← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 76

Sashe 31

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai a lokacin ya juyo ya kalleni kafin ya ce"Bikin ya zo ne ba ki ji ba? Sai na girgiza masa kai jinjina kai ya yi kafin ya maida hankalinsa kan kallon shi lokaci É—aya yana faÉ—in" Ba ma yanzu ba ne. Ina jin sai nan da wattani huÉ—u sai yarinyar ta gama karatun ta ta dawo tukunna za a yi bikin."

"Au daman yarinyar ba anan take ba?

"E. ÆŠiyar ogansa ce a wajen aiki. Tana london ta na karatun masters É—in ta amman ta kusa dawowa in ta dawo ne za a yi bikin."

Ƙara matsan Yallaɓai na yi domin ina son na ji labari kai tsaye na ce" Ikon Allah. Kuma ya na sonta? Wannan karon wani kallo Yallaɓai ya yi mini da ya sa na yi shuru ina yar dariya kai ya girgiza kafin ya ce"Ban san wannan ba. Shi kaɗai zai iya amsa miki wannan tambayar.".

  Ina dariya na ce"Kai ma za ka iya."

Bai ƙara mgana ba sai na kwantar da kaina saman kafaɗarsa ina faɗin" Na yi mamkin da na ji zai ƙara aure. Duk irin yadda suke son juna shi da Anty Zabba'u.''
Yallaɓai dai ya lura da mgana a bakina sai bai biye mini ba sai kawai ya kallleni kafin ya ce" Uhm"
Ina shafa kirjinsa na ce"Wallahi. An ce fa ta yi yaji ta na kano yanzu haka. Gaskiya ban ji daÉ—i ba. Kuma har yau shi Yaya Usman bai zo biko ba ya kyauta kenan?

  Yallaɓai ya muskuta kafin ya cire ni daga jikinsa yana kallona cikin buɗe ido ya ce" Sadiya a ina kika ji wannan maganar? Kai tsaye na ce" Yau da na je gidan Halima ta ke faɗa mini fa. Ko ba a yi ba ne?
Kai ya girgiza kafin ya ce"Ban sani ba. Domin ni a bakin ki ma na ji wannan mganar."

Da sauri na ce"Au wai ba ka sani ba? An ce ko ba ta a fatakol. Ta dawo kano domin Halima ta faÉ—a mini bai faÉ—a mata mganar auran ba sai da aka saka rana da ta ji shi ne ta tada hankalinta ina ga dalilin yajin kenan."
Ƙura mini ido ya yi yana kallona nima ko ina kallonsa ban damu ba na cigaba da faɗin" Gaskiya Yaya Usman bai kyauta ba. Bai kamata ya yi ma Anty Zabba haka ba an zama ɗaya an tara iyalai yayansu biyar fa aurensu sama da shekaru ashirin a ji Anty Zabba ta yi yaji saboda zai ƙara aure ai wallahi sai an zage shi duk da ban sani ba ai na san ba ta rage shi da komai ba. Wani lokacin ku Maza ba ku da adalci in za ku ƙara aure a ƙokarin ku sai duniya ta fahimci mace ta gaza ne ya sa kuke son ƙara aure"

"Shi ya ce miki saboda Zabba'u ta gaza ne ya sa ya ke son ƙara aure?

Ya katse mini mgana nima ko na taso masa da cewa" E mana saboda ya yi munafunci miye a ciki in ya na son ƙara aure da ba zai faɗa mata ba sai da mgana ta kamkama bayan ma an saka rana?
A hankali ya ce" To ai Ogansa ne ya bashi yarinyar kuma akwai girmamawa a tsakaninsu shi ya sa ya karɓa".

Mamakin Yallaɓai ya kamani yadda ya zauna ya na kare ma ɗan'uwansa..
 
"Duk da haka dai ai yana so ne ya karɓa shi fa namiji ba a yi masa dole Yallaɓai na. Kuma tun da har ya amsa me ya sa bai zo gida  sun tattaunawa da matarsa ba? Tsakani ga Allah bai kyauta ba a ce sai da aka saka rana ya ke gaya mata ko ni ce zan yi abin da yafi nata. Yanzu ta koma gida in an zauna ana mgana sai a ce saboda mijinta zai yi aure ta tada hankalinta ta kasa zaman gidanta ahalin abin ba haka ba ne shi ne bai kyauta mata ya yi mata rashin adalci bai kuma kalli zaman auren su na tsawon shekaru ba"

  Yadda na ɗau zafi kamar ƙanwar Zabba'un abin ne ya ɓata mini rai ganin Yallaɓai na nuna abinda ya yi ɗin dai dai ne.
Kallona kawai ya ke yi ya ina ta faɗa sai kawai ya juya ya jingina da kujera ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa amman bai yi mgana ba sai ni ne da na gaji na kalle shi ina faɗin"

Yallaɓai ba ka ce komai ba?

