← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 76

Sashe 64

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Rahila da Yaya Balki ne suka zo min biki domin ba zan saka Ma'u da ƙawarta a lissafina ba. Ni fa ban ma san ta zo ba sai da Yaya Balki ta ce kafin su fito sun yi waya ta ce musu ta na gidan tun ɗazu na ce ni kam ban san ta zo ba sai da suka ci abinci na raka su ɗakin Maman Farko suka yi mata Allah ya sanya alheri daganan muka shiga ɗakin Nene nan na ga abin mamaki Ma'u da ƙawarta shema'u filet ɗin abincin su cike da kaji da nama sannan suna tare da su Gimbiya da Anty Bahijja ana ta hira ana shewa.
  Tana ganin mu ta tsargu ni ko da gangan na kalleta kafin na ce" Su Ma'u manya maso bare kiƙi dangi. Kin zo amman ba ki iya nema na ba?
Sai ta fara kame kamen ta nemi ni ba ta ganni ba sai tana taɓe baki kafin na ce" Muna shashen su Jawahir tare da su Hauwa."
Nan dai muka gaisa ni dai na kai su ciki su ka gaida Nene da Hajiyar Tafida bayan mun fito na ga sun tsaya suna mgana da Ma'u da shirina na yi tafiya ta. Allah ya so mu ma Mimisco ta ce mu ɗiba komai saboda namu baƙin kuma daman ina nemanta saboda ba a diɓar mana na mazajen mu ba, mun yi waya da Yallaɓai duk da sun yi reception a can akwai bukatar mu ijiye musu abinci.

  Anty Maimuna na tare da baƙin ta dangin mijinta. Sulaihat na gani na ce ina Mimisco sai ta ce mini tana bangaren Hajiya iya sai na kalli Anty Bahijja ina faɗin.

" Anty Bahijja muna bukatar nama sannan da waina."

Kai tsaye ta ce" Duk wanda aka ba ku fa?
Nima kai tsayen na ce" To na mutane ne wannan, shi wannan da na ke magana na mazajen mu ne da suka tafi É—aurin aure ne na yi ma Mimisco ma mgana."
Sai gabaÉ—aya suka kalleni har da Gimbiya.
Sai Anty Bahijja ta riƙe baki tana faɗin" To ma su miji. Mu namu mazajen da suka tafi fa? Ba su da rai ne ?
Ina dariya na ce" Kowa na shi ya sani Anty Bahijja. Ba zan hanaki ki ijiye ma Baban Sulaihat ba. Amma ni kam sai na ijiye ma Yallaɓai duk abin da na ci."

Naja'atu ta buga guÉ—a kafin ta ce" Kin burgeni Anty Sadiya. Shi ya sa Kawu dai ya fara ajiyan tumbi."
Ina mata dariya na ce" Ai na iya kiwo ne."
Ta ce kwarai kam. Sai aka maida mganar dariya Anty Bahijja ta miƙe ta na faɗin.

"Muje mai Yallabai."

Ta faɗa tana riƙo hannuna sai aka kara saka dariya ni ko sai na rike ta muka fita daga falon muna tafe tana ce mini wai shi Yallaɓan nan ba zai ci abinci acan ba ne? Na marairai ce na ce zai ci amman akwai tafiya kar ya dawo ya na jin yunwa.

A can shashen Hajiya iya muka je ta diɓar min waina da naman na je na kawo kula ta saka mini tana ta min tsiya Mimisco ta kare min da cewa abin da na yi mai kyau ne mata da dama in ana sha'ani sai su manta da mazajen su.
  Ni dai na wuce na barsu ina zuwa na ce su Hauwa sun ci sun ƙoshi suna sakin tusa sun manta da mazajensu to ni na yunƙura na samo ma mazajen namu abinci sai suka fara min dariya nace su gode minibko na fasa ba su Munnira ne wajen gaba gaban gode mini.  Su Rahila da wuri suka tafi kafin mangariba Ma'u kam tana gidan tawagan masu ɗaurin aure da amarya suka dawo. A shashen Hajiya Iya aka safki amarya da tawaganta. Ana yin mamgariba na kira Yallaɓai na tambaye shi ko yana ina? Ya ce min suna cikin gida a ɗakin Musbahu da kaina na yi lulluɓi na kai masa abinci da ruwa da lemu na san daman shi da Tariq da Uncle Abba ne nama daman da yawa na diɓar musu sauran na bar ma su Munirra domin na ga su ba su damu da cikin mazajen su ba.

Yallaɓai sai da ya rumgumeni ya ba ni sumbata a baki kafin ya ce" Allah ga baiwarr ka nan Halima Allah ka jiɓanci lamuranta kamar yadda take jiblɓanta nawa."

