← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 76

Sashe 33

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai bayan an kai shi É—aki na musamman ne aka bar mu muka shiga yana barci amman Alhajinmu duk ya rame ya faÉ—a. Daga gani ya daÉ—e da ciwo a jiki bai faÉ—a ba an ce mu bar shi ya samu hutu sosai sai muka fito dukkanmu zuwa kofar É—akin muka zauna saman kujerun wajen. Mijin Ma'u ya yi ma Gwaggo sallama zai tafi ita kuma ta tafi raka shi.
Sai bayan sun wuce ne Ya Balki ta kalleni taba faÉ—in" Sadiya ya gida? ÆŠazu kin zo hankula ba a kwance suke ba ba a gaisa ba."

Sai na ɗan saki fuska muka gaisa buɗe bakin Yaya Murja sai cewa ta yi" Duk da haka ta ganmu amman ta fi ƙarfin ta ce mana sannu."
Nima sai na kalleta kafin na ce"Saboda me zan ce muku sannu? Kun ware ni a cikin dangi ba wacce ta iya kirana ta faÉ—a mini halin da ake ciki sai Ya Auwal dake Abuja ne ya kirani ya faÉ—a mini. "
Yaya Balki ta ce"E ba a kyauta ba to ki yi hakuri. Nima Ma'u ce ta kirani ta faÉ—a mini ta ce itama Yaya Murja ce ta faÉ—a mata.'

  Shekeƙe na kalle su kafin na taɓe ba ki na ce"Ai da ya ke Ma'u ce ake son ta sani an kirata an faɗa mata ba shikenan ba."
Rahila na taka min kafa wai in yi shuru cikin masifa na ce"Sai kin ƙi faɗan gaskiya! Wa na ke tsoro?
Gwaggo ba ta nan ta na ciki wajen Alhajinmu.
Ya Muntari ne a wajen ya kirana sunana ya na faÉ—in" Asibiti ne fa nan ba gidan biki ba. Ku bari ku koma gida mana."

Yaya Murja kuma sai ta taɓe baki ta ce"To daman ai mun san baki tsoron kowa mara kunya. Hassada ce da kishi saboda ta ga Ma'u ta riga ta zuwa. An ce ki yi hakuri kuma sai ki na neman gaya mana mgana"
Anty Aina ta tsawatar ta ce a bar mganar ni ko ba na barin ta kwana na ce"Allah ya tsari Sadiya me Ma'u ta mallaka a duniya nan da ni ban da shi sai na yi mata Hassada! Ai ba ta kai ba tukunna dai."
 
"Zan fa ci ubanki Sadiya ni ba tsaran ki ba ne wallahi."

Zan sake mgana Anty Aina ta daka min tsawa ta na faÉ—a min" Wai ba na ce ki yi shuru ba ne Sadiya?
Kaina na kawar gefe ina kaɗa kafata cikin bacin rai. Yaya Balki ta ce"Ita Yaya Murja saurun fusata  ita kuma Sadiya rashin kunya. Alhajinmu na kwance ba lafiya ma ba za su fasa ba."

"Ba za su fasa ? Me ya faru?

Yaya Abubakar ya faɗa yana ƙariso wajen tare da Ma'u sun jero
Ba wanda ya yi mgana sai Zaituna.
 
"Sadiya ce da Anty Murja suke cacan baki."

Yaya Abubakar ya kalleni ya kalleta kafin ya ce" Me ya faru?
Anty Balki ce ta maida masa yadda aka yi kawai sai ya juyo yana kallona kafin ya ce" Ni ne nan na kira Murja na faÉ—a mata na kuma ce ta kira Ma'u da sauran ta faÉ—a musu. Tun da sun ce ki yi hakuri sun yi kuskure ba shike nan ba? Ko ke shikenan ba a baki hakuri ki hakura?

Ko kallonshi ban yi ba sai da na ji ya ce"To kar ma ki fasa. Ke daman ba ki son zaman lafiya ko da yaushe cikin ƙananun mganganu kike."
Ɗagowa na yi ina kallonsa cikin ɓacin ran dake cikin idanuwana shi kuma sai ya juya yana ma Ya Muntari mgana.
 
"Ka na ji suna hayaniya ba ka tsawarta musu ba?

Kai tsaye ya ce" Na yi mgana sun ki ji shi ya sa na kyale su. "
Kawai sai ya juya ya na kallona kafin ya ce" Duk wacce ta san hayaniya ya kawota ta tashi ta ƙara gaba. Mu lafiyan mahaifimmu muke nema ba tashin hankali ba."

"Ka yi hakuri ya Abubakar. Sadiya kema don Allah ki yi hakuri. Har ni na kira wayarki ba ta shiga."

Ma'u ta katse surutun na shi.
"To kin ji ma."
Ya faɗa ya na kallona dakyar na iya danne ɓacin raina na kalli Ma'u ina faɗin" Ya wuce."
Sai ta yi mini mirmishi na mayar mata da yake. Kusa damu ta zauna amman gefen Rahila. Shuru kawai na yi ina danne yanayina ni fa daman da Yaya Murja da Yaya Abubakar haushin su na ke ji tun kan abin da ya faru. Kuma har gobe na san suna bayan Ma'u ne. In da suka ijiyeni nima nan na ijiye su.

  Kiran wayar Yallaɓai ya sa na tashi na bar wajen.
Yana tambayanta ya jikin Alhajinmu na faÉ—a masa da sauki da yadda ake ciki.
"Allah ya ƙara sauki muna idar da sallar  jumma'a zan taso kin ji ko? Ban da damuwa ok?
Sai na gyaÉ—a masa kai kafin ya cigaba da faÉ—in" Yara fa! Ina kika kai su?
"Suna gida tare da Saude."
Sai ya sauke numfashi kafin ya ce"Sai na dawo."

