Sashe 17
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Har goman dare muna gidan Nene mun shiga gida sha ɗaya na dare, a gajiye nake ko wanka ban yi ba na yi shirin kwanciya. Tunda na ci Tuwo a gidan Nene, dije ta yi shi da rana da miyar taushe. Na bar Yusuf na ta aiki a bisa laptop ɗinsa ni dai na yi barci na barshi ban san lokacin da ya gama ya zo bayana ya kwanta ba sai dai farkawa na yi kawai na ganshi kwance ni kuma duk na rufa masa kafafuna bawan Allah ya na shan bugun dare.
 Da safe da Inna Mariya ta kirani ƙanwar Mama ce tana gaya mini rasuwar, Yayar babansu Baaba Atu, Allah Sarki na ji mutuwarta ko kwanaki da muka je Gandun albasa mun shiga mun gaisheta ashe jinya ba na tashi ba ne. Ni na kira Amina na faɗa mata rasuwan ita tunda ta na nesa a kaduna take aure sai dai ni na shirya, kuma mu daman a gidanmu duk abin da ya faru a bangaren Gwaggo gabaɗaya ake zuwa haka bangaren Mama, tun Mama na da rai har ta rasu haka muke yi, Aminar ce ta shiga group ɗin gidanmu ta faɗa rasuwar sai na ji Anty Balki suna faɗi a haɗu a gida sai a tafi gabaɗaya a raina na kunsa sai dai mu haɗu a can. Yaya Auwal kawai na kira na sanar mawa ya ce Yanzu suka gama waya da Alhajinmu ya ce ya gashi ma a hanya zai tafi jana'iza mun gama wayar da cewa ya ce karshen wata zai shigo kanon in sha Allahu.
 Ina faɗa ma Yallaɓai rasuwan yace na shirya mu tafi Allah ya sa ya samu jana'iza. Tea kawai muka sha muka fita sai Gandun albasa, can ne asalin gidan su Mama, itama Baaba Atu ɗin da jinya ta yi tsanani ne, su kawu su ka ɗaukota zuwa gida anan aka yi jinyarta. Ta yi aure a kura mijinta ya rasu amman yayanta duka mata ne duk suna can, ko da muka je dai duk sun iso, tun da rasuwar ta asuba ce can muka iske Alhajinmu da Datti, har da Yaya Abubakar.
Â
Ni kuma sai na shiga cikin gida. Inna Mariya ce kaÉ—ai mace a yan'uwan Mama da suka rage uban su É—aya, sai su Kawu Nafi'u da suma uba suka haÉ—a, Inna Madiyana ta riga ma Mama rasuwa itace suke uwa É—aya uba É—aya, namijin ma tun kafin a haifemu ya rasu.
Duka iyayensu sun mutu, daman ko da muka taso ba mu san kakkaninmu na bangaren uwa ba, mun dai san ta bangaren Uba. Allah ya jiƙan ki Hajiya Dubu.
 Sai bayan an yi jana'iza an tafi kaita sannan sai ga su Yaya Balki, Yaya Aina, Yaya Murja. Sai Zaitunan Matar Yaya Abubakar. Sun shigo kenan ana gaggaisawa sai ga Ma'u itama ta iso, Gwaggo daman tare da su Alhajinmu suka zo.
Â
 Saboda gidan gaisuwa ne ya sa ba su yi min wata mgana ba mun dai gaisa. Sai can bayan an dawo daga kaita maza sun shigo sun yi gaisuwa masu tafiya sun tafi masu tsayawa suna ƙofar gida suna karban gaisuwa.
Yallaɓai mun yi sallama ya ce zai leka Office zuwa anjuma zai zo ya ɗaukeni, Alhaji mustpha ya zo, Alhajimu dai da Datti suna kofar gida Yaya Abubakar kuma ya tafi.
 A waya Yaya Auwal ya kirani na ba ma Inna Mariya ya yi mata gaisuwa ya ce ya yi ma su Kawu Nafi'u ta wayar Alhaji, wasu ƴan uwan namu ma na daɗe ban gansu ba sai nuna ni ake yi ana faɗin diyar Rukayya ce marigayiya, muna gidan har dare, Ma'u da la'asar ta tafi, mun gaisa da fara'a kamar yadda nima ta yi min. Anty Aina ma ta tafi ta ce za ta yi girki ita da Anty Balki, Anty Murja ce kawai sai ni da Gwaggo.
 Muna ɗakin matar Kawu Ali tare da su in da ake karɓan gaisuwa Yaya Murja ta kalleni bayan mun idar da sallar mangariba.
"Kin kyauta Sadiya har ni na kiraki kiƙi ɗauka na yi miki magana ta wasop nan ma shuru, ni fa yar gaskiya da gaskiya ce, daga kuma ƙin ta sai ɓata."
 Kallonta kawai na yi ban yi magana ba. Ta yi ta faɗa har ta na ce min"Ma'un da kika tsana ga ta nan da ita wajen gaisuwan nan in ba masoyinka ba waye zai yi maka haka? In ta biye ta naki ai da ba za ta zo ba."
Â
 Kamar in yi tsaki sai kuma dai na fasa na kyaleta, Gwaggo ce ta tsawatar mata ta ce ta bar maganar Alhaji ya riga ya kashe ta. Ni dai ƙala ban ce mata ba na fahimci gwara na riƙa yin shuru zai fi mini alheri. A lokacin Rahila ta kirani ta yi min gaisuwa bayan mun gama waya Anty Maimuna ta kirani ta ce Tafida ya ce an yi mana rasuwa. Su Jidda suna gidan Nene in mun taso mu biya mu ɗauke su. Ta yi min gaisuwa na tambayi jikin Halima ta ce da sauki suna saka ran gobe su sallamesu su maida ta gidanta.
