← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 76

Sashe 50

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In kana da ƴa'ƴa mata koyon kitso ba zai zama wani abu mai wahala ba. Kuma daman ina da  mai kitson  tun ta can anguwan dakata da muka ta so bayan mun dawo nan tana zuwa gida ta yi mana ina biyanta ranar da kuma ba ta samu zuwa ba na kan kira Salisu ne ya zo ya ɗauki su Jidda ya kai su. wani lokacin in ta gama yi musu kitson yarta ke dawomin da su ranar da ba su samu zuwa ba na yi musu da kaina tun ban ƙware ba har ba ƙware kaɗan kaɗan.

  Da na so sai la'asar zan je gida amman sai Amina ta sake kirana tana faɗa mini duk yau Yaya Hamza da Yaya Auwal za su koma sai na yi tunanin na tafi bayan azahar.
Yallaɓai bai tashi ba sai da na gaji har wajen sha ɗaya saura bayan na wanke tiolet na jiƙo hannuna na zo na tura masa a cikin ƙirjinsa da sauri ya buɗe ido sai a cikin idanuwana.

Ɗan ɓata rai ya yi irin na masu barci ni kuma sai na yi masa mirmishi.

"Yallaɓai a tashi haka nan. Kalli fa rana ta yi."

Na faÉ—a ina buÉ—e masa labulen window É—in bedroom din. Ai sai ya kauda kai har ya na juyawa zai cigaba da kwanciya.

"Yallabai. Haba mana"

Na faɗa cikin yar shagwaɓa amman sai ƙara shigewa da kansa ya yi cikin bargo lokaci ɗaya cikin shaƙewar murya cike da barci ya ce.

"Sai azahar za ki tashe ni. Kin ji".

Ya faɗa ya wani ƙara sakin numfashi sai na saki baki kawai ina kallon shi na buɗe baki in yi mgana wayata dake kan dressing mirro ta ɗau kiɗa alamun kira sai na bar wajensa na isa wajen wayar.

"FaridaAisha."

Faridan Tariq ce. Haka na faɗa a fili kafin na juya ina kallon Yallaɓai lokaci ɗaya ina faɗin" Ka gani ko? Ƙila ma Tariq ke neman ka ka kama ka kashe waya kamar wanda ya kwana aikin gajiya."

Na san ya na jina amman bai yi motsi ba sai ni ce na taka zuwa gefen gado na zauna sannan na É—aga kiran

"Maman biyu."

Daga can bangaren ta ce"Matar injiniya."
Da fara'a muka gaisa sai ta ke ga ya min sun shigo garin ita da Tariq suna Gwammaja suna son ƙarisowa gidanmu amma an kira wayar Yallaɓan nawa a kashe

Da sauri na ce"Yau hutu ya ke ji tun da ya dawo sallar asuba ya kashe wayarsa. Amman ai yanzu yana jin mu. Za ku samu ƙariwan kuwa?

"E. Amman a tsaye gaskiya saboda daga nan sai kaduna in sha Allahu "

Ina buÉ—e baki kamar ta na ganina na ce"Kai. Yau kuma! Ba ku bari zuwa gobe?
Tana yar dariya ta ce"Mai gayya ne ya ce yau za mu tafi"
Ina dariya na ce"kuma an gama mgana ba."

Sallama muka yi ta ce suna tafe. Muna gama wayar na juya ina kallon Yallaɓai amman bai tashi ba sai na miƙe ina faɗin" Yallaɓai ga su Tariq nan da iyalansa don Allah ka tashi ka yi wanka ka ƙarya kafin su kariso"

Dakyar da soɗin goshi na samu Yallaɓai ya tashi. Hararan shi na yi lokacin da na ga ya miƙe ya na miƙa.

"Gajiyar duk ta mene ne?

Sai da ya sargafo hannayensa ta saman wuyana muna kallon juna kafin ya ce"  To kuma me ye na tambaya? Duk tsawon gajiyar da kika tara min ne na wannan watan na ke safkewa"
Ya ƙarishe yana ɗage mini gira. Ture hannun shi na yi daga kafaɗata na wuce ina faɗin" Ni ban ce ka tara min gajiya ba sai kai?

"To ke wani ƙokari kike yi ban da abin ki. Ni ke fa aikin."

Ya faÉ—a yana biyo bayana. Juyawa na yi muka haÉ—a ido kafin na yi masa wani kallo sai kawai ya fara dariya ni kuma sai na rausayar da kai lokaci É—aya ina faÉ—in"

"Au! Haka ka ce ko?

Na nuna shi da yatsa kafin na cigaba da faɗin" Kai nan har wani ƙokari gare ka? Ba domin ni ba Yallaɓai uhmm."

Na faÉ—a ina cije baki. Yana dariya ya ce" Sadiya ki ji tsoron Allah."
Na juya zan fita ina faɗin" Za mu haɗu ne anjuma zamu ga mai ƙokari da mara ƙokari "

Ta baya ya rumgumeni yana faÉ—in" Just a good morning Hug."

Dakyar na tura shi Tiolet ya yi wanka kafin ya fito na soya masa yar sauran doyan da ta rage sannan na dafa masa ruwan tea mai haɗin kayan shayi. Ƙananun kaya ya saka tunda yau ya na gida a saman dining na zauna har sai da ya gama karyawa.

"Yallaɓai daga yau in dafa sauran shinkafar nan komai namu ya ƙare na kayan abinci."

Na faÉ—a ina kokarin tattara kayan da ya yi amfani da shi.

"Kafin Anjuma É—in Allah zai kawo mafita. In sha Allahu."

"Allah ya sa."

Haka na amsa ina mai fita daga falon zuwa kitchen. Na leka su Saude na ga Baby tana hawaye ana mata tsifa daman ita akwai zafin kai ita dai Jidda har ta tsife nata.

