← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 76

Sashe 45

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  In da ma su Gwaggo suka fahimci yana son Ma'u bini bini sai ya je Kura gaida Baaba da ɗan siyayyan shi itama kuma ta fahimta. Magana dai ta yaɗu a tsakanimmu amman ba ta je wajen Alhaji ba. Su Yaya Murja kar a ji labari tana faɗin tuwona maina ne za'ayi ita ƙanwar ango sannan yayar Amarya. Ban taɓa tunanin Ma'u da Baaba za su iya tunanin abin da suka aikata ba. Domin Yaya Abubakar kafin ya kai mganar Ma'u wajen Alhaji ya yi magana da Gwaggo sai ta tambaye shi ko ita Ma'un tana son shi sai ya ce a'a bai bayyana mata ba sai ta ce ya nemi yardan Ma'u.
 
  Abin da ya sa na san haka ya faru. Ranar wata asabar da daddare Yaya Abubakar ya kira Ma'u zuwa zaure na fito daga ɗakin Hajiya na gansu sun wuce shi ya sa na bi bayansu a lokacin ne na ji yana faɗa mata yana sonta ya faɗa ma Gwaggo ga abin da ta ce. Ma'u ba kunya ba tsoron Allah ta buɗe baki ta ce ma Yaya Abubakar ya yi haƙuri ita a matsayin yaya ta ɗauke shi ba da wani manufa ba tun da aka kawo ta gidan nan Yaya Hamza ta ke so. Ina laɓe ina ganin har duƙa mata ya yi amman Ma'u ta fara kukan munafunci sai ya ce shikenan saboda ita muguwa ce sai ta ce wai ya taimaka ya rufe mganar ba ta so Alhajinmu ya ji shi kuma ya ɗau alƙwarin ba wanda zai ji Gwaggo ma zai san abin da zai faɗa mata.

Kafin ta taho na shige É—akin Hajiya ina maida numfashi ta na kwace sai da ta ce" Dubu lafiya?
Ina sauke numfashi na ce" Ba komai Hajiya."
Ranar ko barci ban yi ba ina tunanin mafita ko da ba shiri tsakanina da Yaya Abubakar jinina ne. Na ji tausayin shi da ya sa na fara tunanin yadda zan ɓullo ma lamarin. Washegari na je gaida Alhaji sai ga Ma'u bayan sun gaisa ta ce wai in Alhaji ya bar ta za ta je kura wajen Baaba.

Ina jin haka na ji a raina akan Yaya Abubakar ne. Saboda lokacin wayar hannu ba ta daÉ—e da shigowa ba sai wane da wane Alhajinmu kaÉ—ai ya mallaketa. Ina jin sanda ya ce shikenan sai ta shirya cikin ni ko Rahila wata ta rakata ina jin haka na yi karaf na ce" Alhajinmu ni zan rakata."

   Ba Ma'u ba har Alhajinmu sai da ya yi mamaki. Ma'u kam sake baki tayi kawai tana kallona.
"Lalle Hasiya na da babbar baƙuwa."
Haka Alhajinmu ya faÉ—a ni ai ban tsaya ba na koma É—akin Hajiya ina haÉ—a kayana Hajiya ta ce lafiya na ke haÉ—a kayana.?

"Ma'u zan raka kura wajen Baaba."

Da mamaki Hajiya ta kalleni ba ta da wani karfi kwana biyun nan ba ta da lafiya ta na fama da zazzaɓi sai da aka kaita ma asibiti. Maida kanta ta yi ta kwanta lokaci ɗaya ta na faɗin" Yau kuma? To Allah ya tsare."

Kowa ya ji zan raka Ma'u sai ya yi mamaki har Rahila sai da ta ce"Allah ya sa Sadiya kin sauya kenan."
Ni ba na ta kanta ni na san abin da zai kai ni.
Ma'u ba ta da yarda za ta yi ta na ji ta na gani na shirya kayana Alhajinmu ya bamu kuÉ—in mota mun bar gidan ba ma mu haÉ—u da Yaya Abubakar bawan Allah shi kaÉ—ai ya san abin da ke damunsa.

Har muka isa kura sannu ba ta haÉ—amu da Ma'u ba. Mun isa gidan Baaba ita kanta ta yi mamakin ganin mu tana da abokiyar zama. Zaman dai ba wani daÉ—i ita kanta ta yi mamakin ganina tare da Ma'u cikin mamaki ta ce" Yau kuma wannan ce ina Rahilan?
Ma'u ce ta amsa da cewa ni ce na rakota wannan karon.
Duk da ban samu tarban da ya kamata ba ban damu ba Zainab ce kawai ƙanwarta ta kulani duk da ta na ƙarana ne sai sauran ƙannenta maza. Bayan mun yi salla mun ci abinci Ma'u na son keɓewa da Baaba amman ba hali tun da na hana ina wajen. Sai daddare sun ɗauka na yi barci suka ƙule cikin ɗaki ba su san ina kwance laɓo ina dakon su ba. Ina ganin sun shige ciki nima na tashi saɗaf saɗaf na laɓe ta jikin labule a daga nan na ke jiyo muryan Baaba ƙasa ƙasa.

"Shi wai Abubakar É—in ya ce ya na sonki?

Ma'u ta ɗaga kai cikin damuwa saboda ina hangosu ta jikin labulen ƙurwan ɗakin

Sai kawai Baaba tayi tsaki kafin ta ce" Shi ma dai da rigima ya ke. Ai ke matar manya ce duk da ban raina Abubakar ba. Sai dai tunda Hamza kike so shi ne zaɓina kuma ba kin ce yana can yana cigaba da karatu ba? Nan gaba Allah kaɗai ya san abin da zai zama."

