Sashe 40
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Lokacin da na shiga ɗakin mu na ga baƙuwa. Kallon juna muka yi cikin ido tun a wannan lokacin Ma'u ba ta kwanta mini arai ba idanuwanta kir suke a kan mutane. Rahila ce ta tsaya ta na tambayanta ita wacece, ni ina ko hijabin isalamiyata ban cire ba na fita tsakar gidaa in da Gwaggo da ke shanya kaya a igiya sai Mama dake cikin ƙaramin madafin da ke tsakar gida suna kuma hira jefi jefi da juna.
" Gwaggo Alhajimu ya dawo ne?
Na faÉ—a ina kallonta. Ba ita ta bani amsa ba Mama ce ta amsa min da E. Lokacin muna gidan Haya ne kafin mu koma gidanmu na ÆŠorayi Alhajimu ba shi da bangare sai dai yana zama a É—akin duk wacce ke da girki ne.
 Ina so na tambayi wace ce na gani amman na kasa na wuce zuwa ƙofar ɗakin Mama na tsinkayi muryan Rahila ta na faɗin" La Gwagggo wannan wace ce? Alhajimu ya zo da ita daga Yashe?
Ta faɗa bakinta kamar kunne saboda na juya na kalleta. Sai na ji raina ya ɓaci ganinta rike da hannun yarinyar da na ji Gwaggo na faɗin" E sunanta Asma'u. Yarinyar Baabarku Hasiya ce. Anjuma dai Alhaji zai yi muku bayani sosai."
 "Asma'u"
Na maimaita sunan a ƙasan raina. Kai na kauda ganin Rahila na tsallen murna to miye abin murna. Tana da ni to kuma miye na jin daɗi domin an kawo wata. Duk da akiyasin shekaru ba za mu girmi Asma'u ba tabbas sai dai mu zo tsara. Ni da Rahila tare iyayenmu suka yi goyon cikin mu kwana arba'in ne cif a tsakaninmu.
Lokacin da su Yaya Murja suka yo sallama suka shigo gidan suma da Kayan islamiyansu ni kuma na yi sallama a ɗakin Mama Alhajinmu ya amsa sannan na shiga. Sannu da zuwa na yi masa ya amsa ya na kishiɗen kan kujera ganina ya sa ya ɗan miƙe zaune ya na faɗin" Dubu. An dawo?
Na amsa ina gurfanawa a gabansa.
"Alhajinmu ina tsaraba ta? Ko Hajiya ba ta baka wani abu ka kawo mini ba?
Abin da na fara faɗi kenan kuma kamar ba haka ya dace na ce ba. Ƙila ya dace na ce ne" Alhajinmu wace ce ka zo da ita? Amman ban ce ba. Shi kuma bai damu ba yana yar dariya ya ce"Tsaraban ki ta gyaɗa ta nan. Sai da Hajiya ta jadadda mini ke kaɗai ce mai gyaɗar nan."
 Ina jin haka na washe baki na zauna ina tambayan ya ya baro su Baba Aminu ya amsa da duk suna gaishe mu.
"Alhajinmu yaushe to mu za mu ce?
Saboda ina son garin Yashe ina jin daÉ—i in na je garin Hajiya ta na ji dani saboda sunanta aka sakamin shi ya sa ma Alhajinmu da su Gwaggo ke kirana Dubu. Sauran Æ´an uwana kuma Sadiya.
 "Sai kun samu hutun makaranta. Tun ga ma Asma'u in za ta je ganin gida ke da Rahila za ku riƙa rakata."
 Kallonsa na yi kamar zan yi mgana sai na fasa. Sai kawai na bige da faɗin" Yaushe Hajiya za ta dawo gidanmu da zama?
Alhajinmu ya muskuta kafin ya ce"Sai na gama ginin gidana Dubu. Akwai É—akin Hajiya sai na É—auko ta zauna damu? Hakan ya yi ko?
