← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 76

Sashe 51

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yallaɓai ya faɗa bayan sun ƙara musabaha da Tariq.

Shi ya bude musu get suka fita muna É—aga musu hannu Allah ya sa baby ta samu biskit da ta yi rigiman sai ta je.

Mun dawo cikin falo na kalli Yallabai ina faÉ—in" Duk abin da kuka faÉ—a akan Uncle Abba sai na faÉ—a masa."

Yana ƴar dariya ya ce" To wai shi ne me? In ba ki da kati ki yi mini mgana sai na saka  miki."
KafaÉ—ansa na kai ma duka ina dariya shima yana tayani. Mun zauna kan kujera É—aya muna hira nan ne na ke gaya masa zan je ÆŠorayi da wuri saboda yau su Yaya Auwal za su koma wajen aikin su.

"Ok. Zan kai ki ne da kaina?

"No. Ka bari dai sai ka je ka É—auko ni"

Sai ya gyaÉ—a mini kai sai na mike na wuce da farantin ruwan da na kawo ina faÉ—in.

" Bari na je na wanke ma su jidda kan su."

Da kai ya amsa min, sai na bar masa falon gabaɗaya. Kitchen na biya na sauke kayan hannuna sannan na shiga dakin su Jidda na ga sun gama tsifan har Saude ta ƙara share ɗaki.

"Saude je ki wanke min sauran kofunan da suka ɓaci bari na wanke musu kai tare za mu tafi ɗorayi."

"Umma ba kin ce za ki yi mana kitso ba?

Jidda ta tambaya ne, sai na kalle ta kafin na ce" Sai na dawo ko zuwa dare ne."
Mayafin jikina na cire na shiga tiolet É—in akwai mayukan wanke kansu a ciki tunda daman rabi na kan raba na su da nawa. Kuma daman na iya ni nake yi ma kaina wankin kai ni da yayana a gida tunda ina da handrayer.

Ruwa na tara mai ɗumi sannan na kira Baby na fara wanke mata sannan jidda a karshe, bayan na gama na fito na jona handrayer na busar musu da gashin gabaɗaya na shafa musu man kitso Jidda ita ta ƙara taje kanta ta daure da band ni kuma na yi ma Baby duk da ana yi ta na kuka har sai da Yallabai ya leƙo yana faɗin" To a kyaleta mana tun da an gama"

Ina kallon shi kafin na ce" Za a dai gama amma ba a gama ba."
Sai da na matse na samu na daure mata gashin. Yallaɓai ya ɗauke ta yana lallashinta lokaci ɗaya yana share mata hawaye, domin har da majina saboda kukan.

"Ba ki son gashin ne?

Yallaɓai ya faɗa duk cikin sigan lallashi sai ta gyaɗa masa kai, da sauri ya kalle ni kafin ya ce" Sadiya to a yi ma Baby aski ba ta son gashi balle ta rika kuka ko?
Sai ya kalleta kawai sai ta fashe da kuka tana faÉ—in" Ba na son aski."

Yallaɓai sai ya kalleni kafin ya ce" To a bar mata gashin ta shi ke nan? Ya sake kallonta sai ta gyaɗa masa kai, rumgumeta ya yi, ni kuma me zan yi in ba dariya ba. Jidda ma ta na ta dariya Yallabai ya sunkunci Baby ya fice ya na faɗin" Tunda kun yi faɗa da Umma sai a ji da Abba ko?

Bin bayan su na yi bayan na ce jidda ta ƙara share ɗakin saboda gashi. Ganin har an kusa azahar sai na bi Saude kitchen na ce bari kawai na dora farar shinkafa ina da sauran miya sai a ci da shi kafin mu tafi.

Ni da na so fita tun bayan azahar sai gani har karfe uku sai da muka ci abinci na sauya kaya sannan na bar ma Yallaɓai amanar gidana da yarana ina ta ƙara jadadda masa.

Sai kawau ya ce" Na ji mai gida. Kina ta mini kashedi megadi ne ni?
Ina dariya na ce" Kamar haka! Tun da ko a ina aka je gida na Sadi baby ne."
Na ƙarishe faɗa ina masa fari sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce" Hausawa suna cutar mu. Kai da guminka sai ka ji ana gidan Sadiya."

"Ko gidan Maman jidda ba."

Na faÉ—a ina yi masa dariya.

"To ba a cewa na Baban jidda."

Yadda ya yi mganar ne yasa har ina riƙe ciki wajen dariya. Mun rabu sai mangariba zai zo ya dauke ni bayan ya sake duba Alhaji.

A daidaita muka samu zuwa Ɗorayi a kofar gida muka yi sallama da Saude bayan na ce  ta gaida mamanta.

****

ÆŠorayi.

Ko da na je gida cike da ƴaƴa da jikoki. Domin kaf su Yaya Murja da yaransu suka zo tun da yau lahadi ba makaranta. Na iske har Ma'u tare da Zainab da su Alhaji ƙarami. Rahila ce kawai ba ta zo ba wai ba ta jin daɗi

Mutanen Abuja dai sun riga sun tafi saboda nisa. Sai Yaya Hamza ne shi ma lokacin da na zo suna sallama ne za su É—au hanya. Amina kuma za ta bi su su rage mata hanya daga zariya sai ta hau motar kaduna. Da ta ce sai gobe megidanta zai zo su koma tare to shima sai daga baya ya kirata ya ce suna da taro a wajen aiki da wahala ya samu zuwa. Ya dai yi ma Alhajinmu sannu ta waya. Tunda mijin Amina lacara ne a jami'ar kaduna.

