Sashe 32
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
  Na yi wucewata na barsa nan tsaye sai ya biyo ni yana dafani kamar irin yadda ƙawaye ko abokai suke yi
"Ba yanzu ba. Sai na zama mai kuɗi lokacin kin zama Gwaggo sai na auro yar shilla mu ƙarishe rayuwarmu tare ko?
Da gwiwan hannuna na tokare masa ciki ya yi gefe yana dafe cikinsa fita na yi daga falo ina mai buga masa ƙofa. Bai biyo ni ba sai da ya tsaya ya kashe kayan wuta gabaɗaya ni daman ɗakin yara kawai na leka na ga sun yi barci sun bar wuta akunne Jidda ta bar littafanta nan ƙasa barci ya ɗauke ta. Ta shin ta na yi ta koma saman gado ni kuma sai na kwashe littafanta na ɗora mata saman drower ɗin su na tashi Baby ta je tiolet ta yi fitsari sannan ta dawo na kwantar da ita na sake tofa musu addu'a na kashe musu wuta na rufo ƙofar ina fitowa muka haɗe da Yallaɓai na dauƙe kai na ƙarisa wajen makashin wuta na kashe duhu ya bayyana.
Na ji takunsa ta baya na ban anƙara ba na ga ya ɗagani sama yana nishi nishi. Wuntsila kafa na fara ina faɗin" Ni ka sauke ni"
 Na faɗa ina tura masa baki, shi kuma ya na faɗin" An ki ɗin" Wuntsila kafa na yi da sauri muka yi baya kamar zamu faɗi shi ya sa ya sake ni yana dafa bango. Dariya na saka masa saboda akwai duhu har bayansa na bige bango.
"Wassh.."
Haka ya faÉ—a, ni kuma sai na kwashi gudu ina jin sa ya na faÉ—in" Sadiya ki tsaya anan wajen."
Ƙofa na buɗe na gudu bedroom ɗin mu ina faɗin" In kana da karfi ka kamani.".
 Ina shiga na kashe hasken ɗakin duhu ya bayyana ya na shigowa ya fara kiran sunana ni kuma ina danne dariyata.
"Yarinya in na kama ki za ki sha wuya fa."
Motsina ya ji ya fara laluɓata ina gudu muna zagayen gado daga karshe mune har saman gado. A ƙarshe dai Yallaɓai ya yi nasaran kamani ina ta dariya gabaɗayanmu muka baje kan gado muna sauke numfashi. Muna kuma kallon juna acikin duhun ɗaki ni ce na ganganra na hau jikinsa na rike masa duka hannuwansa biyu na duka ina sumbatar bakinsa. Shima ya na tayani daga karshe. Da ya ke ya fini karfi tuni ya ƙarbi ragamar lamarin ya mirgina da ni na dawo ƙasan sa shi kuma ya kama ni a hannu tuni muka lula cikin irin ta mu kyakyawan duniya ta ma'aurata irin mu masu marmarin juna da muradi a kullum.
 Â
*****
Washegari ta kama jumma'a ne. Yara sun tafi makaranta Yallaɓai kuma an kira shi ya fita office tun safe sai ni kaɗai a gida. Tara na safe Saude ta zo yau gyaran kitchen na ke jin yi sai na ce ma Saude ta gyara sauran ɗaku nan ni kuma sai na gyara kitchen. Ina can ina gyaran wayata na ɗaki ana ta kira ban sani ba.
Da ya ke Saude iyakarta gyaran falon farko da na biyu sai É—akin yara da kitchen sai wanke tiolet ni na ke gyara É—aki na da kaina sai haraban gidan bayan kwana biyu ko uku haka.
Ni na ce ta shiga É—akin da na ke sauke baki da ke kallon Bedroom É—ina ta gyara mini sai ta ji kamar ana ta kiran wayata sai ta ruga kitchen ta na cewa" Anty na ji kamar ana kiran wayarki a É—akin ki."
Sai na sauke Towel din da nake goge gogen na nufi cikin ɗakina sanye na ke da riga doguwa amman iyakarta gwiwata da kaɗan kwalliyar safen da na yi ma Yallaɓai ne kafin ya fita.
Ina zuwa na É—au wayata da ke saman gado na yi mamakin ganin kiran Ya Auwal har sau uku shi da kira É—aya ya ke yi shi da Yaya Hamza in kin zo kin ganni sai ki kira su daga baya ganin kiran sa har uku sai na ji tsoro ina shirin bin bayan kiran shi sai kuma ga kiran shi ya sake shigowa da hanzarin na É—aga.
 "Yaya Auwal"
Haka na faÉ—a cikin fargaba daga can bangaren da sauri na ji ya ce"Sadiya kina asibitin ne? Ya jikin Alhajinmu na mu?
Cikin mamaki da rawan baki na ce" Wani asibiti ku. Kuma? Alhajinmu ba shi da lafiya ne?
Cikin mamaki ya ce"Ba ki sani ba! Dazun nan Yaya Abubakar ya kirani ya ce Gwaggo ta kira shi a ruÉ—e Alhajinmu ya faÉ—i. To mun sake mgana ya ce ga shi sun isa asibitin mun rabu kan zai sake kirana amman shuru kuma na yi ta neman layin sa ban samu ba."
Cikin tashin hankali na ce"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Wallahi ban sani ba. Ba wanda ya kirani Ya Auwal."
"To ki yi maza ki shirya. Ki kira ki wayar Gwaggo ki ji asibitin da suke kin ji ko?
