← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 76

Sashe 37

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Ina sassauta fushina kafin na ce" Ba zan yi ba Hauwa."
Kallona ta yi kafin ta ce" Kin tabbatar? Sai na gyaÉ—a mata kai sai ita kuma ta gyara zama ta cigaba da faÉ—in" Ita fa Ma'un ta ce haka aiko Anty Maimuna ta ce ba ki isa ba kin auri É—an dangi saboda haka in ke baki son haihuwa za su aura masa wacce za ta zo ta cika masa gida da Æ´a'Æ´a."
Idanuwana har sun tara ƙwallah zuciyata na zafi. Na kalli Hauwa kafin na ce" Ban yi mamaki ba. Tun zuwan Ma'u gidanmu na san ita din ba alheri ba ce. Na kuna san watan wata rana sai ta zame mini matsala da damuwa. Amman ta je Allah ya fita ni dai ban taɓa bin ta da sharri ba in tana tunanin abin da ya faru na fasa auranta da Yaya Hamza take rike da ni a cikin ranta ta makara har gobe ban yi nadama ba. Da na bari ta auri Yaya Hamza da tuni ta haɗa mana yaƙi a cikin gidanmu."

  Cikin mamaki Hauwa ta ce"To daman da jiƙaƙƙiya a tsakaninku?
Kai tsaye na É—aga kaina kafin na ce"Akwai kam. To sai aka yi yaya?
Hauwa ta cigaba da faɗin" Kawai sai wacce suka zo tare da kika ce ƙawarta ce ta na cewa shi ya sa kika yi tsarin iyali kenan ga shi ya ja za miki matsala kina son haihuwan kuma  ta ƙi samuwa. Nan take Anty Maimuna ta ce sai dai ke matsala ta ƙare a kan ki Tafida aure zai ƙara in sha Allahu."

  Mirmishi kawai na yi a cikin raina ina jin kamar in na ga Ma'u na shaƙe mata wuya. Sannan ido na idon shema'u wallahi tallahi sai ta raina kanta
Hauwa na faÉ—in wai na kwantar da hankalina ba su isa su saka Yaya Tafida ya yi aure ba.
Kallonta na yi kafin na ce" Sun isa mana tunda ƴan'uwan shi ne kuma suna gaba dashi. Ni bare ce ko yau ya sake ni gidanmu za ni su kuma ai ba shi da kamar su. Hauwa na rantse da Allah ba zan hana Yallaɓai ya ƙara aure ba, ya ƙara ta zo ta ci duk abinda suke tunanin ina ci ƴaƴa kuma ta tara masa duniya ni kuma biyun da Allah ya bani Allah ya raya min su."

Na faɗa ina ƙokarin maida kwallar da ta kawo min. Hauwa ta dafa kafaɗata ta na faɗin" Ki yi haƙuri. In sha Allahu ke ma za ki ƙara haihuwa. Ba kin je asibiti ya kuka yi da likitan?
Ina sauke numfashi na ce" Ta dawo da ni nan asibitin Aminu kano. Jibi zan fara zuwa in sha Allahu."

  Hauwa ta yi ta mini fatan dacewa na kalleta ina ƙaƙaro mirmishi.
"Na gode Hauwa."
Mun daɗe a wajen ta na ba ni baki na dai nuna mata bakomai ne amman ni kaɗai na san halin da zuciyata ta ke ciki. Amman na yi ƙoƙarin nuna ma Hauwa ba komai.
Saboda haka ne na kalle ta ina faɗin" Kin ji Yaya Usman zai ƙara aure?

  Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Na ji fa. Duk ranar sunan na ji ana tattaunawa. Shi kuma can bakin ƙannen shi na ji su Nasara suna ta zagin Anty Zabba wai so ta ke yi shi Yaya Usman ɗin ya zauna da ita kaɗai? Ko ya yi ma Ogan shi gaddama yaƙi karɓan auran. Sai zaginta suke yi suna faɗin kar Allah ya sa ta koma ɗin."
Cikin mamaki na ce"Ikon Allah. Mutane sai Allah yau kuma ita Anty Zabban suke zagi? To Maman farko ba ta yi mgana ba?

  Hauwa ta ce" Oh na ji dai kamar an ce ta kira shi a waya ta ce ya bar komai ya ke yi ya zo ta na son ganin shi " Sai na gyaɗa kai kafin na ce"Uhm. Allah dai ya kyauta.". Ta amsa da Amin ni na cigaba da faɗa mata yarda muka yi da Yallaɓai ya haƙinƙan ce. Ta na dariya ta ce" Ni ai ban yi ma Muttaƙa mgana ba. Kar ya ce ina son jin gulma amman na san shima bayan ɗan uwansa zai bi"

Dariya muka ɗan yi gabaɗayanmu. Muna wajen Munira ta kira waya ta. Ta na tambayata jikin Alhaji? Na ce da saúƙi a ina ta ji ta ce Nasir ya faɗa mata ya ce Tafida ya saka a group ɗin su na gida. Ta tambaye ni wani asibiti ne na faɗa mata sai ta ce min ƙila gobe ta shigo. Ina dariya na ce ma ai ga Hauwa ta zo tun ɗazu.

"Kai Hauwa sannu da É—anwaken zagaye ko ki kirani mu taho tare."

