← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 76

Sashe 62

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Falon yara na koma na zauna ina maida numfashi. Na huta kafin na tashi na yi wanke wanke. Amman na so Yallaɓai ya ta shi ya yi wanka ya karya sai na haɗa komai na wanke domin da na fara shara na fara jin jiri tuni na je na karya cikina ya cika to ina zan zauna shi ya na can kwance ni kuma ina aiki yunwa ta far min a ciki na faɗi a sume tuni na nema ma kaina mafita na karya na barshi.
Na yi hutun sama da minti talatin domin kallo ma ne ya ɗau hankalina wani film ɗin hausa da suke haskawa tashar Arewa24 na ga ya fara mini kyau sai na zauna ina kallo tuna ina hutun jaki da kaya a saman kaina ne ya sa na miƙe. Har na fara wanke wanke kuma sai na tsame hannuna a cikin ruwan omo na wanke da ruwa na fita zuwa cikin bedroom ɗinmu.

Tsaye na yi kawai a gaban gado ina kallon Yallaɓai ina sanye da wando baki plazo rigar jikina vest ce ta lame min jiki kaina ɗankwalin doguwar riga ne na yi gammo da shi a saman kaina.
Zuwa na yi kusa dashi, na fara jan bargon ina kiran sunan shi amman sai ya juya ya na jan bargon ina ja, alamun dai ba zai iya ta shi ba.

"Yallaɓai.."

Na faÉ—a ina dai dai ta saitin kunnuwan shi. A hankali ya buÉ—e idanuwansa da suka shige ciki saboda barci.

"Mene ne kuma?

Ya faɗa da muryan barci har ya na wani yamutsa fusaka ina ganin haka na saka hannuna na shafa kumatunsa sai ya ji sanyi da sauri ya ware ido yana kallona ni kuma sai na koma na riƙe kugu ina kallonshi rabi harara harara.

Ɗan tashi ya yi kaɗan ya na jingina da jikin gado kafin ya kalleni daga sama har ƙasa sai kawai na ga ya yi mirmishi kafin ya ce" Me kuma na yi! ?
Baki buɗe na ce" Me ka yi fa ka ke tambayata Yallaɓai?
Ya na kallona ya ce" To ba dole na tambaya ba, kin ta da ni kamar yaƙi. Ga shi ke kuma kin riƙe kugu kamar mai shirin dambe."
Yana cewa mai shirin dambe na dunkule hannu na ware kafa ina masa gusha gusha sai na kai masa hannu kamar zan naushe shi. Dariya ya ke ta yi kafin ya ce"Oh yau tekwando rana za mu yi kenan! To ai na iya irin wannan ba ri ki gani"
Kawai sai na ga ya sauko ƙafafunsa ƙasa ya janye bargon sanin halin shi ya sa na yi saurin dawowa dai dai na riƙe masa hannu ya koma ya zauna na zauna a gefen shi na mararaice ina faɗin" Yallaɓai na."

  Na faɗa har ina masa fari, ina zan yarda ya yi wasan chinese da ni. Lokacin ina amarya sai ya ce mu yi daga karshe dai na gane ni ce ke shan wuya ya fi ni karfi awasa duk ya naushe ni in na yi shagwaɓa na ce da zafi sai ya ce wai saboda kashina ya yi ƙwari kuma nan gaba ya koya min faɗan kare kai. Daga baya na ce ni wallahi ba na so shi ya sa muka daina amman ina amarya ba wasannin da ba mu sha yi ba. Ko dawowarmu nan gida in ya na da lokaci muna yar gudu ni da shi da yara ranar weekend muna da kayan jugging. Daga baya na daina fita saboda na gaji ban iyawa shi kuma ya ce wai na tara kitse ne shi ya sa. Sai dai ranar da ya so ya na fita tare da jidda da Baby ya na kuma gaya musu motsa jiki na ƙara lafiya a jikin ɗan adam.

Yadda na yi masa farin ne da yanayin maganata ya sa ya san akwai abinda na ke so.
Cikin mirmishi ya ce" Me kike so ne Sadiya? Domin in za ki cuce ni haka kike yi."
Hannuwansa na riƙe cikin nawa na marairaice ina faɗin" Haba Yallaɓai na wani rin cuta kuma? In miji ya taimaki matarsa sai a kira shi cuta?

  "Kamar wani taimako kenan?

  Ya faɗa ya na mai tsare ni da ido da sauri na marairaice kafin na ce" Yallaɓai na yi shara na yi mopping na wanke Tiolets baya na duk ya kage to kuma  ga  wanke wanke can ba a yi ba."

  "To shi me? Wai na je na yi wanke wanken?

Ya faÉ—a yana kallona da sauri na ce" Ni ban ce ba."
Sai kuma na saki hannun shi na miƙe ina tafiya daƙyar kafin na ce" Ka tausaya mini Yallaɓai Allah bayana ke ciwo."

"Kina da ciwon baya ne ban sani ba?

Ban juyo ba na ce" To ni dai ina tunanin tun lokacin haihuwan jidda na goce. Kasan kuma sai a hankali a hankali ya ke tashi."
Da iya gaskiya na faɗa domin wani lokacin in na yi aiki bayana sai ya rike amman sai Yallaɓai ya ce" Ba shakka. To sannu."