Ma'u ta kalli Baaba kafin ya ce" Baaba ya zan yi? Har fa ya faÉ—a ma Gwaggo. Kuma su ma yan gidan sun fara gane yana so na ba na so Alhaji ya ji labari Yaya Abubakar ya yi min katanga da abin da na ke so.'

Baaba ta kama hannun ta lokaci É—aya tana faÉ—in" Kwantar da hankalin ki. Gobe da safe ku koma gida ni kuma cikin satin nan zan shigo. Da ikon Allah ke rabon Hamza ce."
Sauri na yi na koma wajen kwanciya a falo a saman katifa na yi kamar mai barci sai can bayan wani lokaci Ma'u ta fito ta dawo ta kwanta a gefena. Ta kwana mutsu mutsu nima haka a cikin raina ina tunanin ta wata hanya zan hana Baaba aiwatar da kudirinta?

Har muka koma kano ban samu mafita ba. mun koma mun iske Yaya Abubakar na kwance ba lafiya daga ni sai Ma'u muka san dalilin ciwon shi. Zazzabi da ciwon kai har dai da Yaya Muntari ya raka shi asibiti ya ga likita.  Na ɗauka Ma'u za ta tausaya masa amman sai na ga kamar ba ta da tausayi ban samu mafita ba har Baaba ta zo gida ta kuma tara su Alhajinmu ta kawo mganar Ma'u tana son Hamza tun tuni ganin abin na gida ne yasa ta zo da mganar Alhajinmu na jin haka ya fara murna ya ce kuma zai aurama Ma'u wanda ta ke so. Gwaggo ta na so ta yi mgana amman Baaba ta san me za ta ce sai ta datse ta. Bayan an gama zaman a ɗaki Hajiya Dubu ke faɗa mini abin da ke tafe da Baaba. Daman na san za a rina. Ma'u na so ta haɗa mana yaƙi a gida Yaya na sonta ita kuma tana son ƙani.

Cikin lokaci kawai na ji ana mganar haɗa auran Yaya Hamza da Ma'u da kuma Rahila da Muntari. Yaya Abubukar kuma Alhajinmu ya ce fito da matar aure. Ba shi da mafita illah ya amsa Gwaggo ta so ta yi magana sai na ji sa yana roƙonta ta bar mganar shi da Hamza duk abu ɗaya ne. Kowa ya ji ba Yaya Abubakar ba ne sai ya yi mamaki saboda shi dai Yaya Hamza kowa ya san halin shi. Shi kuma Umarni kawai Alhaji ya bashi, shi kuma bashi da mafita. Amman kwata kwata bai taɓa hasaso da ya auri Ma'u ba. Da farko da aka sanya lokaci na yarda makaman yaƙina ganin har Alhajinmu ya ba ma Yaya Hamza umarnin dawowa gida ya ga Ma'u ya kuma dawo sun gana Ma'u ta yi ta rawan jiki ita a dole burinta ya cika.  Sai dai me Yaya Abubakar ya kasa ɗaukan takwallalin ya haƙura da Ma'u ya fara rama a tsaye ga yawan ciwo ina tsoro kar rashin tausayin Ma'u ya kashe min ɗan uwan na yi ta kulla yadda zan yi na rasa mafita.

A wannan halin an saka ranar auran su da zaran mun ƙara zana jarabawar sakandiri a karo na uku. Yaya Muntari ya samu aiki da wani kamfanin sarrafa leda. Shi kuma Yaya Hamza ya fara aiki da bankin first bank a can ibadan ɗin. Ni ba kaina na damu dashi ba saboda ban samu miji ba daman kuma ni burina sai na gama jami'a zan yi aure.
Muna gabda gama zana jarabawarmu kawai Yaya Abubakar ya fara wani ciwo har da kwanciya a gadon asibiti ganin haka yasa na ce ba zan bari Ma'u ta kashe mini É—an'uwa.

Ni na je na samu Hajiya Dubu na faÉ—a mata duk abin da na sani. Ita kuma ta samu Alhajinmu ta faÉ—a masa abinda ke faruwa ni na ba da shaidar Gwaggo ma ta sani da aka kirata sai ta amsa amman ta ce Abubakar É—in ya ce a bar mganar kar kowa ya sani kuma itama tana ta tabbacin ciwon nan saboda Ma'u ne. Alhajinmu bai yanke hukunci ba sai aka sallamo Yaya Abubakar daga asibiti Alhajinmu ya taramu a gaban kowa da kowa har da masu auran da Yaya Hamza da Alhaji ya sa ya dawo garin.
A gaban kowa da kowa ya tsitsiye Yaya Abubakar sai da ya faÉ—i gaskiyan yana son Ma'u duk yadda ta yi ta masa inkiya da ido kar ya faÉ—a. Har Baaba an kirata tana wajen jin haka shima Yaya Hamza ya ce ya bar ma É—an uwansa shi daman baya sonta.

Hankalin Ma'u da Baba ya tashi saboda Alhajinmu ya ce an maida auran Ma'u akan Yaya Abubakar kuma ya yi ta faɗan cewa ba domin na zo na faɗa ba da an yi auren kuma azo ana neman mafita. Ban manta kallon da Ma'u ta yi mini a wannan lokacin ita da Baaba. A kuma nan take ta fashe da kuka ta ce ba ta son Yaya Abubakar Yaya Hamza take so shi kuma ya ce a ƙanwa ya ɗauketa. Alhaji ya rasa mafita yace zai yi mgana da sauran yan uwanshi. Har sai da su Baba Aminu su ka zo garin. A ɗakin Hajiya suka zazzauna suka tattauna Hajiya Dubu saboda samar da masahala sai ta kalli Alhaji kafin ta ce
Chapter 45 · 0% Book details