← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 76

Sashe 27

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Kauda tunanin komai na yi a cikin raina na tashi na cire hijabin da na yi sallah. Gyaran ɗakin na fara duk bai da datti na san Yallaɓai na gyarawa. Sai da na share na gyara gado na goge komai na saka turaren wuta a ɗaƙin ya ɗau kamshi sannan na shiga wanka. Daga can na ɗauro alwala na fito bayan na shafa mai na yi kwalliyata kamar yadda na saba domin Tarban Yallaɓai na cikin zumuɗi da muradi mai girma. Da gaske ne na yi kewarsa sosai.

  Ina sallar isha'i Jidda ta shigo ta na faɗa mini Uncle Datti ya zo. Shi ya sa ina idarwar na ɗauko wayata zuwa falo ina sanye da riga da wando na wani material na saka mayafi abaya baƙi a saman kaina ina tashin kamshi. Kaina ba kitso har lokacin amman ina tunanin zuwa gobe zan je a wanke mini na yi kitso.

  Mun gaisa da Datti da tambayan su Gwaggo ya ce duk suna lafiya. Saude na ce ta zuba masa abinci. Bayan ta kawo masa na ce ta ja su Jidda ɗakin su ta zauna kafin Yallaɓai ya shigo.

Datti na cin abinci muna hira sama sama.

"Na É—auka sai wani satin za ka koma. Ya Auwal na tafe wannan weekend É—in fa."

  Sai da ya sha ruwa sannan ya ce min" Na so haka amman ranar Friday an saka mana wani test ne, ina bukatar komawa na yi karatu"

  Kai na jinjina kafin na ce"Haka ne. Allah ya bada sa'a. "
Da ya ke yana karatu ne A kaduna state University KASU"

Ko bai faɗamin ba na san abin da ya kawo shi. Alhajinmu yanzu ba kuɗi duk suna gona daman karatun na su shi Ya Auwal  da su Ya Hamza ne ke taimakawa sai ni da Amina da ɗan abin da ba a rasa ba nan take na tura masa 20k cikin kuɗin da ke acct ɗina.

"Ga 20k nan ka lallaɓa zuwa karshen wata in sha Allahu."

Godiya ya yi mini kafin ya ce" Yaya Auwal ma turamin 20k zan É—an yi siyayya kafin goben na wuce."

"Allah ya kai mu."

"Ma'u ta zo gida jiya muka haÉ—u na ce mata yau zan koma. Shi ne yau da safe ta kirani ta ce na je tana son ganina ta bani kayan tea da sabulun wanka da na wanki."

  Ya na mgana ina masa wani kallo sai da ya gama maganar sannan ya fahimta da sauri ya ce"Wallahi ba ni na roƙeta ba Yaya Sadiya."

  Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce"Allah ya ba da lada." Da na so na yi wata mgana sai kuma na fasa tuna nima na sauya taku akan Ma'u.

  Mun saki wannan hiran sai kuma muka kama na Yaya Abubakar a bakin Datti na ke jin shekaranjiya Zaituna ta kwaso rigima har da yan sanda aka kira mata. Ita wai uwar adashe ta cinye kuɗin jama'a. An ce dakyar suka ba da belinta sai dare da ta yi kwana cell.

  Mamaki ya kamani na riƙe haba ina faɗin"Kai matar nan wai har yanzu ba ta daina saka Yaya Abubakar a uku ba! Shegiya ka rasa abin da take yi da kuɗin jama'a sai ta jawo rigima ta bar ɗan'uwanmu da biyan bashin ta"

  Datti ya ce"Wallahi nima har mamaki na ke yi. Kuma shi Yaya Abubakar ɗin bai iya ɗaukan mataki a kanta ba."
Tsaki na ja kafin na ce"Yaushe wannan zai iya? Tun fa muna gida ni nasan Yaya Abubakar sai mace ta bautar dashi. Da dai irin su Ya Hamza ne kai kasan Zaituna ba ta isa ba. Shi fa yana jin sa kamar ba namiji ba"

  Datti na yar dariya ya ce"Sanyi gare shi ne."
Cikin jin haushi na ce"Sanyin me?  ya dai auro wacce ba ta san ciwon kanta ba. In bai tashi tsaye ba sai ta kashe sa lokacinsa bai yi ba"

  Datti dai ta na dariya. Ban san adadin awannin da muka ɗauka muna hira dashi ba. Ni a bakinsa na ji wai Alhajinmu ma ba shi da lafiya jiya ya yini da ciwon kai nace ni ba wanda ya faɗa min ya ce su Yaya Bahijja duk sun sani sun je sun duba shi har da Ma'u."

  Takaici ma ya hana ni mgana. Sai shi ne ganin raina ya ɓaci ya ce" Ƙila saboda sun ga bakya nan ne." Uhm kawai na ce ina duba agogon wayata tara da rabi na dare sai na zaro ido Yallaɓai bai dawo ba har yanzu.

  Wayarsa na kira ta na ringing amman bai ɗaga ba har sau biyu tuni zuciyata ta harba ina hashashen ko har yanzu yana can Ranon ne tare da ita? Ga Saude ta na jiran mu mu kaita gida ganin har goma ta yi Datti ya ce min zai tafi sai kawai na ce ya tsaya ya tafin mu da Saude gida.

"Ba nan take kwana ba daman?

  Ina miƙewa na ce"Ba a nan ba ne. ta zo ta kwana da yara. Yallaɓai bai dawo da wuri ba shi ya sa na ce ka wuce da ita."

