Sashe 60
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sati ɗaya da dawowarta Yallaɓai ya ce na shirya muje Rano domin na ƙara yi musu gaisuwa ban yi musu ba na shirya ashe tare da Mutakƙa ne da Hauwa sai na ji daɗi a motar Yallaɓai muka je ranar weekend yara kuma wajen Nene muka bar su gabaɗaya.
Mun je mun iske mutane cike a gidan a kallah dai ba za ta yi kaɗaici ba. Sannan ga babbar Aminiyarta babbar ɗiyar Anty Zuwaira Naja'atu duk da ita Gimbiya ta girmi Naja'atu amman kuma Allah ya haɗa wannan kawancen lokacin da aka yi rasuwar ita da mijinta ba sa ƙasar suna Italy. Kuma lokacin da aka yi rasuwar ta so dawowa sai matslan visa ya hana ta sai dai su yi mgana a waya to faa sai cikin satin nan ta dawo. Amman a kano take aure da yaron wani mashuririn ɗan kasuwa a garin kano mai suna Buhari manga. Ba su cika ma zama a Nigeria ba yawancin kuma duka yayan da Naja'atu ta haifa guda uku a kasar waje ta ke zuwa ta yi renon cikin ta ta haihu.
Ita muka iske tare da Gimbiya wacce ta faÉ—e ta rame sai dogon fuska da hanci bakinta duk ya bushe idanuwanta duk sun zurma. Tana sanye da hijabi da caabaha. Mun gaisa da Naja'atu duk ba wani damuwa da mutane ta yi ba, irina ce shi ya sa na ke yi mata uzuri ban cika damuwa da halinta ba ammam duk in da muka haÉ—u za ta gaisheni da tambayan su Jidda.
A ɗakin Hajiyar Tafida muka zauna ita kuma Gimbiya da ƙawayenta suna ɗakin Hajiya Kaltume kamar acan aka sauke ta tana takabar nata. Muna Rano har bayan la'asar na yo alwala daga bayin waje Hauwa ta rigani yin na ta shiga ɗakin Hajiya ni kuma lokacin da na yo tawa sai na ga maza sun shigo yan gaisuwa sun shiga ɗakin sai na wuce ɗakin da Gimbiya ke ciki Naja'atu ma ta bani darduma na shimfiɗa na ta da salla.
Na kai raka'a ta biyu na miƙe a raka'a ta uku Yallaɓai ya shigo na ji muryan Mutaƙka da na Uncle Abba sai na wasu mazan amman tun da ina salla ba zan iya sanin su ba. Ina ji Mutaƙka na yi ma Gimbiya sallama daman kuma Yallaɓai ya ce bayan la'asar za mu tafi.
Daga nan sai kowa ya fita har Naja'atu aka bar Yallaɓai da Gimbiya. Ban sani ba ko shi ya gane ni ce ke sallah ko kuma bai gane ni ba amman ita ta san nice na ke yin salla a wajen
Suna ta gefen damana ne, ina kai sujjadar ƙarshe na ga Yallaɓai ya duƙa a gaban Gimbiya yana mai kiran ta da sunan da ya saba kiran ta dashi.
"Daughter."
Sai ta ɗago ta kalle shi a marairaice kafin ta amsa murya shaƙe.
"Daddy."
Dai dai lokacin da na ce" Assalamu alakum waramatullah
Hagu da dama da kuma ƙarfi, ina juyawa bangaren dama muka haɗa ido da Yallaɓai har da ita Gimbiyan
Ina salla ne amman kirjina na wani irin suya ne. Kallon yadda ya gurfana na yi a gaban Gimbiya har gwiwar kafarsa na gugan kafafunta da ke tankwashe sai kawai na kauda kaina na miƙe ina na ɗe darduman da na yi sallah da shi.
Ko kunya ya ji da ya ganni sai ya yi saurin matsawa baya ya na mai miƙewa tsaye.
"Da man ke ce ke salla?
Ya faÉ—a ya na kallona sai kawai na kalle shi kafin na ce" E"
Sannan na ijiye darduman a saman hannun kujera kafin na kama hanyar barin É—akin ina faÉ—in" Ku cigaba da mganar ku."
Ban san ko sun bi ni da kallo ba saboda ni ban juyawa ba har na fice daga É—akin.
Ba dota ba doya ba daddy ba Dada. Tun daga lokacin na rage fara'a har Hauwa sai da ta tambayeni ko lafiya na ce lafiya lau kila Yallaɓai ya tsargu ne ya sa bai daɗe a ɗakin ba ya fito ya leƙo nan ya na cewa mu fito za mu biya gidan su Nene kafin mu wuce.
Sallama muka yi musu, sannan mun kara shiga wajen Gimbiya muka ƙara yi mata Allah ya jikan rai ya ba da danganta ta amsa a hankali. Daganan sai gidan su Nene muka je muka gaida Innayi ko minti talatin ba mu yi ba muka kamo hanyar gida. A cikin zuciya na ga to damuwar ta mace ce, namiji fa sunan shi Namiji ba abin da ba zai yi ba sai kawai na watsar da abin na ɗan saki fuska Yallabai daman suna hira da Mutaƙƙa ya nna ta faman sako ni a ciki da a shake na ke amsa masa sai daga baya na saki jiki muna ta hira. Sai da muka biya Gwammaja muka ɗau yara sannan muka kai su Hauwa gida muka wuce namu gidan
Yallaɓai dai kamar ya kama kan shi ni dai ƙala ban ce masa ba sai shi ne da za mu kwanta ya ɗauko mganar.
