← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 76

Sashe 56

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daran muka fita mu ka je Gwammaja mu ka kaima Nene nata ya ƙara mata da 20k tana ta saka albarka farko ma ta ce ba za ta amsa ba ni na ce ta karɓa.
Sai ta saka hannu ta karɓa tana faɗin" Komai fa suna yi min Sadiya to kuɗin kuma na mene ne?
Ina mirmishi na ce" ki rike a hannun ki Nene kina yin baki da ga Rano ko na sallamansu kya samu."

"Haka ne. Na gode Allah ya yi albarka"

Muka amsa da Amin Amin muna gidan sai ga Mimisco(Anty Zuwaira) ita da mijinta itama kayan abincin ta zo da shi da kayan tea, sai mganar zuwa ganin likita ga Nene, tunda nauyin asibitin na ta Mimisco ce ta ce a bar mata za ta iya.

Mun gaisa  da ita kamar yadda muka saba ni dai ban taɓa samun matsala da ita ba. Tana da ilmi ta kuma san yadda za ta zauna da jama'a. Saboda zuwanta ya sa muka ɓata lokaci tunda Yallaɓai suna ta hira da mijinta. Sai wajen tara da rabi muka baro gidan bayan Yallaɓai duk ya shiga ɗakunan su Hajiya Iya ya ba su 10k kowacce suka karɓa suna godiya a hanya ne ma da za mu je Ɗorayi Yallabai ke faɗa, min Yaya Usman ya shigo garin  jiya amman bai kwana ba ya koma a ranar.

"To. Ya zo biko ne?

Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce" Ban sani ba. Na san dai ba zai rasa zuwa gidan su ba."
Sai na jinjina kai kafin na ce" Hmm. Allah ya kyauta.".
Saboda ina so na yi magana ina tsoron  kar Yallaɓai ya taso min shi mai ɗan uwa.

Mun fara zuwa gidanmu muka sake duba Alhaji 20k Yallaɓai ya ba ma Alhajinmu. Gwaggo kuma 10k suna ta saka albarka. A bakin Gwaggo na ji labarin yau da safe Baaba ta koma na ce Allah ya tsare. Daganan mun shiga gidan su Saude 50k Yallabai ya ba ma Balaraba daman a wata 30k kuɗin aikinta amman Yallaɓai na yi musu ihsani kuma kafim mu baro gidan sai da ya yi mganar ya na so ya saka Saude a makaranta bai da ce a barta haka ba karatun boko ba, ta gama firamari ba ta cigaba ba. Mahaifiyarta har da hawaye tana ta godiya zaman amana ne da maƙotaka ya haɗamu har na ga Saude na ce ta riƙa zuwa tana kama min aiki saboda na taimaka musu.

Daga gidan su Saude gida muka dawo tun da daman mun yi sallama da su Gwaggo muna hanya Yallaɓai ya ce na tura mai acct number Datti zai saka masa wani abu ina ta masa godiya.

"Tsakanin mu ba Godiya Sadiya ta."

Haka ya faɗa ya na kallona ni kuma sai na yi masa mirnishi kafin na ce" Duk da haka dai zan gode maka. Yallaɓaina Allah ya sa a fi haka."
Sai ya amsa min da Amin muna yi ma juna mirmishi.

*****

Washegari da sasaafe, bayan Yallaɓai ya ja mun yi ta barnar ruwa ni dai ai nace dole zan kira mai kitso kafin Yallaɓai ya sa gashina ya sauke ƙasa saboda jiƙashi da na ke da ruwa.
Sai bayan su Jidda sun tafi makaranta a gurguje muka yi abin da aka umarcemu mu kawo daga Lab. Saboda yadda ya jadaddamana cikin sauri muka yi wanka Yallaɓai ya kai ni asibitin na kai musu da sauri suka karɓa bayan na haɗa musu da takardan da suka ba ni shekaranjiya. Suna karɓa suka ce mu jira a waje za su ba mu result ɗin.
Tare da Yallaɓai muka yi zaman jira ana ta kiran shi ma a office bai tafi ba sai da aka gama test ɗin suka kuma bamu result ɗin da cewa zan kaima likita ranar clinic ɗina.
Daga nan Yallaɓai ya dawo da  ni gida ya ijiye shi kuma ya wuce office domin ya faɗa mini akwai kwangilan da ya samu na zanen wani kamfani da za a buɗe a kaduna ne. Na bishi da Allah ya ba da sa'a shi ya wuce ni kuma na buɗe gida na shiga.

Ban san me result É—in ya nuna ba tunda rubutun likitoci sai su sai na adata kafin ranar Monday. Ranar yini na yi gugan kayan under É—in mu da na wanke mana na goge su tas na feshe da turare, na jera mana a cikin wardrope, ganin na samu natsuwa ya sa na É—au wayata na kira Aisha lame na yi mata mganar ina son Body lotion, sau Face soap sai Fade cream sai showergel na wanka

Sai ta ce mini za a kawo mini sai na ce kamar yadda muka saba zan tura mata kuɗin ta, Aisha Lame ba abin da ba ta saidawa na gyaran jikin mata. Kuma kayan ta suna da kyau da inganci su na ke amfani dashi shi ya sa kullum Yallaɓai sai ya ce ya na son taɓa fuskata saboda taushi da santsi sannan ba guraje, jikina kuma ya yi fresh ya yi taushi domin Showe gel ɗin ta ba baya ba yana bala'in gyara fata.
Cantact Aisha lame.
+234 703 666 2633
Tana aikawa da kayanta ko'ina a faÉ—in Nigeria

Daga ita sai na kira Surayya Dee mai kayan gyara na BOJUWA ta dalilin Aisha lame na san Surayya. Kuma na yi amfani da kayanta na yaɓa da ingancinsu.