Da haka muka yi sallama. Ganin har azahar ta yi sai na fita haraban asibitin na tambayi wata nurse masallaci sai ta nuna mini. ga mata nan suna alwala mazan dai ina ga waje za su fita su samu sallar jumma'a nima sai na bi bayansu na yi alwala muka shiga masallaci na yi sallah na zauna ina addu'o'i bayan na shafa sai na kira wayar Amina sai ta ce minI ita Yaya Aina ta kira ta faÉ—a mata mijinta baya nan amman in ya dawo in sha Allahu suna tafe gobe na ce Allah ya kaimu.

Muna waya Khaleesat na kirana bayan na katse sai na kirata jikin Alhaji ta tambaya na ce da sauƙi ya na barci ita ke faɗa min suna hanya na yi musu fatan isowa lafiya. Na daɗe a masallaci sai da Rahila ta kirani ta ce ko na tafi ne? Na ce a" a ina masallaci.

"Oh mu ai nan muka yi tamu sallar. Ki zo ga su Baba Aminu  nan sun iso."

Sai na ce mata gani nan zuwa. Ji fa har mutanen jihar katsina sun ji labari sun iso amman ni ana raina min wayau. Kuna ina da tabbacin cikin su ne wata ta kira su ta faÉ—a musu.
Na fito daga masallacin zan wuce bangaren dakin da Alhajimmu ya ke na ci karo da Baaba Asiya ta na ta neman ɗakin kamar ma ta na kiran waya ne ƙila Ma'u take kira sai na ƙarisa wajenta ina faɗin" Baaba."

Sai ta juyo ta na kallona fuskarta kadaha kadahan kamar yadda muka saba karɓan juna tun bayan faruwan rushewar auran Ma'u da Yaya Hamza da na zama ni ce sila."

"Yauwa. Ma'u bari ma ga Sadiya na gani."

Daga haka ta katse wayarta. Da yar jaka a hannunta da kayanta a ciki.

"Sannu da zuwa Baaba"

"Yauwa dai."

Sai na mika hannu zan karɓi jakar sai ta hanani ta wuce gaba tana faɗin" Ina ne ɗakin da aka kwantar da Yaya Sulen?
Ban damu ba na wuce ina faÉ—in" Ciki ne."
Ba tun yau ba ni na san ta tsane ni ita da yarta. To nima dai ɗin ba wani son su nake yi ba shi ya sa ban taɓa damuwa ba matar da na san ba ta ƙaunar uwata ina zan taɓa ganin farinta.
Ta bakin Hajiya Dubu da ke yawan faÉ—in" Asiya ki daina wannan dabi'un naki karki tsufa kuma tsufar ta zo ta yi miki gardama."
Allah ya jiƙan Hajiya Dubu da gafara. Mutuwarta da mutuwar Mama sai nima na mutu  zan iya mantawa da su.
 
  Muna tafe ina gaba ta na baya har zuwa ɗakin da Alhajinmu ya ke. Baba Aminu ne ashe da Baba Sani suka zo. Ma'u na ganin uwarta ta yi wajenta tana mata barka da zuwa.
Ban ƙara ta kan su ba na isa wajen su Baba Aminu ina gaishe su.

"Lafiya lau! Dubu ce?
Sai na ansa musu domin kaf gidan su Alhajinmu ba mai kiran sunansa sai dai Dubu saboda na ci sunan Hajiya Dubu ce kuma ita É—in mai Daraja ce ta matsayin uwa a wajen su.

  Da ɗaya da ɗaya likita ya ba su izinin shiga su ga Alhaji. Da suka fitio ne na ji Baaba na faɗin Yaya Sule ya ya ɗan farka yana ta mganganu har yana kiran sunan Ruƙayya
Gabana ya faÉ—i Mama kenan fa. Kar shima dai Alhaji tafiya zai yi ya bar mu? Likita ne ya ce daga yanzu ba wanda zai sake ganinsa sai dare a barshi ya huta.

  Kowa ya ji labari amman ban da Datti na ce aƙyale shi saboda suna da test kar mu ɗaga masa hankali. Ma'u ta kira gida yar aikinta ta yo abinci direba ya kawo tare da Zainab. Dukkanmu ba wacce ta koma gida sai Zaituna da mijinta ya ce ta koma gida Gwaggo ma sai bayan la'asar da su Baba Aminu suka matsa sannan ta yarda Yaya Abubakar ya ɗauketa a mashin ɗinsa ta koma gida ta yi wanka sannan ta ɗauko ma Alhaji wasu kaya ruwan zafi da kayan Tea Ma'u ta saka an kawo. Abincin da ta kawo shi kowa ya ci amman ban da ni. Har su Baba Aminu shi suka ci Rahila ta ce ba zan ci ba na ce ta san ban iya cin wani abu a asibiti.

  Wajajen biyar Yaya Hamza suka iso tare da Khaleesat da yayansu Amna da Tasleem. Ba daɗewa tsakani sai ga Yaya Auwal da Anty Laila suma sun iso asibtin diret ko gida ba su je ba sai da suka leƙa Alhajinmu suka ganshi sannan hankalinsu ya kwanta. Yaya Auwal yana zuwa ya ba da kuɗi aka siyo kata  katan ɗin ruwa da lemuka. Ya yi kuma oder abinci na dare tunda muna nan ba wacce ta iya koma gida sai Gwaggo. Ita kuma a can gida Yaya Abubakar ya siya anta ya kai mata za ta dafa ma Alhaji tunda sun ce yana bukatar cin wani abu mai ruwa ruwa haka.
Chapter 33 · 0% Book details