"Dazu Allah ban san ke ce ke sallah ba."
Na yi kamar ban ji sa ba sai ya ƙara cewa" Kin san da ya ke sai a hankali. Na shiga yi mata sallama na ke ƙoƙarin lallashinta ta riƙa cin abinci."
"Haka fa. Ai ka kyauta."
Daga nan na juya masa baya na ja bargo. Ban sani ba ko yabi ni da kallo amman ina da tabbacin ya yi haka. Bai takuramin ba amman ya raɓo ta bayana mun kwanta.
*****
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya. Wattani wajen biyu sun zo sun shuɗe kamar tafiyar iska. Har su Jidda sun yi jarabawa 3rd tearm sun yi hutu. Jidda Gidan Mimisco ta tafi hutu ita kuma Baby gidan Yaya Maimuna gida tsit daga ni sai Yallaɓai sai Saude da ke zuwa yi min aikace aikace.
Bangaren asibitina kuwa tuni na yi nisa a gwaje gwajen da ake yi minib wanda na yi na ƙarshe shi ne Pap smears ne kuma har na karɓi result ɗin wannan satin da ya wuce na kai ma Dr Aisha cikin ikon Allah ta ce mini shima ba wata matsala.
In da na ke ɗan samu salama kenan kuma ta na bani hop ɗin duk da saura gwaje gwajen ba mu gama ba, ba ni da watsala lokaci ne bai yi ba in ya yi zan ƙara haihuwa.
Zuwa lokacin shiryen shiryen bikin Yaya Usman ake yi domin cikin watan da za mu shiga kafin azumi za a yi bikin na shi. Anan Gwammaja za a yi bikin tunda ɗaurin auran ma a kaduna ne. Yadda Yallaɓai ya faɗa mini gabaɗaya da Anty Zabba da yaran za su zo kamo sai an gama biki za su koma fatakot har da amaryan.
Har anko ƙannensa su Nasara sun fidda Atamfa ce mu ma duk mazajen mu sun yi mana mu da yara. Aure dai ya tabbata ba fashi amarya na dawowa daga london aka tsaida date ɗin biki.
A kuma tsuƙin ne na kirga za mu yi 15 years Anniversery da aure ni da Yallaɓai zuwa bayan sallan azumi da kwana shidda kenan. Ni kaɗai a raina na shirya za mu yi walima tun da tun na 10years ba mu kara ba lokacin Baby ta cika shekara ɗaya sai muka haɗe da birthady ɗin ta.
Ba mu kara yi ba sai wanman karon na ke fatan mu sake yi. Daman a gida ne daga ni sai shi sai yara muka yanka cake ɗin mu sha hotunan mu da ciye ciye washegari kuma Yallaɓai ya fita damu mu wajen wassani da sauran su. Tun tuni na so na yi masa mganar amman bai samun lokaci Alhamdulillah yana ta samu kwangila bayan gama gina gidan buredi a Rano dalilin haka ya samu kwangilan gina bayuka na wasu makaratun sakandiri a garin na Rano sai ya kasance zamansa a nan office ba sosai ba sai dai Musabahu ya zauna wani lokacin gidan bulo kuma daman sun ɗauki yara ma su kula da shi, shi dai Musabahu manaja ne kawai.
Abin da na fara lura da shi shi ne Gimbiya ta fara ƙoƙarin takura ma rayuwar aurena ta na daga can gidansu tana takaba.
Ni na san cewa Yallaɓai na zuwa ganinta tun da yana yawan zuwa Rano. Ban kuma taɓa nuna damuwata ba ko na nuna fuska ban ji daɗi. Sai dai na ga ba ta da hankali in ya dawo gida sai ta kira shi a waya ta ji wai yadda ya koma gida. Da safe kuma ta iya kiran sassafe tsirfa kala kala daga ta ce Anty Bahijja za ta ba da saƙo a kawo mata sai ta ce Nene sai ta ce Anty Maimuna wani lokacin ita ce ma za ta ce ya siya mata abu kaza ya taho mata dashi tsirfa kala kala ranar da bai je Rano ba ta riƙa kira kenan ta na korafin me ya sa bai zo ba? Abin da ke ba ni mamaki shi kuma sai ya na biye mata sau ɗaya na yi masa mgana da cewa wani lokacin ta na kiran shi a waya ba ta da abin faɗa sai kawai ya ce min abar tausayi ce kuma ga shi ta samu hawan jini dalilin rasuwar nan shi ya sa ba a son ana ɓata mata rai.
Na ga ƙoƙarin Yallaɓai da ya iya faɗa min haka amman kuma ta wanni fannin ban yi mamaki ba mun taɓa samun matsala da shi a baya tun ban haifi Baby ba akan Gimbiya muka yi faɗa da Yallaɓai na ce in son Gimbiya ya ke yi me ya sa ya aure ni bai aure ta ba saboda na ga bin binin ya yi yawa amman sai buɗe baki ya yi ya ce mini" In da bai haɗu da ni har Allah ya haɗa zukatanmu ba to ya ba ni tabbacin bashi da mata sai Saudatu."
Har Gimbiya ta yi aure ban daina fargaban wata rana zan ta shi na ga Yallaɓai ya auro min ita ba na huta da ta yi aure amman yanzu kam bayan ta zama bazawara ta sake dawo mini cikin rayuwata ta na yi min barazana.