← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 76

Sashe 55

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan na samu Adaidaita zuwa cikin kasuwar Wambai akwai shagon da na ke siyan su bra da pant da kananun gajerun wanduna na yara nan na fara tsayawa na siya ma su Jidda pant da vest sai sikat na yara da ƙananun wanduna sai na siya ma Jidda da Baby dogayen wanduna baƙaƙe saboda makaranta. Har da safuna na siya musu farare da baƙake, nima na siya ma kaina pant da bra sannan na siya ma Marwa, daga nan na wuce shagon Musa mai kayan costimetic na siya irin su shampoo sai sabulin da su Jidda ke wanka, sannan na siya Veet da kayan wankin tiolet sai Moneyfresh saboda Mopping, na yi siyayya sosai na amfanin gidana har man kitso na siya mana. Saboda siyayya shago biyu ne kawai shi ya sa ban wani daɗe ba na dauki drop ɗin Adaidaita zuwa gida a ƙofar gida na ga Saude ta na jirana.

"Shi ne ba za ki kirani ba?! In ban dawo da wuri ba fa."

Kanta na ƙasa ta ce" Na kira ki ba ki ɗauka ba. Yanzu na zo fa daman."

Sai da ta ce ta kirani sannan na tuna wayata na can cikin jaka, key na saka na buÉ—e gidan Saude ta taya ni É—aukan kayan zuwa cikin gida duk na ji na gaji, ga cikina kamar an yi yasa kamar ban karya ba kafin na fita sai da na haÉ—a tea na sake sha sannan na dawo dai dai.

Sai da na natsu sannan na kira Farida na yi mata ban gajiya da yadda suka koma gida. Sannan sai na kira Amina ba ta É—auka ba sai na kira Khaleesat itama na yi mata ya hanya. Lailan ma Yaya Auwal mun yi mgana da ita.

Da rana tuwo na yi tun da shinkar tuwon kaɗai ya rage mana. Saude sai wajen uku na rana na bata kuɗin mota ta tafi gida, ni kaɗai a gidan jin an kira sallar la'asar sai na yi sallah sannan na kira Yallaɓai nan ya ke faɗa mini ya na Rano ya je duba aiki. Ni kuma daman na manta ne ban faɗa masa mganar a saka drinks ɗin yara na makaranta ba da kayan kamshin girki tun da shagon babba ne a can kasuwar Singer ba abin ba sa saidawa.

"Ai na tura masa na ce kuma ya saka duk abin da ya kamata."

Sai na ce ya dai sake kiran shi ya faÉ—a masa sai a manta wani abun sai ya ce to.

Sai shidda saura su Jidda su ka dawo, na so na yi wanki gajiya ya sa sai na ce bari na bari zuwa gobe sai na yi wankin.

Sai wajen tara na dare Yallaɓai ya dawo gidan yana tambaya ta ba a kawo kayan abinci ba? Na ce ba su kawo ba nan ta ke ya sake kiran shi manager ɗin sai ya ce a ba' a gama haɗa kayan ba ne sai zuwa da safe in sha Allahu.

Da wuri muka kwanta su Jidda daman ko da Yallaɓai ya dawo sun kwanta. Ina kwance a saman ƙirjinsa sai na kira sunan shi.

"Yallaɓai."

"Uhm"

"Ba ka ga Saloon É—ina ba ne"

"Na gani mana"
 
Ya faÉ—a ya na Æ´ar dariya duk da ba na ganin fuskar shi amman ina jin sautin dariyan shi.

Baki na tura kafin na ce" Shi ne ko ka ce ya yi kyau?

Hannunsa ya kai ya zare mini hulan kaina ya na mai tura hannun shi a cikin gashin sannan ya kai hancinsa ya shinshina ya kuma sumbata da baki kafin ya ce" Kina da gajen hakuri. So na ke yi daman na baki kyakyawan tuƙwaici."

Na ga ko kyakyawan tuƙwaici a daran nan sai da Yallaɓai ya saka ni jiƙa kai gabaɗaya kamshin Saloon ya bi ruwa ina tura baki na ce" Yallaɓai wannan tuƙwaicin naka ban yi maraba da shi ba."

Yana min dariya ya ce" Saboda mene?
Hararan shi kawai, na haye gado na shige cikin bargo ina tura baki, sai da ya tsane kanshi da danshin ruwa sannan ya hayo gadon ya na min dariya ni ko ko busar da kan ban samu na yi ba na dai tsane shi da towel.

Har da asuba sai da ya ƙara jiƙa mini kai, lamarin yallaɓai ya ishe ni har sai da na tsare shi ina masa tambayoyi.

"Yallaɓai ka faɗa mini gaskiya me kake sha ne a bayan ido na?

Na faÉ—a ina mai tsare sa da ido. Muna dining ne bayan mun gama karyawa su jidda sun tafi makaranta.

Wani kallo ya yi mini na bangane ba kafin ya ce" Kamar na me fa?
Ina haɗe rai na ce" Ko ka siya manpower ne ka fara sha a ɓoye ban sani ba?

Sai ya buɗe baki yana kallona kafin ya rufe ya na dariya. Ni ko ban yi dariya na tsare shi da ido ina faɗin" To Yallaɓai gwara na sani. Kana samu ɓarnan ruwa da yawa yanzu."