Daman sun ce yunwa suke ji.  Suna ma shirin tashi su fita su je su ci abinci a cikin gari ne sai ga ni, Tariq dai ba baka sai kunni ya fara cin nama Uncle Abba kuma sai ya kalleni kafin ya ce" Sadiya na ce wai ba ki da yar ƙanwa ne a gida?
GabaÉ—aya suka saka masa dariya nima sai da na dara kafin na ce" Babu Uncle Abba kana so ne sai a duba maka a dangi?

Sai ya ɗau naman kaza ya saka a baki yana tauna kafin ya ce" Ina tunanin haka na gaji da wulaƙancin da yaran nan suke yi mini. Yusuf a gabana bai ji kunyar kama mace ba ina kawun sa."
  Yallaɓai na cin waina ya ce" Ba fa Mace ba. Matata na kama. Kawu kuma ai ban hana shi aure ba ko?. In ka ji haushi gobe a ɗaura ko Tariq?
Ya faɗa ya na kallonshi Tariq ya gyaɗa kai sannan ya ɗaga hannu Abba ya zungure shi da ƙafa yana faɗin" Shege sarkin cin abinci."

  Ni dai gajiya na yi na fita na bar su domin ba za su fasa ba sai dai idan ba su haɗu ba.
Farida dai na faɗa mata ba ta damuwa Tariq na tare da Yallaɓai. Su kuma su Hauwa suka ce wai na yi musu wayau na kwashe tsokoki na bar ma mazajensu kashi ina dariya na ce" To wai na hana ku diɓar musu ne da farko? Bana son son zuciya fa. Ku dai cigaba da zama."

  Ranar ma ban kwana ba gida na koma amman tare da Farida da Sameena su Munnira ma gida za ta koma ta kwanta Hauwa ce na ga tana shirin ƙara kwana na ce ta je gida ta kula da mijinta tun da ban ga abin da za ta yi ba in ta kwanan
Uncle Abba da Tariq Rano suka koma suka kwana Yallaɓai kan gida ya dawo su Farida a ɗakin su Jidda na sauke su da safe bayan mun karya mun yi wanka muka koma Gwammaja.
Sai a ranar muka shiga muka ga Amarya. Doguwa ce baka mai jiki. A shashen da muka zauna ajiya yau ma nan muka zauna da farko ba mu yi niyyar zuwa gidan su Anty Zabba ba sai da ta kira Munnira ta ce tun da mun zama yan amarya ta yafe mu shi ne yasa muka shirya bayan azahar muka tafi can anguwarsu ta Rijiyar zaƙi.

  Da muka ce ga in da zamu a gidan kafin mu tafi, sai da Anty Bahijja ta yi ƙorafin ne zai kai mu? Ita da Anty Zulaihat wai ai da gangan ta ki sauka anan a yi biki gabaɗaya Mimisco ta kashe bakin su da cewa" Ku bar su je yana da kyau haka a matsayin su na surukan gidan nan"
Dole suka yi shuru.  Mun je ma Anty Zabba biki da muka je har tana cewa ta yi fushi nima ta ce ko waya ban kira ba na bata hakuri.
Anty Zabba har ta É—an rame amman kuma ta yi gayunta tsab da ita itama ta yi taro gidansu cike da mutane yaran nata sai a ranar da za mu taho suka biyo mu zuwa gidan kakaninsu a daran kuma aka zagaya da amarya duka É—akunan gida mu ma aka tara mu aka yi mata bayanimmu É—aya bayan É—aya.

  Washegari litini da wuri Ango ya ɗau amaryansa da Rakiyan ƙannensa mata su Anty Nasara suka raka su gidan su Anty Zabba suka haɗa su suka yi musu nasiha daga nan sai filin jirgi suka ɗaga sai garin fatacol sai fatan Allah ya ba su zaman lafiya ya kaɗe fitina.
  Shikenan gida ya watse baƙi da nesa da na kusa zuwa talata duk sun koma gidajensu Gimbiya dai ta na nan amman na ji Hauwa na faɗin daga nan Abuja za ta wuce an kira su kan mganar rabon gado. Mganar aikin ta kuma Yallaɓai ya faɗa mini an dawo da ita nan office ɗin NGO da ke reshen Jihar kano. Amman sai ta dawo daga Abuja za ta fara zuwa aikin.
A lokacin da ya ke gaya minibsai da na tambaye shi.
"A wajen Nene za ta zauna kenan?
Sai ya gyaɗa min kai har yana ce min" Nene ma ta karɓe ta. Ta ce sai kuma aure zai raba su."

"Uhm!

  Kawai na ce a lokacin amman ban iya sake mgana ba.

Sai bayan bikin Yaya Usman na samu damar yi ma Yallaɓai tuni kan Anniversery ɗin mu ya ce wallahi ya manta gwara da na tuna mishi. To shima zai ba ni kyakyawan surpise a lokacin in sha Allahu ina ta murna ina cewa ko Hajji za ka biya mini? Ya ce Allah ya sa haka.

******
Chapter 64 · 0% Book details