Sai na gyaÉ—a masa kai ina mirmishi. Labarin makaranta ya tambayeni na gyara zama ina bashi labari sai da aka kira sallar mangariba sannan hiran mu ta katse.
 Kowa ya yi alwala domin gabatar da Sallah. Alhajinmu shi da Yaya Abubakar da Yaya Auwal sai Datti suka tafi masallaci Yaya Hamza baya nan ya na Niger can ya ke karatun babban sakandirinsa. Shi Yaya Abubakar je ka ka dawo ya ke yi anan cikin garin kano.
 Ina zaune a gefe ina ganin yadda ƴan gidanmu ke kara kaina akan Asma'u da Yaya Murja ta fara laƙaba mata sunan Ma'u da ya kashe Asma'un ma gabaɗaya. Kowa na rawan jikin tambayata abin da take so ta ci Rahila har tana ɗaukan kayanta ta na saka shi cikin jakar kayan mu na sawa tun da kayanmu na waje ɗaya ne. Ni dai ko magana ta fatar baki ba ta haɗa mu ba kusa da ita ma ban je ba. Har da Gwaggo da Mama a masu kai da kawo akan Ma'u.
Sai da aka yi isha'i su Alhajinmu suka dawo. Kowa ya ci tuwon da Mama ta yi amman ban da ni ba kuma ba na jin yunwa ba ne ina ji amman Rahila ce ta baƙan ta mini rai.
 "Mama ki haɗa mana Tuwon mu tare da Ma'u ko Sadiya?
Tsabar haushi sai kawai na ce"Ni ban ci.".
Saboda na ga daga zuwan yarinya amman Rahila ta fifita ta sama da ni kawai sai na ce na ƙoshi.
Gwaggo ta kalle ni kafin ta ce"Me kika ci?
Sai na rausayar da kai kafin na ce"Bakomai."
Sanin halina na tsirfa wani lokacin sai Mama tace a rabu dani.
Ranar na sha mamaki domin Ma'u kasa cin tuwo ta yi tana ta jagwalgwalawa har su Alhajinmu suka shigo a ka shimfiÉ—a babban tabarma a tsakar gida ana zazzaune ana cin tuwo ni kuma ina daga gefe ina kallon kowa É—aya bayan É—aya.
"Bakuwar nan fa kamar ba ta cin Tuwo"
Yaya Abubakar ya faÉ—a duk sai suka kalleta. Haka ne ko ba ta ci sai wasa take yi da shi a hannunta.
"Ko ba ta cin Tuwo ne Alhaji?
Cewar Gwaggo. Mama ke ce tambayan Ma'u ko ba ta cin tuwo dai dai lokacin da Alhajinmu ya ce"Anya. Ban sani ba. Asma'u a siyo miki wani abun ne?
Sai ta kalle shi amman ba ta yi mgana ba.
"Za ki sha shayi?
Yaya Abubakar ya faÉ—a sai ta kalle shi sannan ta É—aga kai alamun eh. Na sandare a zaune lokacin da Alhajinmu ya ciro kuÉ—i daga aljihunsa ya ce Yaya Abubakar ya je ya haÉ—o kayan haÉ—a shayi a haÉ—a ma Asma'u tunda ba ta cin tuwo. Da fitansa da sauri da tashin da Rahila ta yi ta ce bari ta sa ruwan zafi sai Mama ta ce akwai ma a saman tukunya a madafi.
A daran nan dai Ma'u shayi ta sha da buredinta. Ahalin har Alhajinmu tuwo ya ci. GabaÉ—aya hankalin yan gidanmu na kanta kamar sun ga wata sabuwar hallitta. Ina ji Alhajinmu na kora bayanin wace ce Ma'u a garemu gabaÉ—aya.
"Ɗiyar ƙanwata ce Hasiya. Mahaifinta ya rasu ɗan nan garin Yashe ne. Ta dawo hannun Hajiya da zama shi ne da na je na ganta na taho da ita za ta zauna da mu har abada."
