← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 76

Sashe 24

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai na gyaÉ—a mata kai kafin na ce"E. Kuma in na sha jinin na tsayawa gaskiya."

Sai ta jinjina min kai, ta É—an daÉ—e tana rubutu kafin ta É—ago ta na kiran sunana.

"Miss Sadiya."

Na amsa mata da Mah.

"Da kika fara zuwa ganin likita bayan kin fuskanci canje canje a jikin ki, an faÉ—a miki kin samu Secondary Infertility ne?

  Sai na gyaɗa kaina, ba ta damu ba ta cigaba da faɗin" Daman in kuka zo za ku yi planining, ana yi muku bayanin cewa akwai disadventage da advantage na yin shi ko? Kuma sai da amincewar miji da mata ko?

Sai na amsa mata da Yes.

Sai ta ƙara kiran sunana.

"Miss Sadiya."

Sai na amsa mata.

"Me ya sa kika zaɓi ki zo wannan asibitin? Na ga a fayel ɗinki ya nuna daga kano kike? Me ya sa ba ki tsaya a asibitin Aminu kano ba?

Kai tsaye na ce"E. Daman zaɓi biyu a ka bani ko can ɗin ko nan ɗin. Na ji hankalina ya fi kwanciya da nan ɗin ne."

  Sai ta jinjina kai kafin ta ɗago ta na kallona lokaci ɗaya kafin ta ce" Za ki iya jin haka. Amman a matsayina ta likita zan iya ba ki wata ƴar shawara?

Sai na gyaɗa mata kai. Ba ta damu ba ta cigaba da faɗin" Zai zame miki wahala a ce duk wata ki rika tasowa daga kano zuwa Zariya ganin likita. Kar mu fara saka maganar kashe kuɗe da walwalahu mu fara duba yanayin tsaron ƙasarmu da ya ke ƙara tabarɓarewa."

  Ba ta damu da na yi mgana ba ta sake kallona kafin ta ce" Zan yi transfer ɗin ki zuwa Aminu kano.  Zan haɗa ki da wata consultan Dr Aisha Bukar ita za ki cigaba da gani a kan matsalan ki. Karki damu duk ƙwarewarmu a nan suma acan akwai ƙwararru kuma duk ɗaya ne abin da za mu yi miki a nan a can ma shi ɗin za su yi miki."

  Na yi shuru ina tunanin maganarta. Kuma gaskiya ts faɗa. Ban yi tunanin haka ba Yallaɓai kuma bai yi magana ba saboda ya ga nan ɗin na ke son zuwa.

"Miss Sadiya ta amince na yi mata Transfer zuwa Aminu kano?

Ajiyar zuciya na sauke kafin na ce"Shike nan."

Mirmishi ta yi kafin ta ɗauki wayarta da ke kan Tebur ta danna. Zuwa can ta  saka ta a speaker ta ɗora saman tebur ɗin gabanta. Ita kuma sai ta cigaba da rubutu saman wata takardan da ta yaga daga wani littafi da ke gabanta.

"Hello. Dr Fatima."

Aka faÉ—a daga cikin wayar cikin harshen Turanci suka gaisa sannan ta ce"Dr Aisha zan yo miki transfer É—in wata patient ta bangarenki ce gynea. A kano ta ke ta zo ganin likita anan asibitin saboda nisa na ga gwara ta koma tana ganinki a can."

"Ohk.."

"Zan tura miki bayanan ta in brief ta email É—in ki. Yaushe za ki ba ta appoitment?

"Mu bar shi next week. Gobe zan je semina lagos sai after 3days zan dawo. Mu bar shi coming monday sai ta zo ta same ni a asibiti in sha Allahu."

"Thank You Dr. Aisha."

"Always Welcome Dr. Fatima.

Daga haka suka katse kiran, ni dai ina zaune bayan ta gama rubutun ta miƙa mini takardan da report ɗin na wancan asibitin sai da na karɓa sannan ta ce" Na yi mata mgana Consultan ce. Ranar monday za ki je Aminu kano ki ganta. Ki je mata da wannan takardan"

Na rusunar da kai ina yi mata godiya. Jinjina kai ta kafin ta ce"Miss Sadiya mun fito daga Jiha É—aya nima Granfa É—ina É—an Yashe ne. Wacce na haÉ—a ki da ita za ki samu dukkan abin da kike nema daga gare ta. Zan ba ki lambarta ana gobe za ki shiga asibitin ki kira ta, itama zan tura mata lambar ki in sha Allahu matsala. "

Sai na ji kamar ma na samu waraka daga matsalolina ina ta yi mata godiya. Ta karanto min lambarta na kwafe a waya na yi saving. Itama ta ce za ta tura mata lambata. Na fito daga office É—in ina yi mata godiya.

  "Thank You Doctor."

"My pleasure."

Ta faÉ—a tana mirmishi.

  Sai da na fito haraban asibitin sannan na kira Dr. Fadil na faɗa masa Dr Fatima ta sallame ni. Ya tambayeni ko ba matsala na? Sai na sanar dashi ta yi mini Transfer zuwa Aminu kano ta haɗa ni da wata consultan.
Shima ya nuna hakan ya yi dai dai saboda zirga zirga can zai fi sauƙi kuma duk ɗaya ne Shika da Aminu kano duk manyan asibitoci ne a afurka.
sallama na yi masa tare godiya ya ce bakomai.

