← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 76

Sashe 67

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Na yi ƙoƙarin bayan na gama karanta wannan na fita amma sai zuciya ta rinjaye ni na srolling sama ina ganin saƙonnin da ta ke tura masa. Tun da aka fara azumi  ta ke tura masa saƙo da asuba a tashi a yi sahur sannan sai ta tura masa sakon barka da shan ruwa wani lokacin ya ba ta amsa wani lokacin ya yi shuru. Na duba saƙonin har wanda ta na Abuja lokacin da mijinta ya rasu. Wani saƙo da ya ba ni mamaki ya sa na ji kirjina sai da ya buga dam! Shine ta tura masa" Na yi kewarka Daddy yaushe za ka zo?
Shi kuma sai ya ba ta amsa da Gobe in sha Allahu.

  Kirjina ne na ji ya fara suya, har ina ganin duhu duhu da ya sa ban ƙara gaba ba na ijiye masa wayar a nan saman side drower ɗin da ya ke kwance. Kallonsa na ke yi ina mamakin Yallaɓai ashe shima ya iya munafuncin maza? Ashe jiya ba Nene ba ce ta tsaida shi ba ashe Gimbiya ce ta tsaida shi, bayan ta yi masa girki ya ci har ya na santi daga karshe har ya na ba ta tuƙwaici ni kuma ko oho. Wani ƙululin abu ya tokaremin a kirji da wani haushin Yallaɓai don Allah menene na ƙarya tsakani ga Allah? Sai kawai na juya da na so na fita ne ba zan tashe shi ba sai dai yau ya yi ɗaure amma sai na danne zuciyata da na yi wani tunani sai kawai na dawo na fara buga gefen gadon yau ko sunan shi ban kira ba. Sannan ban taɓa shi kamar yadda na saba ba. Bai da wani nauyin barci sai gashi ya buɗe idanuwansa da suka yi nauyi yana kallona sai kawai na juya ina faɗin.

"Ka tashi lokacin Sahur ya yi."

  Da ga haka na yi ficewata na bar shi a raina kuma na kudiri niyyar ko bai tashi ba na gama tashin shi. Daga yau sai ita wacce ke tashin sa sai ta cigaba da tashin shi. Ban da munafunci ta san ya na da mata amma wai ta ce duk asuba sai ta kira shi ya ta shi ya yi sahur? Ban taɓa lura ba saboda da na tashi na ke zuwa kitchen domin samar da abin buɗe baki ban taɓa cin karo da kiran nata ba sai yau.

  Tun da na zauna a wajen nan ban yi dariya ba. Tun kafin ya fito na ce ma Jidda ta zuba ma kanta da Baby sai ta kalleni kafin ta ce" Umma Abba fa? Wani kallo na yi mata kafin na ce" Kar ki ci ki tsaya jiran wani Abba."
Ita kanta na san ta yi mamaki domin sai da ta kalleni ni kuma na kauda kaina ina cin alalen da ma ɗumama sai ruwan tea wanda ban saka madara ba na ke sha dashi Baby dai sai cin ƙwanta ta ke yi ba ta damu ba Jidda kuma jikinta a sanyaye ta ke kurɓan tea ɗin ta ke sha tare da buredi ni kuma a raina ina ta roƙon Allah ya sa kar Yallaɓai ya tashi yau sai dai ya yi ɗaure sai dai addu'ata ba ta karɓu ba sai ga shi ya fito ya na sanye da jallabiya mai ruwan ƙasa Baby na ganin shi tana ƙoƙarin miƙewa ban san lokacin da na daka mata tsawa ba.

"Ke koma ki zauna ko na saɓa miki."

Haka na faɗa cikin zare mata ido. Daga Yallaɓai har Jidda da kallo suka bini, ita kuma sai ta kalleni ta ruɗe har ba ta san kafarta ya ture tea ɗin gabanta ba. Sai ga shi ya malale min a saman cafet kallon tea ɗin na yi yana gangarowa wani abu na tokaremin zuciya.
Ganin irin kallon da na ke yi ma Baby ne ya sa Jidda ta yi sauri miƙewa ta na faɗin" Ki yi hakuri Umma bari na gyara wajen."

  Yallaɓai na tsaye hannunsa harɗe a kirjinsa yana bin mu da kallo barin ma ni.  Kawai sai na yi kyafci ina kallon Baby da ta yi kamar za ta yi kuka na kaɗa kai kafin na ce" Lalle ko za ki ci ubanki Maimuna"
  Ta na jin abin da na ce ta barke min da kuka, tsawa na ƙara daka mata kafin na ce" Za ki yi min shuru ko sai na zo na tattaki a nan wajen?
  Na faɗa ina mata wani kallo, Sai kawai Yallaɓai ya kira ta sai ta kalleni ta kasa tashi shi kuma sai ya ce ta zo mana ya na kiranta ganin na kauda kai ne ya sa ta tashi ta nufe shi ta na kuka ta faɗa jikinsa ya rumgumeta yana faɗin" Shii Umma ce! Kyaleta kun kwance da ita ko?