  Sai ya amsa mini, ɗaki na koma na ɗauko 2k cikin jakata na wanda Yaya Hamza ya bani na fito. Sai na iske su afalo Datti ya ba ma su Jidda Chaculate din da ya zo musu dashi ya ce har ma zai tafi ya manta bai ba su ba.

  Na ba ma Saude 2k ɗin ina cewa"Yallaɓai bai dawo ba sai gobe zan shigo anguwan. Ki gaida mamanku sai na zo."
Ta karɓa tana min godiya Baby ta makale mata sai ta je dakyar na riƙe ta na ce ta bari ranar da ba makaranta sai su je can Ɗorayin su kwana.

  Har haraba na rakasu. Suna fita na rufe get ɗin muka dawo cikin gida. Ganin dare ya yi sai na rakasu ɗakin su suka yi shirin barci sai da na tabbatar sun yi addu'an barci sun kwanta sannan na rage musu hasken ɗaki na rufe musu ƙofa na dawo falon farko na kame kan kujera. Ga TV a kunne amman ba na fahimta duba lokaci kawai na ke yi a wayata har goma da rabi har sha ɗaya na dare Yallabai bai dawo ba. Bai kirani ba sannan na ƙara kiran shi amman bai ɗauka ba again.

  Na yi ta ƙokarin boye yanayina. Na zauna ina jiransa a falo ni kaɗai duk kwalliyan da na yi ta gama susucewa. Lallashin kaina kawai na ke yi ina zaune. Sha ɗaya da mintina sha ɗaya sannan na ji ana buɗe get da ƙaran shigowan mota.

  Ajiyar na sauke ina zaune har ya shigo falon. Muka haɗa ido dashi ya na shigowa da leda a hannunsa mirmishi ya ke yi min irin na shi mai sanyaya mini zuciya.
Amman sai na ji na kasa maida masa martanin mirmishin na shi, ya ƙariso har gabana ya na sauke ledan hannun shi ya ɗago kawai ni kuma na miƙe na wuce ma mukunnin wuta na kashe hasken falon na fice a falon na bar shi tsaye sake da baki yana bina da kallo.
Na sake kashe hasken falon na biyu daga nan na shiga tiolet na kama ruwa ko da na fito na same shi a cikin É—aki yana tsaye kawai ya harÉ—e hannu a kirjinsa yana kallona.

  Yi na yi kamar ban gan shi ba. Na isa gaban wardrope na laluɓo rigar barcina. Ina shirin tuɓewa na ji ya rumgumeni ta baya ƙamƙam bayan ya sagalo hannunsa ya riƙe rigar barcin dake hannuna.

  Na ja shima ya ja kawai sai na sakar masa. Numfashi ya fesar min ta saman wuyana. Duk ina jinsa sai na yi masa bakam mugun haushin sa na ke ji da wani abu mai zafi da ya tokare mini a ƙirji.

"Sadiya ta. Fushin kike yi da ni?

Haka ya faÉ—a ya na mai zuro da kansa wajen fuska.
Kauda kai na yi kafin na ƙwace jikina ya juyo muna fuskantar juna ni da shi cikin basarwa na ce"Fushin me? Ka yi wani abu ne?

  Haka na faɗa kai tsaye kuma na miƙa hannu ina faɗin"Ba ni rigar barcina. Ina so na yi shirin kwanciya ne "
Sai ya maƙe kafaɗa alamun ba zai bayar ba. Ni kuma kawai sai na juya na sake buɗe wardrope ɗin na ɗauko wata itama yasake ƙwacewa na bar masa na sake ɗauko wata itama ya sake ƙwacewa a ƙufule na kalle shi kafin na kira sunan shi.

"Yusuf.."

Haka na faɗa ina tsare shi da ido. sai ya yi wani iri da fuska kafin ya ce" Yallaɓan naki ne kuma yau ya dawo Yusuf?

"Ai sunan ka ne ko ba sunan ka ba ne Yusuf?

  Na faɗa cikin gatse ina hararan shi. Sai ya yi dariya ni kuma sai na juya ina ƙara laluban wata rigar barcin kai tsaye ya ce" Ko sau dubu za ki ɗauko sai na ƙara ƙwacewa gwara ma ki tsaya mu yi mgana."

  Ni na san halin ɗan kayana. Shi ya sa na dakata na juyo ina kallonsa kafin na ce" Ni fa ba ka yi min komai ba. Kawai dai ina so na kwanta ne."

Takowa ya yi gabana ya saka hannunsa guda ɗaya ya riƙe min hannuna guda ɗaya ya zaunar da ni a gefen gado sai ya durƙusa a gabana lokaci ɗaya ya na riƙe duka hannuwana cikin tafin hannunsa.

"Am Sorry. Na yi dare. A gidan Baba Hajiya ta matsa mini sai na tsaya na ci abinci sannan kuma Tariq ya zo gida shi da iyalansa shi ya tsaida ni muna hira ban san dare ya yi ba. Na ga kiran ki ina hanya shi ya sa ban É—auka ba."

  Har ya gama mganarsa ina kallonsa. Zuciyata ta ɗan yi sanyin jin ba abin da na yi tunani ba ne amman ban nuna masa ba sai na ƙara hade rai har ina kauda kaina gefe.

"Ki yi haƙuri kin ji ko? 

Ya faɗa ya na matse min yan yatsuna. Zare hannuwana na yi daga cikin na shi sannan na miƙe ina faɗin" Na ji."
Chapter 27 · 0% Book details