Haɓa ya riƙe kafin ya ce" Fisabillahi Sadiya kamar ni na yi lalacewan da sai na sha wani abu za mu yi barnan ruwa?

Kai na kaÉ—a kafin na ce" shi ne na ke tambaya."
Miƙewa ya yi a kaina sai da ya yi mika sannan ya sunkuya dai dai kunnina na dama kafin ya ce."

"Ke ba ki san muna girma  ba ne muna ƙara sanin daɗin abin da darajarsa ba"

Kallonsa na yi sai ya dage mini gira kafin na samu zarafin mgana ya sumbaci wuyana da sauri na ture shi na miƙe ina hararanshi.

"Miye haka?

Saboda na ga ya na ƙokarin riƙo ni kuma yana min wani kallon ƙasa ƙasa.

"Allah zan busar miki da gashin da kaina."
Ya faɗa ya na ƙokarin jawo ni ai da sauri na warce na fara zagayen dining ɗin ina faɗin" Bar shi kawai na yafe. Ina da hannu"
Shima sai ya fara bi na ya na faÉ—in" Kai Sadiya ta. Guduna kike yi yau kuma?

Ya faÉ—a har yana marairaicewa. Na san halin shi cikin sauri na ce" E wallahi yau na guje ka."
Dariya ya yi min ni ko na haɗe rai, haka muka dinga zagayen falon nan daga karshe na fice da gudu zuwa bedroom ɗin ina shiga kafin na rufe ƙofa ya cimmin karfi ba daya ba turani ya yi kan gado ya biyo bayana ya na faɗin" Duk wayon Amarya dai."
Ina ture shi ko gizau sai ya fara min cakulkuli ina ta dariya kamar zan mutu ina faɗin" Yallaɓai cikina don Allah ka bari."

Sai da ya ga numfashina na sama sannan ya kyaleni ya na faÉ—in" Gobe dai dole ki bari na yi shagalina tunda kin ga asibiti na bukatar samples."
Ko mgana ban yi mishi ba ina maida numfashi shima sai ya yi rigingine ya na nishi, ina ganin haka na lallaba na haye kanshi na fara masa cakulkuli da ƙarfi tun yana daurewa har ya fara dariya yana hantsila kafa, karshenta dai muka yi biji biji da gadon fililluka duk a kasa in ya yi min cakulkuli nima na yi masa daga haraba ma za a iya jiyo dariyan mu.
Har sai da muka gaji sannan muka koma muka kwanta muna hutawa.

Karfe sha É—aya Yallabai ya yi wanka ya fita ya ce zai je Gwammaja ne daga can zai ta fi office ya fita ba daÉ—ewa Saude ta zo ita na bari da gyaran gida na kwaso under É—in yallabai da nawa sai kayan barcin mu na fita can in da muke wanki na kafa kujera kayan ba su da yawa kuma ba su yi wani datti ba cikin lokaci na gama na shanya na saka abin matse shanya na kama dasu.

Bayana sai da ya riƙe ina gamawa na yi wanka da ruwa mai zafi, sannan na gyara bedroom ɗin da muka yi kaca kaca dashi ni da Yallaɓai. Ina da sauran fulawa sai na tura Saude kasuwar ƴan kaba ta siyo min kayan miya har da kabeji, ƙuli kuma daman ina da sauran shi sai dai bai da yawa ne. Da ya ke ina son gurasa to ina yi da kaina lokaci bayan lokaci.

Gurasa na yi mana. Ita kuma Saude ta niƙa min sauran kayan miyan a blander na saka su a cikin fridge bayan ta ci na saka mata guda uku a leda na ce ta tafi da shi gida. Da safen daman Yallaɓai ya yi mganar albashinta daman mu da kan mu mun kan je gidansu hannu da hannu mu ba ma mahaifiyarta haka tsarin ya ke,  sai na ce mata ƙila mu shigo zuwa dare.

Su Jidda suna dawowa su ka ga gurasa na yi suna ta tsallen murna. Kayan abinci ko sai bayan mangariba suka kawo mana. Yallaɓai baya nan dole su suka kwaso su zuwa cikin gida. Ma sha Allah na furta a raina komai an kawo har da su maclean da kayan maggi, ni da Jidda muka gyara komai a muhallinsa na Nene kuma na cire mata nata kayan Tea ne sai sabulan wanka da na wanki sai katan ɗin taliya da maracroni sai coouscous, tun da ta na so, shi ma saboda ya saba siya mata duk wata ne a matsayinsa na Namiji amman abincin gidan gabaɗaya yana Wuyan Yaya Usman ne gaskiya duk da sauran duk suna yi, matan ma kowacce tana iya bakin ƙokarinta. Kayan tea ɗin ma gida uku ne Nene da Hajiya Iya sai Maman farko.

Da Yallaɓai ya dawo sai na nuna masa ya kalleni kafin ya ce" Ba matsala dai ko?
Sai na rumgumeshi ina faɗin" Ba matsala mun gode Yallaɓai Allah ya ƙara buɗi da wadata."
Sai shima ya riƙe ni yana amswa da Amin Amin. Ni nasan na yi dacen miji, in dai Yallaɓai ya na dashi ba zan taɓa neman wani abu na rasa ba.
Chapter 55 · 0% Book details