"Allah ya taya mu riƙo Alhaji."
Gwaggo da Mama har suna haÉ—a baki wajen faÉ—a.
"Æ´ar uwan ku ce Ina fata za ku kalleta a matsayin jini É—aya."
Yaya Abubakar ya amsa da in sha Allahu.
 Yaya Murja ta yi karaf ta ce"Muna son ta Alhaji. Ga ƙawa ma na yi mata Rahila."
A lokacin ƙankance ido na yi ganin ta haɗa hannun Rahila da Ma'u waje ɗaya. Saboda sun zauna daman a kusa da juna ne. Ita kuma Rahila sai mirmishi take yi a yayin da Ma'u ke kallon kowa da idanuwanta. Tun kafin zuwan Ma'u daman ni da Yaya Murja ba ma zama a waje ɗaya saboda ta na da faɗa ni kuna ina da baki ta bakin ta ta ce ba ni da kunya manya na mgana ina saka musu baki.
"Har da Dubu ma. Saboda na ga za su yi tsara ya sa na samu karfin gwiwan É—auko Asma'u."
Alhajinmu ya faɗa sannan idanuwansa suka fara laluɓena sai ya ganni a can baya ina zaune.
"Dubu..'
 Â
Ya kirani kamar yadda ya saba kirana sai na amsa. Sai ya ya fito ni da hannu na taso na zo gaban shi.
"Dubu ba ki ga yar'uwan ki Asma'u ba ne?
Na juya muka kalli juna ni da ita sai na kauda kaina kafin na ce" Na ganta."
Ya na mirmishi kafin ya ce"To ga ta nan ke da Rahila na bar ma Amanan Asma'u. Ku yi ƙawa da ita kun ji ko?
Ni dai kai na ɗaga Rahila ce ta amsa har ta na cewa" Alhajinmu a saka ta a makarantar mu don Allah"
Sai kawai na ji Alhaji na faÉ—in "In sha Allahu tun da daman Hajiya ta ce ta gama firamari sai na saka ta a tare daku har islamiya ma"
Sai kawai Rahila ta rumgume Ma'u tana murna.
A lokacin Yaya Abubakar ya kalleni ya ga na haÉ—e rai sai kawai ya kalli Ma'u yana faÉ—in" In Sadiya ta yi miki wani abu kar ki raga mata ki rama kin ji ko?
Ya faɗa yana kallonta lokaci ɗaya yana nuna ni. Ana ta dariya har Alhajinmu. Amman ni ban yi dariya saboda ni ban ɗau abin da wasa ba. Mun ƙara kallon juna ni da Ma'u na wani lokaci sannan kowa ya ɗauke kansa.
Yaya Murja har tana faÉ—in" Wallahi kuwa. In Sadiya ta ga sakenta ai ta shiga uku."
Mutane biyu da suka fara bin bayan Ma'u tun kafin tafiya ta yi nisa. Suna faÉ—a mata abu mara kyau game dani.
 A wajen kwanciya ma na ga abu. Mu uku muke kwana a karamar katifa a ƙasa ni da Rahila da Amina. Amman sai Rahila ta jajibo mana Ma'u ban iya shuru ba sai da na ce" Rahila a ina za ta kwanta? Ko ke za ki kwana a ƙasa ki bar mata wajen ki?
Daga mgana sai aka ga laifina. Kawai sai Yaya Murja ta fara zagina su suna babban gado ita da Yaya Balki. Gwaggo sai da ta shigo ta raba faÉ—an da har Yaya Murja ta ce Ma'u ta dawo gadon su ta bar mun katifar sai Gwaggo ta ce Amina ta koma wajen su Yaya Murja mu kuma mu kwanta mu uku ban ji daÉ—in hukunci Gwaggo ba amman ba ni da mafita ni ta kafafunsu na kwanta Rahila na bari da kwanciya filo É—aya da Ma'u.