  Kukan Baby ma ƙara harzuƙani ya ke yi amman ban yi mgana ba sannan ban ɗago kaina ba. Ina jin su yana ta lallashinta har sai da ta daina kuka sannan ya ce ta koma ɗaki ta kwanta ita kuma Jidda ta dawo da tsumma ta goge wajen tas ta gyara da na ce ta zauna ta ƙarishe shan tea ɗin ta sai ta ce mini ta ƙoshi. Uban gayyar kuma na tsaye ban kuma ce ya zauna ba sai da ya gaji sannan ya zauna a ƙasa kusa dani yana faɗin.

"Zuba min tea."

Da na so na ce ya kira Gimbiya sai kuma na fasa na haɗa masa tea ɗin na tura masa gabanshi da ƙwan da buredin ganin yadda na ƙi kallon shi ya sa cikin mamaki ya kira sunana.

"Sadiya."

Ban É—ago ba amma na amsa sai kawai na ji yana faÉ—in" Me ke faruwa ne?
Sai a lokacin na yi masa kallon ƙasa ƙasa kafin na ce" Me ka gani?
"Abubuwa da ya wa. Na ga kamar ranki yana ɓace ne me ya faru? Ke da yara ne?

Ya faɗa yana kallona nima sai a lokacin na kalle shi sai kawai na kauda kai kafin na yi mirmishi gefen baki na miƙe ina faɗin" Bakomai."
Abin ya bashi mamaki ganin na bar shi a falon na yi shigewata ciki kuma na san ya bi ni da kallo ban kuma ko waigo ba. Ban ƙara ganin Yallaɓai ba sai da ya zo daukan hula da carbi ina kan darduma ya ce mini ya tafi masallaci sai na gyaɗa masa kai kawai ba tare da na yi masa mgana ba.

Da safe ma haka na tashi gim da raina ko fara'a ban yi masa ba daga shi har ƴayan shi Jidda dai ta ga har da safen ban huce ba sai ta sameni a falo ina zaune domin ɗakin na bar ma Yallaɓai gabaɗaya.

"Umma ki yi hakuri don Allah."
Har da Baby ma kamar ta yi kuka ta ce" Ki yi hakuri Umma."
Sai suka ba ni tausayi laifin Ubansu ne ya shafe su sai na ɗan saki fuska na ce musu zo su wajena na haɗa su na rumgume na saki fuskata shi ya sa suka tafi makaranta suma sun warware. Amma shi kan Yallaɓai ya kasa gane kaina da ya matsamin sai na ce masa ban ji daɗi ne.

"To ko mu je asibiti ne? Me ke damun ki?

Kai tsaye na ce" Ba sai mun je ba. Ciwon kai ne kaÉ—an zai bari zuwa anjuma."

Kasa fita ya yi saboda yadda ya ga ina basar dashi ya san halina dole akwai wani abu da ya yi mini ne.

"Sadiya don Allah ki faÉ—a min me ya faru?

Na ce masa bakomai ba sau adadi amma bai yarda ba. Ganin ya damu sai na É—an saki raina saboda na ga ya na damuna da tambaya tun da ba gaya masa abin da ke danuna zan yi ba gwara na saki raina ko zai kyaleni da tambayoyin sa.
Na É—an sakin masa har muka zauna muna ta hira sai muka ganganro kan mganar kayan salla ya ce yana jiran cikon payment na aikin da suka yi a Rano ne a wannan sati sai a yi mganar kayan salla da É—inki da sauran su ya so ba zai fita ba ne sai kuma Musbahu ya kira shi ya ce wasu mutane sun zo suna jiran shi. Da zai fita sai na ce bari na shirya ya sauke ni Gwammaja na duba Nene, da gayya na faÉ—i haka saboda na ji me zai ce sai kuma bai ba ni kunya ba.

"Nene ta samu sauƙi fa. Ke da ba ki da lafiya, ki bari ko zuwa jibi tunda ba ki ji daɗin kema."

Kai tsaye na ce" Na ji sauƙi mu je ka sauke ni zan iya zuwa."
Na ɗauka zai ƙara mgana sai kuma ya yi shuru sai da muka jira Saude ta zo na bar mata gidan daman mun yi wanka mun shirya ni shadda na saka da farim mayafi shi kuma sai ya saka kananun kaya.
Da ya kai ni Gwammaja bai shiga ba saukeni kawai ya yi ya wuce office ni kuma na shiga ciki sai da na lelleƙa daƙunan su Hajiya iya muka gaisa sannan na ƙarisa ɗakin Nene na ganta garas da ita ita kaɗai ce a shashen ita ta ke faɗa mini Gimbiya ta leƙa wajen aiki.

Da na yi mata ya jiki ta na mirmishi ta ce" Tafida sai da ya ta so ki? ÆŠan zazzabi ne Gimbiya ta É—aga masa hankali tun jiya ina shan mganguna na warware."
Sai na yi mata fatan samun sauƙi bayan tambayan yara na ce suna makaranta mun ɗan taba hira da ita anan na yi azahar ina shirin tafiya sai ga Gimbiya ta dawo mun gaisa sama sama kamar yadda muka saba. Ta dai tambayi su jidda na ce suna makaranta.
Chapter 67 · 0% Book details