Ni duk bayan wata uku na ke shan mganin sanyi sannan na ɗora da na gyara Ni macece da ta yarda da gyara shi ne har gobe ya sa na ke da matsayi a zuciyar Yallaɓai. Duk da har kayan marmari ba na wasa da su da duk abin da zai kawo mini Ni'ima amman kuma ban zauna ba ina gyaran jikina tare da can ainihin majalisar ɗinkin duniyan gabaɗaya.
Maganin infection na ce ina so Surayya ta aiko minibda shi in na gama zan siya kazan uwargida tana ta dariya ta ce" Hajiyar Injiniya ba a dai gajiya da gyara."

Nima ina dariyan na ce" Ba a gajiya Hajiya Surayya. Gyara shi ne mace da gyaran ya sa har gobe muke ƙyalli a idanuwan mazajen mu."

Tana ta dariya mun rabu akan yau É—in nan mai kawo mata kaya zai kawo mini tun da ya san gidana, tun da ba yau muke tare ba, sama da shekara É—aya tun da na gwada kayanta na san ingancin su.
Domin ke ma ki dace da ingantattun kayan gyara contact Surayya Halin yau on
+234 803 277 3332. Kano Nigeria tana aikawa da kayanta ko'ina.

Zuwa yamma sai ga saƙon Surayya Halin yau, a daran kuma na tura mata har kudin kazar da zan siya. Mayuka na bangaren Aisha lame kuma sai washegari da safe ta aiko mini dashi.

Ranar jumma'a gidan Rahila muka yini  ni da su Jidda, Rahilar ba ta da lafiya zazzaɓi daga ita har Bbyn na ta sai dare Yallabai ya je ya dauko mu, mun sha hira mun yi tsiya mun yi daɗi ta ji sauƙi tun da har kitso sai da ta yi mini daman ta iya ta rufa mini asiri kafin Yallaɓai ya saka ruwa ya sauke mini gashi.
mun rabu da Rahila ta roƙe ni ƙanwar mijin Ma'u za ta yi aure za ta biyo mini mu je tare kai tsaye na ce" In ta gayyace ni ba? In ba ta gayyace ni ba wallahi ba zan je gayyar soɗi ba."

Rahila na dariya ta ce" Ki ji tsoron Allah Sadiya. Ke yanzu sai kin jira Ma'u ta gayyace ki."
Ina hararanta na ce"Kwarai kuwa. Kawai tusa kai ba kwarjini in ta gaya min zan iya zuwa amman ba ta gaya mini ba sai dai na ce a sha biki lafiya."

Washegarin asabar kamar ta san mun yi maaganar da Rahila sai ga shi ta tura mini katin biki sannan daga baya ta kirani.

"Ina fatan za ki zo dai zo ko Sadiya?

Sai na ce mata in sha Allahu tun da sati na sama ne.

******
Ranar Monday, na koma asibiti na ga Dr Aisha bayan na ba ta sakamakon ta duba cikin ikon Allah ta ce da ga ni har Yallaɓai sperm din mu suna active matsalan ba daga nan ba ne yanzu tun da an yi wannan an tabbatar da ba matsala za su yi focusing a kaina ne.

Sai ta rubuta mini blood tests to look hormone levels. Na je na kai lap aka ɗibi jinina suka ce na dawo nan da kwana biyu domin karɓan result. Tun ina hanya na kira Yallabai na faɗa masa likita tace matakin farko ba matsala yanzu dai sauran gwaje gwajen akai na ne.

"Alhamdulillah. Suma sauran in sha Allahu ba matsala."

"In sha Allahu."
Na amsa masa cike da yaƙinin hakan

A satin Hauwa ta zo gida na ta yini ita da yara a bakin ta na ke jin Anty Zabba ta koma amman sai bayan Yaya Usman ya koma ni ko sai na ce" Ya fi mata. Amma ba ta gina gidanta ta bar ma wata shi saboda kishi ba."

Sai dare Muttaƙa ya zo ya dauke su.
Washegari gidan Halima na je na kai mata Atamfar da na da siya mata a Dija collection+234 903 661 7473
Domin kayanta ta na ba da su ne akan farashi sari mai sauƙi.
Sai na siya rigar yaro ssi pampers da na je sai na ɗora mata 5k na ce nawa ne kuɗin kayan kuma daga Yallaɓai ne tana ta godiya a gabana ma ta kira shi tana yi masa godiya ya ce ba komai.

Ina shirin tafiya sai ga Anty Bahijja wai sun zo nan kusa ne ganin gidan da ƙanwar mijin Ma'u za ta zauna shi ne ta biyo wajen Halima. Da gangan na yi ma Anty Bahijja taɗin bikin ina dariya na ce.

"Anty Bahijja ashe biki gare ku ba gayyata."

Sai ta kalleni kafin ta ce" Ba ni ya kamata na gayyace ki ba Ma'u ce."
Ina mirmishi na ce" Ai fa ta gayyace mu muna nan zuwa."

Na ga ta kalleni da mamaki amman sai ta shanye ta ce sai mun zo ni dai anan na barta na koma gida da wuri saboda yara.
Chapter 56 · 0% Book details