Yanayin mganar na shi ya sa na san bai yarda ba sai na juya ina faÉ—in" Fisabillahi Yallabai yanzu ka lalace sam ba ka son aiki."
Me Yallaɓai zai yi ba dariya ba, ni ko sai na tsaya ina kallon shi da gaske fa haushi ya ke ba ni, ya na gida ace ba zan more shi ba.
Sai kawai na tura baki kafin na ce" Ko a da ka fi tausayina ne! Yanzu kuma ka daina tausayina ko?

  Ganin yana kallona yana dariya yasa na fara matsan kwallar karya ina faɗin" Ko dai ka daina sona ne Yallabai?
Na tsare shi da ido har lokacin fa bai daina dariya ba. Sai kawai na fashe da kukan da ba hawaye ina faɗin" Na shiga uku Yallaɓai na ya daina so na"
Ya na dariyan ya ƙariso ya rumgumeni yana faɗin" Mamaki na ke yi da har yanzu ba ki san aikin da nake yi mai muhimmanci a cikin gidan nan ba?
Sai na É—ago ina kallon shi kafin na ce" Wani aiki ne? Barci ko?

  Sai kawai ya kai hannun shi saman ƙirjina ya na shafawa ina kallon shi na ga ya dage min gira ai da sauri na kwace jikina ina faɗin" Ai daman anan kafi auki ba za ka zo ka tayani aiki ka motsa jikin ka ba."

Na faÉ—a ina tura masa baki. Yana dariya ya ce" Ai abin da nake yi shi ne babban misalin motsa jiki."
Sai kawai na jinjina kai kafin na ce" Kuma kana taimakon kanka ba."
Sai ya daga hannu saama kafin ya ce" In ji wa? Taimakon kai da kai dai ko?
Balla masa harara na yi na kama hanyar fita ina faÉ—in" Kai dai ka sani."
Ina jin sa ya biyo bayana yana faÉ—in" Ciwon bayan ya warke ne?
Sai na tuna da sauri na riƙe kugu na sauya tafiya ina cije baki. Yallaɓai dariya har tana sauti na yi masa banza na fice ina faɗin ai sai ya yi ta kwanciya.

  Har na dawo zan cigaba da wanke wanke ya leƙo ya ce na zo na bashi abin karyawa. Dole na koma falo na haɗa masa tea na zuba masa ɗumamen tuwon da na yi jiya da daddare miyan allayu zama na yi sai da ya gama ci muna yi muna hira bayan ya gama na tattara komai zuwa kitchen sai ya biyo ni ya na faɗin" Je ki huta bari na yi "
Ina jin haka na daka tsalle na rumgume shi na bashi sumba a baki kafin na ce" Yaron kirki Yallaɓan Sadiya."
Kaina ya dankwanfar ya na faÉ—in" Sai na fasa."
Da sauri na ce" Na tuba ranka ya daÉ—e ka yi mini rai."
Yana dariya ina dariya ban kuma iya zuwa na huta ba saman cabinet É—in kitchen É—in na haye na zauna yana wankewa ina karba ina jera su a muhallinsu.

  Anan ne ma ya ke ce mini yanzu ya girma iyalai sun fara taruwa ba girman shi ba ne a ka ga yana aiki
Ni ko sai na buÉ—e baki na ce" To mi ye a ciki? Ko Æ´ayan ka sun gan kana aiki ba abin kunya ka yi ba ka na koyi da sunnar ma'aikin mu ne kuma daman da shi muke koyi "

"Uhm daÉ—in baki ko?

Ya faÉ—a ya na kallona da sauri na ce" Haba Yallabai ai tsakanimu ba daÉ—in baki sai dai gaskiya da gaskiya."
Na faÉ—a ina masa yar dariya sai kawai ya kalleni ya girgiza kai kafin ya ce" To ke ina wani aikin da kike ta zuzutawa? Tun auran mu tare muke aikin nan ban daÉ—e da daina yi miki girki kina kwance ba."

Sai na buÉ—e baki ina kallon shi, ban rufe ba ya cigaba da faÉ—in" Kuma hatta renon su Jidda tare muka yi shi to ina aikin da kike ta kira?
Sai na rufe bakina na kasa mgana sai da ya yarfa min ruwan wanke wanken da ke hannun shi yana faÉ—in" kin kasa mgana ne?
Sai na kauda kai ina faÉ—in" To na ga abin ya koma gori ne gwara a bar mganar."
Dariya ya yi yana ƙokarin sake mgana na yi saurin cewa" Yallabai yau ba za ka fita ba ne?

"Zan fita mana. Zan je office akan mganar aikin nan na kaduna ki yi min addu'an Allah ya sa ta faÉ—a za mu samu alheri in sha Allahu.'"

Da sauri na ce" In alheri ne Allah ya tabbatar in babu Allah ya kawo na alherin."

"Amin Amin Abar ƙauna ta."
Ya faɗa ya na min wani kallo sai nima na tsume ina masa kallon soyayya. Sai kawai Yallaɓai ya ce a hankali" Ko mu je mu yi ɓarnan ruwa ne mu dawo?
Da sauri na ce" A'a. Fita fa za ka yi nima zan je Gwammaja."

"To mu haÉ—a wankan mana ba shikenan ba."

"Ba ko shiken nan ba.'

Na faÉ—a ina haran shi, dariya ya fara yi min kafin ya ce" Me ke damun ki ne? Allah kin fara zama raguwa."

Ko magana ban yi masa duk irin ƙokarin da nake yi wai na fara zama raguwa.
Chapter 62 · 0% Book details