Sai na amsa masa shima ya ce daman suna shirin tahowa ne da ya bari sai gobe asabar amman tunda ga wannan matsalan suna nan tafe in sha Allahu.
Muna gama mgana hankalina tashe na kira wayar Gwaggo ba ta É—auka ba sai na kira ta Yaya Abubakar amman ba ta shiga ba sai na kira Rahila ita na sameta abin mamaki suna asibitin tare da Ya Muntari shi ta ba ma wayar ma ya faÉ—a min asibitin da suke.
Hankalina duk ya tashi Alhajinmu na da hawan jini amman ya daɗe bai tashin masa ba sama da shekaru biyar. Bayan rasuwan Mama ne ya kamu da hawan jinin. A gaggauce na yi wanka na shirya na kira Yallaɓai ina faɗa masa ya ce gashi a hanyar Rano amman zai dawo da wuri mu haɗu a asibitin. Saude na bar ma gidan na ce ta dafa musu sauran taliyan da ta rage ita da su Jidda. Ta kuma tsare min gida har in dawo Alhajinmu ke asibiti ba lafiya.
Cikin yar damuwa ta ce" Sai kin dawo Anty. Allah ya bashi lafiya" na amsa mata da Amin tsabar sauri sai da na fita na tuna jakar da na ɗauka ba kuɗi a ciki sai da na koma na sauya wata jakar fitar ta sauri ce kayan jikina doguwar rigar atamfa ce sai na saka dogon hijabi Jalbab. Adaidaita na tara zuwa asibitin na kuɗi ne ban ƙara razana ba sai da na kira Rahila ta ce suna Emergency a firgice na tambaya aka kwanta ta mini
Duk da ina cikin firgici na yi mamakin ganin kaf Æ´an gidanmu a wajen kowacce da mijinta har da Ma'u Alhajinta da su ake shiga ana fita. Yaya Aina ce kawai ba mijinta a wajen amman har da Mijin Yaya Balki da na Yaya Murja. Yaya Abubakar da zaituna suna wajen. Ga Rahila ga Ya Muntari.
A ƴan ɗakin mu ba kowa tunda Amina na kaduna ƙila ba ta sani ba ni ce kuma a cikin su ba wanda ya kirani amman sun iya kiran Ma'u saboda tsabar munafunci.
  Raina ya ɓaci da haushi shi ya sa daga su har mazajen na su ba wanda na ce ma sannu. Ina ji Rahila na kiran sunana na wuce zuwa in da Gwaggo ke zaune na duka ina gaisheta ta amsa min cikin kulawa da casabaha a hannunta.
"Ya jikin Alhajinmu Gwaggo?
Kai tsaye ta ce" Da sauƙi sun ce jininsa ne ya yi sama sosai nunfashin dakyar ya ke fita amman sun saka masa Oxygen yanzu ba daɗewa."
Ido na zaro ina faÉ—in" Innalillahi."
Sai tadafa kafaÉ—ata kafin ta ce"Ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu Alhaji zai tashi."
 Sai na jinjina mata kai ina maida kwallar da ta kawo mini mutuwar Mama kawai na ke tunawa.
"Gwaggo shi ne ba a samu wanda zai kirani ya faÉ—a,mini ba? Yanzu É—in ma ba domin Yaya Auwal ba da ba zan sani ba kenan?
Cikin lallashi da damuwa ta ce" Ki yi hakuri hankula a tashe suke. Abubakar kawai na kiran suma yan'uwan na ki ki yi musu usuri sun shiga É—imuwa"
Sai ban ce komai ba amman a raina na ce a dimuwan aka kira wanda ake so.
 Ba bari a shiga in da Alhajinmu ya ke Yaya Abubakar ne kaɗai da su Ya Muntari ke zirga zirga. Zama na yi kusa da Gwaggo ba wacce ma na kallah balle in yi mata sannu har Yaya Abubakar ban gaisar ba sabida ya bani haushi har da ya ganni ya na ce min" Ke sai yanzu kika iso?
Cikin gatse na ce" E. Sai yanzu aka faÉ—a mini"
Hankalinsa ya yi can bai ma jini ba Rahila ce ta zo ta zauna kusa da ni muka gaisa
Yadda ta ga na haÉ—e rai ne ya sa ba ta jani da magana ba.
"Hala Yallabai baya nan ne?
Kai tsaye na ce"Lokacin da na ji labarin abin da ke faruwa ya fita"
Sai ta yi shuru kafin can ta ce"Ki yi hankuri ni kaina hankalina ya tashi na manta da kiran ki."
Wani kallo na yi mata amman ban iya mgana ba.
Muna nan zaune jugum jugun har wajen azahar sai da aka cire ma Alhajimmu iskar Numfashi tun da sun ce numfashinsa ya daidai ta. Sannan suka maida shi ɗaki na musamman da Mijin Ma'u ya biya duk na ji Yaya Abubakar na faɗin Yaya Hamza ya turo kuɗi shi da Yaya Auwal amman kuma mijin Ma'u ya biya komai. Ina kallo suna ta yi masa godiya su Yaya Murja har tana faɗin" Allah ya saka masa da alheri ba domin alherin Ma'u a gare shi ba yaushe har zai riƙa yi mana Hidima haka? Ma'u ƙi kara yi masa godiya kin ji ko"
Sai ta amsa da toh kawai. Ban yi wani mamaki ba sanin halin su balle Yaya Murja akwai son abin duniya ita kuma Ma'u in ta fahimceka ta san yadda za ta riƙe sosai.