Kai tsaye ya ce" Me zan ce! In yi mgana ki ce ina kare masa saboda yana É—an'uwana ko in ce ita ba ta kyauta ba ki ce sabo da ni Namiji ne ko?
Baki kawai na saki ina kallon Yallaɓai ganin kamar ya ɗau lamarin da zafi. Ban gama mamaki ba na ji ya na faɗin" Ke ba ki san abin da ya faru ba kin bi kin zauna akai har kina zargin wani bai kyauta ba a mata da miji ba ka jin bangare ɗaya ka yanke hukunci shin shi kin ji na shi ne! Kin san me ya faru tsakaninsu da ya sa ta yi yajin? Kuma ban yarda Yaya Usman bai faɗa mata ba sai dai in ita ce ta ƙi amincewa tun farko daga baya da ta ga abin da gaske ne sai kuma ta sauya labarin. Mganar yaji kuma ita ce ta ji kunya miye na ta na yin yaji? Auransu shekara ashirin ko sakin ta Yaya Usman ya yi gidan nan ya zama nata. Hakan da ta yi ta nuna cewa ba za ta iya rufa ma mijinta asiri ba ta gwamace ta koma gida ta fallasa komai domin a san halin da suke ciki a yi musu dariya kuma wallahi kanta ta rage ma ƙima in ma tana tunanin ta yi ne domin samun wata daraja ko ɗaukaka in ta yi hakuri wallahi tallahi wata ba za ta zo ta fita ba ba kuma ina kare masa domin yana ɗan uwana ba sai domin na san halin shi adali ne kuma jajircettace ai yana sonta ya aureta ba zai zama domin ta gaza ba ne zai ƙara aure sai domin auran na cikin kaddaran Rayuwansa"

  Idona a kan Yallaɓai ganin yana ta rattabo mgana.
"Hmm "
Kawai na ce kafin na yi shuru shima shurun kawai ya yi yana cigaba da kallon shi ban sake mgana ba ina auna mganarsa a zuciyata ba wani saboda yana ɗan'uwansa sai kuma domin ya na Namiji amman ko Anty Zabba na da laifi shima Yaya Usman ɗin ya na da laifi ni ko kwana za mu yi anan wajen maganganun Yallaɓai ba za su sa na daina ganin laifin Yayansa ba.

HaÉ—e rai na yi har ina matsawa can nesa da shi kallona ya yi kafin ya yi É—an mirmishi ya na faÉ—in" Ni ban kare masa ba. Gaskiya na faÉ—a miki. Sannan ki cire wannan tunanin na in namiji zai kara aure wai gazawar ta gida ce ba haka ba ne saboda shi aure da mutuwa duk É—aya ne ba ka sanin lokacin in Allah ya kaddaro maka ne ba yarda za ka yi amman ba nufin ta gida ta gaza ba."

  Taɓe baki na yi kafin na ce" Haka kuke nunawa shi ya sa muka ɗauka haka ɗin ne."
Na faɗa har ina hararan shi sai kawai ya yi yar dariya kafin ya ce"To ke miye naki a ciki! Tun da ba ni ne zan ƙara auren ba."
Ina mele baki na ce" Da nawa a ciki tunda mace ce Æ´ar uwata kuma muna aure a zuru'a É—aya."

Kawai sai ya fara mini dariya na kalle shi ina faÉ—in" Na zama abar dariya ne? Hannu ya É—aga sama kafin ya ce"Ko É—aya gani na yi har matsawa kika yi daga kusa da ni. Ni ne Yaya Usman É—in?
Tabe masa baki na yi sai ya fara matsowa kusa da ni yana faɗin" Yanzu dai Yaya Usman bai yi ma Zabba'u adalci ba ko? Mata ban san me namiji zai yi ya iya muku ba. Auran su sama da shekaru ashirin bai yi tunanin ƙara aure ba sai yanzu. Da ace ya ce zai yi a farkon auren su sai a ce daga yin aure zai ƙara mata kishiya in ya bari sai ta ɗan sha miya sai a ce sai da ya ga ya sun gama wahala tare ya yi kuɗi zai saka mata da kishiya in kuma ya bari ta manyanta sai a ce ya ga ya gama moran ƙuruciyanta zai ƙara mata kishiya. Mara adalci butulu duk kalaman ku ne. Na rasa ko wani yanayi ne na kishiya zai taɓa zama dai dai a wajen ku.'

Kafin ma ya ƙariso na yi saurin miƙewa ina faɗin"Ba wannan yanayin domin ba macen da ke son zama da kishiya. Ko a gidan Annabin Rahama matansa sun yi kishi ballatana mu."
 
Shima miƙewan ya yi yana yar dariya kafin ya ce" To wai an ya ni za ki bari na ƙara auran nan? Wata uwar harara na wurga masa kafin na ce" Ai na san ka na da ra'ayi. Allah ya ba da sa'a. Ta zo mana tunda ba kaina za ta zauna ba "
Chapter 31 · 0% Book details