A speaker na saka Hauwa ta maida mata da amsa da cewa" Ke ni fa mijina ya kawo ni. Goben ki saka mijin ki kema ya kawo ki."
Munira na dariya tace" Au gorin miji da kin ga Habibi ba ya gari? To na san hanya kin ji ta Yallaɓai gobe ina nan tafe." Na ce Allah ya kawo ta lafiya daga nan muka yi sallama.
Ganin shidda har ta gota yasa Hauwa ta ce bari ta je ta yi ma su Gwaggo sallama ta wuce gida. Muna zuwa na ga Shema'u ta zo har ga Allah na so na daure amman na ƙasa ta kalleni ta na mini mirmishin munafunci irin na ƙawarta amman ni ta ga irin kallon da na yi mata. Ba domin muna asibiti ba ne. Kuma da ba uba na ne ta zo dubawa ba wallahi sai Shema'u ta raina kanta baƙar munafuka.

Tana min magana na yi kamar ban ji ba sai da Ma'un ta ce" Sadiya ba ki ji Shema na mgana ba ne. Ba ta gari ne É—azu ta dawo ta na zuwa, ke ta fara tambaya."
"Oh."
Haka kawai na ce na juyar da fuska ta domin na kasa iya ɓoye abin da ke zuciyata. Hauwa ta yi musu sallama kularta kuma aka juye abincin na riƙa mata har bakin asibiti ta samu adaidaita muka yi sallama.

Ba domin Yallaɓai ya kirani ya ce bayan mangariba suna tafe tare da su Uncle Abba  da har na gaji na ce tafiya ta gida zan yi. Rahila ma ta koma gida wai za ta yi abinci da ga ni sai Ma'u da kawarta Gwaggo ma Yaya Hamza ya maida ta gida kiri ƙiri Baaba taƙi bin ta wai ta je za ta zo. Can suka keɓe da yarta suna da ƙuskus ni ko dagani sai Yaya Balki itama mijinta take jira Zaituna kuma ta koma gida saboda yara a cikin raina ina fatan Allah ya sa a sallani Alhajinmu gobe na gaji da zaman asibitin nan

Waya ta na ɗauko na kunna Data na kwana biyu ban hau ba. Sai na ga an yi min mgana har da Yaya Maimuna ta na tambayan jikin Alhaji. Hindatu kuma ta ce ta kira waya ta ba ta samu ba.  Har da matar Muhammad kabir ma na ga maganarta. Kuma na ji daɗi na amsa su sama sama saboda an fara kiran sallar mangariba. Yaya Balki kawai na faɗa ma zan je sallah sai ta ce na tsaya mu tafi tare. Muna masallacin kafin mu fito Yallaɓai ya ce ga su sun iso asibitin.

A haraban wajen muka haÉ—u suka gaisa da Yaya Balki ta yi gaba ta bar mu ina gaisawa da Aminan mijina guda biyu. Uncle Abba da Tariq. Sun yi min ya mai jiki na ce da sauki muna gaba ni da Yallabai suna baya zuwa in da É—akin da Alhaji ya ke ciki.

"Me ya faru na ga kamar ranki a ɓace?

Yamutsa fuska na yi kafin na ce" Na gaji ina son na koma gida."
Sai ya kalleni da saurin na ce" Zan bika yanzu ko za ku je wani waje ne?
Kai ya girgiza kafin ya ce" A'a Gwammaja muka yi. Sai mu wuce taren su ma daga can za su wuce."

  Tun da Gwaggo ba ta nan da Baaba suka gaisa sai su Ma'u sannan na raka su ciki suka duba Alhajinmu ya ma tashi Baba Sani ya ƙariso zai taimaka masa ya yi alwala ya yi sallah. Ya ji daɗi ya na ta saka musu albarka da godiya ba dadewa suka yi masa sallama dukkansu kuma sun aje masa kuɗi ya na ta saka albarka.

"Alhajinmu Allah ya ƙara lafiya zan bi Yallaɓai zuwa gida sai gobe."

Alhaji ya jinjina kai kafin ya ce" Shi kenan mu kwana lafiya Dubu! A gaida min da Hauwa kuluta."
Na amsa masa ina mirmishi,  sun rigani yin gaba ina fitowa na ce ma Yaya Balki zan bi Yallaɓai sai gobe ta ce ai ya kamata na je gida tun safe fa. Daƙyar na iya yi ma Baaba sallama ta amsa sama sama.

"Sadiya Gwammaja za ku je?

Na juya ina kallonta Shema' u ce. Kamar na ce a' a sai kuma na ce mata eh.
Sai kawai na ji Ma'u na faÉ—in" To ki je mana Shema. Sadiya itama Gwammaja za ta je gidan kawunta."

  Juyawa kawai na yi ban ko yi mgana ba ina ji ta na yi ma Baaba sallama. Ina zuwa na ce ma Yallaɓai za mu rage ma kawar Ma'u hanya. Ya ce to ba matsala Ma'un ce ta rakota abin mamaki tana ganin motar su Tariq dabam sai kawai Ma'u ta kalli Yallaɓai ta na faɗin" Yallabai bari ta bi wancan motar ko ba waje ɗaya za ku je ba?

"Can za mu je gabaÉ—aya. Ta je ta shiga."

"Tariq..."

Ya ƙwalama sa kira ya na waya ne tsaye a bakin mota Uncle Abba ya riga ya shiga bangaren direba tunda motarsa ce.

''Ga ƙari na samo muku itama Gwammaja za ta je"
Ya faÉ—a ya na nuna Shema'u dake tsaye ita da Ma'u.

Sai ya ɗan ɗaga masa hannu alamun toh sai ya ce ta je ta shiga. Ni dai tuni na shige gaban mota na zauna Ma'u ta leƙo ta na fadin sai da safe na ce mu kwana lafiya.
Muna tafe amman acikin raina ina tunanin me ya sa shema'u ta ke son bin motar su Uncle Abba? Tabbas da wani abu a ƙasa.
Chapter 37 · 0% Book details