dawo kan mu, shigewata cikin gida na yi ina ji Yusuf na kiran sunana na yi masa banza na yi shigewata na bar su nan ƙofar gida.
 
  Dogon korido ne mai ɗauke da ɗakuna uku na waje, biyu suna rufe ne sai guda ɗaya ne a buɗe. A raina na ce kila Datti ya zo gida ko kuma an yi baƙin maza daga Yashe ko Yan tumaki.
Ban gama mamaki ba sai ga Datti ya fito daga cikin gida sai muka ci karo da juna.

"Datti.."

Na kira sunan shi, sai  ya kalleni domin fitowarsa daman hankalinsa na kan wayar hannunsa. Daga shi sai baƙin wando da farar singileti.

"Yaya Sadiya? A daran nan?

Ya faɗa yana kallona, jiyo muryoyinsu Yusuf suna ƙokarin shigowa ya sa na raɓa ta gefensa na wuce, ina jin sa ya na tambaya ta.

"Ke kaɗai kika zo? Ina Yallaɓan da su Jidda?

  Ko juyowa ban yi na faɗa tsakar gidanmu da sallama. Gwaggo na Madafi na kuma nasan shayi ta ke dafama Alhajinmu da tun tasowarmu nasan ba ya iya barci sai ya sha wannan ruwan zafi. Ita ta amsa min sallamata tana kuma leƙowa muka ci karo da juna tsakar gidan tar yake da hasken  gulop.

  "Maraba da Hajiya Dubu."
 
  Sai na sa ki mirmishi ina faɗin"Kai Gwaggo ni dai wannan tsohuwar ta mutu ba ta bar mini gadon komai ba sai na sunan ta."
Gwaggo na dariya ta ce"Ka ji min Æ´ar nema. Ai ko ita ta bar miki gado tunda ta bar miki gadon suna mai daraja irin Halimatussadiya."

  Ya na iya?. Domin in dai  Gwaggo ce ta riƙa sharhin sunan kenan da kawo tarihi. Gaisheta na yi cikin girmawa ta amsa ta na faɗin"Na gan ki ke kaɗai ina shi Yusufan?
Na rausayar da kai kafin na ce"Ga shi nan shigowa."

  "Oh. To ina yaran suke? Ko can gida kuka baro su?

Ban amsa mata tambayarta ba. Sai na bige da faÉ—in"Alhajinmu na ciki ne Gwaggo?
Na faɗa ina kallon ƙofar falon shi da na hangi hasken wuta.

  "E. ya na ciki tun ɗazu ya dawo. Zaman jiran ku yake yi. Domin nima sai yanzu ya ke yi min taɗin kuna tafe ke da Ma'u"

  Ta na dire maganarta sai ga sallamar Ma'un ban tsaya ba ni kuma na kara sauri zuwa falon Alhajinmu.
Da nesa kaÉ—an dashi É—akin Gwaggo ne shima akwai hasken wuta daga cikin É—akin, kusa da shi kuma É—akin Mama ce a sakaye, daman in dai ba mu ne muka zo gida ba, É—akin Mama yana yini a sakaye ne
Ɗakin na kallah ta window ya yi duhu alamun an kashe hasken ɗakin gabaɗaya ƙwallah suka taho min na yi saurin shanyewa amman a fili sai da na furta" Allah ya yi miki Rahama Mama."

Lokaci É—aya na cire takalmina akofar É—akin Alhajinmu na shiga da sallama a bakina.

  Alhaji Sulaiman Abubakar Yashe(Alhajinmu) na zaune a saman kujera mai zaman mutum biyu cikin jerin kujerun da suka yi ma falon kwanya. Falon da na girma sosai shi ya sa sai kujerun suka zama a can tsakiya.
  Alhajinmu ba tsoho ba ne, ko na ce yanayin jikinsa na ɓoye shekarunsa. Ya mori jiki saboda bashi da kiɓa tun zamanin samartakansa har kuma girmansa. Dattijo ne wankan tarwaɗa,  mai matsaikacin faɗin fuska da furfura ta gama zagayewa. A shekarunsa zai iya haura 65 amman kuma ba zai ga za  67 ba.

  Cikin yanayin maganarsa da zafin murya irin ta Alhajinmu ya amsa min sallamata.

"Amin wa'alaikis salam. Dubu ce tafe?

Sai da na ƙarisa gabansa na zauna ina faɗin"Ni ce Alhajinmu barka da dare."
Yana yar dariyansu ta manya ya ce"Barkan mu dai. Yana ganki ne kaÉ—ai ko Yusufan ya na waje ne?

Ko kafin na samu zarafin magana Ma'u ta yo sallama ta shigo bayan ta kuma mijinta ne Alhaji mustapha da Yallaɓaina Injiniya Yusuf.

  Itama gaban Alhajin ta zo ta zube ta na gaishe shi, ni dai na matsa can gefe na jingina da kujera suma su Yusuf nan kasan cafet ɗin da ya malale ɗakin suka samu mazaunin zama cikin girmamawa suna gaishe da Alhajinmu ya amsa cikin sakewa da dattako, sai ya karkata kansu yana tambayan su aikinsu da sauran harkoki.

  Ni kuma kaina sai na dukar da kaina ina duba wayata ganin har tara na dare ta gota da kaɗan. Ita kuma Ma'u sai ta tankwashe kafa kamar mutuniyar kirki kanta na ƙasa ban san abin da ta ke yi ba.

  Shigowar Gwaggo ɗakin dauke da shayin Alhaji ya katse hiran ta su, ta miƙa masa a wani ƙaramin mug ya karɓa ya na faɗin"Na gode Maimuna. Allah ya yi albarka"
Ta amsa da Amin. Sannan ta juya suna gaisawa da su Yusuf tunda da suka shigo ta ce su shiga itama ga ta nan zuwa.

  "Ma'u ya gida ya yara? Ina su Alhaji karami?

Gwaggo ta faÉ—a ta na kallon Ma'u. Ita kuma sai ta É—ago ta na faÉ—in" Lafiyan su lau Gwaggo na baro su gida tare da Zainab"
Chapter 8 · 0% Book details