Kallon ta na yi lokacin da muka samu keɓewa a ɗakin Mama ina faɗin" Ke yanzu da sai ki tafi ba mu yi sallama ba?
Ta na yar dariya ta ce" Ai na san kina hanya."
Gyara zama na yi kafin na ce" Tun da Datti ya koma ya zo gidanki weekend kuwa?

"A'a ya ce suna ta test ne. Zai zauna a cikin makaranta ya yi karatu. Ƙila sai sun gama zai taho.'

Sai na jinjina kaina. Saboda Datti a farkon shigarsa jami'ar a gidan Amina ya fara zama amman sai aka samu matsala tun da akwai wani ƙanin mijinta a gidan da suka yi ta samun matsala da Datti har lamarin na neman shafan auren Amina tunda kowa kanshi ya sani. Sai Yallaɓai ya ba da shawaran gwara ya samu hostel ya koma can da zama, Allah ya sa ma akwai wani abokin shi ɗan nan kanon ne shi ya bashi waje a ɗakinsa suka yi sukwatin. Sai dai ya na ɗan zuwa wani lokacin ya yi ma Aminar weekend.

"Mubarak É—in ma ba ya nan yanzu. "

Ita ta katse min tunani Mubarak sunan kanin mijin na ta.

"Me ya faru? Har ya gama karatun?

"Ban sani ba. Amma ina kyautata zaton kamar ya samu matsala ne duk da yayan na shi baya son faɗa mini. na san ya na Aji uku ne sai ya tafi can zuntu sama da wata biyu bai dawo ba gashi ana ta karatu sai na yi zargin wataƙila ya samu matsala ne a can makarantar."

Sai na gyaÉ—a kai kafin na ce" Za ta iya yuyuwa. Ke dai tunda ba a faÉ—a miki ba. To ba ruwan ki."
Tana dariya ta ce" Haba. Kamar ba ki sanni ba'
Aiko na san Amina miskila ce kafi mahaukaci ban haushi, mun ɗan yi hira sama sama kafin Khaleesat ta leƙo ta na fadin ta fito su wuce ni na riƙe mata karamin akwatin ta muka fito suna falon Alhajinmu muma sai muka shiga can.

"Na gode ƙwarai. Allah ya kai ku lafiya."
Alhajinmu ya faɗa ya na ɗan kishigiɗe a saman kujera. Ya na riƙe da Amna Tasleem na kusa dashi.
Khaleesat ta duka a kusa da Mijinta ta na faɗin" Allah ya ƙara lafiya Alhaji sai mun ƙara dawowa."

"Allah ya sa. Na gode Allah ya yi muku albarka gabaÉ—aya."
Muka taya su amsawa da Amin mune rakiyar har waje bakin mota gabaÉ—ayanmu ba mu iyayen ba, sannan ba yaran ba.

Sai da suka ɗaga muna ɗaga musu hannu suna ɗaga mana. Har sai da motar su ta ɓace ma ganin mu sannan muka koma cikin gida.
Aneesa É—iyar Anty Balki ce ta tambayi su Jidda na ce suna gida, a É—akin Mama muka yada zango gabaÉ—ayan mu tun da an ce a bar Alhaji ya huta É—akin Gwaggo kuma ta ce Baaba na ciki tana barci kar a dame ta.

  A kusa da Yaya Aina na zauna ina faɗin" Wai su Marwa ba su samu hutu ba ne?
Kai tsaye ta ce mini" Sun kusa fara jarabawa. In ta dawo za su fara pratical a asibiti to babanta ya ce ta dawo gida ta yi kawai."
"E. Gaskiya ai yafi. Ni ko wai ba ta da waya ne kwanaki ina ta kiranta a kashe "

"Ta lalace tana saka layinta a wayar wata ƙawarta ce."
Sai na kaÉ—a kai kafin na ce" Haba shi ya sa ba na samunta. Ta dawo sai a gyara in ba ta yi sai a siya wata amman ba ta zauna ba waya ba."
Yaya Balki ta yi karaf ta ce" Tun da tana da uwa Sadiya ba"
Sai na fashe da dariya kafin na ce" Kwarai kuma matar Injiniya ba."

Yaya Aina na dariya amman ba ta yi mgana ba. Yaya Murja na zaune waje É—aya da Ma'u sai da suka jiyo suna kallon mu, sai na yi kamar ban gansu ba muka cigaba da hiranmu da su Yaya Aina. Muna nan zaune sai ga Zaituna ta shigo fakam fakam kamar an jeho ta.

Yaya Balki ce ta yi mata mgana da cewa" Daga ina? ÆŠazu mijin ki ya fita ya na cewa ba ki zo ba?
Ruwa ta ce a bata sai da Aneesa ta kawo mata pure water biyu ta shanyen su tana maida numfashi.

"Wallahi na É—an je barka ne. Wata yayarmu ce ta haihu."

Daga ji ƙarya take yi saboda sai wani faman kifta ido ta ke yi kamar wacce ta yi ma sarki karya.

"Za ki ci abinci ne?

In ji Yaya Murja ai da sauri ta ce" Wallahi kamar kin san ina jin yunwa. Can anguwa uku ne ba mu samu abin hawa ba sai da muka ci uban tafiya duk abincin da na ci ya gama zazzagewa."
Chapter 51 · 0% Book details