 Sai Taran na dare muka bar gidan, nan na bar Gwaggo tare da Alhaji za su koma gida, Yaya Murja ma ta na nan mijinta ɗan gareji ne in ya taso zai biyo ya ɗauke ta.
Sai da muka biya Gwamnaja muka É—auko su Jidda, Baby ta makalemun tana faÉ—in"I miss u Umma."
Ina dariya na ce"Miss u more my Princess."
 Sun yi kitson su, sannan an siya musu sabbin lunch box da sock da sandal ɗin makaranta suna nuna min nace sun gode. Nene na falo zaune ta ji sauƙi ta yi min gaisuwa ta ce Maimuna ta faɗa mata da ta kawo su Jidda. Har Hajiya Iya sun yi min gaisuwa, sun ce in suka samu lokaci za su leƙa tunda Nene ba ta jin daɗi.
 Washegari Litini ma ban zauna ba. Amina ta iso daga kaduna ni kuma na tsaya a gida na yi girki sannan na tafi dashi. Ko da na je Ma'u ta yo abinci ta aiko da shi alale. Yaya Aina ma ta yo awara ta kawo hatta Gwaggo ta dafo abinci ta zo da shi, Rahila ma ta zo gaisuwa a ranar, haka muka yi ta jigilan zuwa har ranar uku, Hauwa ta zo mini gaisuwa ita da Mutaƙƙa. Muniran Nasir ta zo min gaisuwa, Anty Zabba'u kuma a waya muka yi magana tun da mijinta soja ne, Yaya Usman suna parthercourt ne su Yaya Hamza ma duk ta waya suka yi mana gaisuwa.
 Sai da aka yi uku na samu hutu a gida wannan zirga zirgan ya sa na ji duk jikina ba daɗi sannan sai na yi ta ganin juwwa ban kawo tunanin komai ba sai rashin zama waje ɗaya. An sallami Halima tana gidanta ni ban ma je ba, Amina ranar huɗu ta koma kaduna ni dai ban sake komawa ba sai ranar biyar daga nan sai ranar da za a yi bakwai. Da la'asar kuma na wuce gidan Halima domin na ƙara duba ta. Tun da tun bayan da ta koma gida ban samu zuwa ba.
Sun É—aga suna sai sati biyu sannan za a yi.
 Ban yi mamakin ganin Ma'u ba, saboda tana shiga dangin mijina da sunan ta na yi ma Anty Bahijja kara, ni kuma na san ba haka ba ne, tana ganina ta taso ta tare ni, na saki fara'an da ke faman fuskata. Wacce itama nata iya saman fuskarta ne. Tare da ƙawarta Shema'u suke, wacce haɗuwa ce ta tun muna makaranta. Shema'u na ganina ta tare ni da fara'a tana fadin" Hajiyar Injiniya Afuwan. Ban ɗauka maganata ta ranar za ta yi miki zafi ba. Don Allah ki yi hakuri."
Mirmishi na yi mata kafin na ce"Ayya rashin fahimta ne. Ya wuce."
 Ban zauna wajensu ba na shiga cikin ɗakin mejego muka gaisa, na ɗauki Baby, ina kallo ta na gefe ta ce"Anty Sadiya ya haƙuri? Yaya Tafida ya ce an yi miki rasuwa"
Sai na amsa mata, muna ɗan taba hira su Sulahait ne a gidan sai Hauwa da Jamila, Hauwa ce ke ta aiki, kallonta kawai na ke yi ina dariya a raina. Ba aikin da zan yi nima na gyara zama can falo kuma su Ma'u ne, ban son haɗa inuwa ɗaya da ita shi yasa ban fita ba.
 Ina zaune na ji marata ta karta daman tun jiya da daddare ciwon mara kaɗan kaɗan ya matsamin ba na tunanin al'ada tunda na yi shi a wannan watan. Ban taɓa tunanin in na shiga makewayi zan ga jini ba, jini sosai na gani na zubar mini hankalina ya tashi na wanke jikina na fito, da sauri na ce ma Halima zan ta fi, ko tsayawa ma in bi ta kanta tana cewa lafiya ta ganni cikin gaggawa?
 Na fita falo ina kiran wayar Yusuf ta shiga amman bai ɗauka ba, su Ma'u ba sa falon ƙila sun shiga sallah ne. Hankalina tashe na fita na samu abin hawa zuwa gida ina shiga gidan sai ga wayar Yallaɓai.
"Yallaɓai jini na gani, na bani al'adata ta dawo da mini wasa kamar baya."
Cikin damuwa ya ce"Topha. Yanzu kuma? To da yawa?
Ina cire mayafin jikina na ce"Ina jin sa yanzu haka yana bin kafata. "
"Subhanallah, ko za ki tura mini mganin da suke rubuta miki a asibiti lokacin nan? Na ga kina amfani da shi zubar jinin ya ke dakatawa."
 Kamar in yi kuka na ce"Na daɗe ban je na ga likita ba. Ba zai yuyi na sha mgani ba tare da na je an sake dubani an ga in da matsalar take ba. Ka taimaka mini ka sake kira mini Uncle Abba ina bukatar ganin likita a cikin satin nan."