  Na dawo gidan Yaya Hamza bayan sallar azahar ne, ina ma hanya ne azahar ɗin ta same ni. Itama kanta Khaleesat ɗin ta yi mamakin dawowata da wuri. Ina sauke jakar hannuna ina faɗin" Ke kam don ma na tsaya motar da na hau zuwa pizzet ba ta cika da wuri ba da tun ɗazu ina gida.."

  Khaleesat ta sake riƙe baki kafin ta ce"Ikon Allah. "
Sai da na kai zaune domin na ji kafafuwana sun gaji, sannan na cire mayafin jikina ina faɗin" Ke kam komai fa yanzu a Nigerian nan in kana da hanya ba ka ba baƙin ciki. Ƙarin abin ma likitan musulma ce kuma yar garin mu ce itama ƴar yashe, sosai ta karɓe ni, ni ta fara gani bayan ta iso da taimakon Dr Fadil."

"Ai fa. Na ga alama. Fatan dai an da ce? Ba wata matsala ko?

  Ta faɗa lokaci ɗaya ta na zama a gefena. Kora ma jawabin yadda mu ka yi na yi sannan na ƙarishe da faɗin" Ta ce a duka ɗaya ne. Ta yi Transfer ɗina zuwa Aminu kano ta haɗa ni da wata consultan ɗin"

"Allah ya sa a dace. Maganarta gaskiya ce. Ko don zirga zirga. Nima kuma sai da na yi tunanin haka ban dai yi mgana ba ne."

Na amsa mata ina hammar gajiya da yunwa kafin na ce" Ni idona ne ya rufe, gani na ke yi in na je nesa zan fi dacewa.".

Dariya ta yi min kafin ta ce.

"Ki yi sallah ga abinci nan na gama tun É—azu"

Da toh na amsa mata sai da na mike sannan na kwashi jakata da mayafina. Ita kuma sai ta juya ta nufi kitchen daman a ciki take lokacin da na shigo gidan.

"Ina Amna? Ban ji motsinta ba ne?

"Ta yi barci yanzu ba daÉ—ewa ba."

  Ina shiga ɗakin da na sauka ina faɗin" Wannan yarinyar kamar kasa? Sai barcin tsiya."
Ina jin dariya Khaleesat. Nima dariyan na yi nifa tun da aka haifeta duk lokacin da zan ganta tana barci ne, jiya ma da na zo ana gama bata nono sai barci da safe har na fita tana barci, yanzu ma haka.

  Tiolet na shiga na ɗauro alwala na zo na yi sallah. Na idar kenan ina addu'a na ji wayata a cikin jaka na ringing da sauri na miƙa hannu na ɗauko jakar daga saman gado kafin na fito da wayar ta tsinke. Ina dubawa sai na ga Yallaɓai ne kaina na dafe na manta shaf ban kira shi ba, ina dafe da kaina ya sake kirana ina ɗagawa na ce bayan na sassauta murya.

"Yallaɓai na."

  Daga can bangaren ya ce"Ba wani Yallaɓan ki, ina ta especting kiran ki shuru ni da na damu na kira. Ya ake ciki ne?
Ina ta jin hayaniya a wajen da ya ke, ban ma samu zarafin mgana ba na ji ya na sake faÉ—in" Ga Kawun ki nan ya damu sai cewa ya ke akira ki a ji me ake ciki"
Karya wuya na yi kamar ya na ganina kafin na ce"Ayya Afuwan Yallaɓai na. Ina shirin kiranka ne sai ga kiran ka"

"Na ji. Yanzu ya ake ciki?

Bayani na yi masa duk yadda muka yi da likitan na ƙarishe da faɗin" Ta ma haɗa ni da likitan rana ita yau in sha Allahu zan je na ganta a Aminu kano in sha Allahu.

Kai tsaye ya ce" Nima na yi miki wannan tunanin amman ganin kin dage sai can ɗin shi ya sa na ƙyale ki? Ba dai wata matsala ko?na amsa masa da ba matsala. Mun cigaba da tattaunawa har na ce ya ce ma kawu ya yi ma Dr Fadil Godiya ya yi min ƙokari.

"Injiniya muna buƙatar ka anan wajen fa"

Na ji ana faÉ—a daga cikin wayar.

"Yau ma kana Rano ne?

Sai ya amsa min da E. Sallama muka yi tunda ana ta aiki ne, muka rabu akan sai anjuma in mun sake yin waya. ina wayar ma Khaleesat ta yi ta leƙowa, na san maganar abinci ne, ina sauke wayar nan saman gado na zare hijabin jikina na fita falo. Ta na zaune akan kujeran Dinning ta na jirana tare muka ci abinci doya da miya muna ci muna hira bayan mun gama muka dawo falo, ta kunna kallo amman rabin kallon duk hirar duniya ce muke yi da ita.

  "Ni fa lamarin ki ya bani tsoro. Kin san Allah ina son nima na yi tsarin iyali na huta ko na shekara uku ne."
Chapter 24 · 0% Book details