Ina dariya na ce"Baby ki bari a yi tsifa an juma Babanki ya ce zai si yo miki ice cream kin ji?

Jin haka yasa ta washe baki. Sai na ce to a daina kuka in ta na son shan Ice cream. Fita na yi daga ɗakin na rufo musu kofa duk da na yi wanka ina bukatar na ƙara tun da tun safe ne.

Ina wanka su Farida suka iso domin na ji lokacin da Yallaɓai ya fita ya buɗe musu get Tariq ya shigo da motarsa shi ya sa a gurguje na gama wanka na fito na shirya na saka riga da sikat na wani material sai ga Yallaɓai ya shigo.

"Ke sun fa ce suna kan hanya ne."

"Ga ni nan zuwa Sorry."

Sai ya juya ya fita ya na faÉ—n" Ki taho musu da ruwa."
Sai na amsa da to. Mayafi na saka na rufe jikina sannan na biya ta kitchen na É—auko musu ruwan gora a fridge da kofuna guda biyu bayan na saka a faranti.

Ina shiga falon Farida ta zo ta tarbeni. Falon ya yi albarka Baby  ta ga yan biyu  sai wasa suke yi, ƙila babansu ya kira su su gaida baban na su, Jidda ba ta falon tabbacin ta koma ciki.

"Sannun ku da zuwa."

Na faɗa ina sauke ruwan saman center table ɗin da ke gaban Yallaɓai da Tariq.

"Yauwa Sadiyar Yallaɓai. Ai ina nan ina masa tsiyan yau ko ba ya so mu ganki ne ya ɓoye ki?

Ina dariya na zauna a kujeran kusa da Farida.

"Haba dai ko É—aya. Ina wanka ne lokacin da kuka shigo."

Tariq ya jinjina kai kafin ya ce" yan hutu. Shi ma ai yanzu ya ke faÉ—a mini bai daÉ—e da tashi barci ba."

"Shi ne É—an hutu. Amman ni tun asuba ban koma ba."

Farida na hararan mijinta ta ce" Shima É—in ya na fin haka ma yana barci."

Yallaɓai ya ce" to daman mana. Ni da suka raina ne suka saka mini ido shi da kawunsa Abba."

Tariq na dariya ya ce" Tafida yarinyar  nan fa ta kirani. Ni dai kawun ka ya kusa kashe min aure. Madam fa ta ƙi yarda da rantsuwata shi ya sa na matsa mu zo ga ka ga Sadiya ƙila tafi yarda da mganar ku."

Ina dariya Yallaɓai na dariya Farida ce ta haɗe rai kafin ta ce" To na sani ko sabuwar budurwa ya yi. Kira kan kira"
Ina dariya ne amman ina auna wawancin Shema'u kina mace ki zama mai arha haka! Amman tuna wacece ita sai ban yi mamaki ba.

"Maman biyu kar ki yarda. Tabbas ni ma kwanaki nan ban gane masa ba duk yadda aka yi ya fara neman aure a boye."
Yallaɓai ya faɗa ya na haɗe ai sai Tariq ya kasa magana amman ya buɗe baki.

"Uhm. To Allah ya ba shi sa'a."

Farida ta faɗa kai tsaye ganin ta ɗan shaka sai na karɓi mganar ina faɗin" ƙyale Yallabai.'
Nan na faÉ—a mata abin da ya faru a jiya duk da ta na nuna ba ta damu ni na san ta damu.

"Ku kam ba abokan rufin asiri ba ne. Daga kai har tazurin kawun ka."

Tariq ya faÉ—a yana ture hannun Yusuf dake saman kafaÉ—ansa.
Farida na dariya tana bamu labarin sun je gaida innayi sun haÉ—u da Uncle Abba shima dai tuburewa ya yi da bai san zencen ba shima Yusuf ga abin da ya ce.

"Ai gaskiya ne. Mu ba mu san yadda aka haihu a ragaya  ba."

Yallaɓai ya faɗa yana dariya sai Tariq ya miƙe ya na fadin" Madam lokacin mu ya ƙare anan fa."
Itama sai ta miƙe tana rataya jakarta.
Dukkanmu sai muka miƙe gabaɗaya ina faɗin daga zuwa sai tafiya.

"To ai zuwan daman na a gaisa ne. Muna nan muna jiran ku ke da Yallaban na ki dai."

"In sha Allahu."

Na faÉ—a, muka bi su har waje ina yi ma yan biyu wasa. Kamar na sani na sako yar dubu É—aya daga É—aki shi na bama yaran ganin Farida ta zo ma da su Jidda bickit mai yawa.

Sun shiga mota ina bangaren Farida ina yi mata sallama. Yallaɓai kuma suna bakin motar shi da Tariq suna mgana.

"Man sai yaushe kenan?

Tariq ya buɗe mota ya shiga lokaci ɗaya ya na faɗin" Ai ni ƙila sai ranar da tuzurin kawun ka ya samu matar aure in za mu je tambaya sai na shigo."

Dariya suka yi har suna tafawa.

Ni ko sai na ce" Kawun ku ke ma haka? To ai ba ku za ku yi masa tambaya ba."

Tariq na dariyan mugunta ya ce" har auran ma za mu karɓa masa. Gaya min su wa za su je? To iyayen duk sun tsufa sun kare mu ɗin dai mune rufin asirin sa. Tafida ka bar gemun ka ya taru nima haka saboda na ga kamar kawun na ka ya fara maganar aure. Ko wani lokaci zai iya neman mu."

Dariyan su suka sha suna tafawa nima ni da Farida muna ta É—an dariya.

"Sai mun yi waya. Allah ya kiyaye hanya."
Chapter 50 · 0% Book details