← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 76

Sashe 71

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Wani kallo na yi mata sai ta kama dariya Hauwa na taya ta. Nuna ni take yi tana faɗin" Ta firgita ta. Kin gan fa Hauwa."
Ta faÉ—a tana nuna ni ture hannunta na yi ina faÉ—in" Firgitan me? A kaina za ta zauna? Allah ya kawo ta lafiya."
Hauwa da Munnira na ta danne dariya haushi ya kamani na ce" Wai dariyan na menene kuma? Ko kin ji labarin auren ne ni ban sani ba?
Da sauri Hauwa ta ce" A ina? Wallahi wasa ne kawai ba abin da muka ji."

Hararan su na yi domin na ga sun maida ni abin zolaya. Munnira ce ganin na haÉ—e rai ina faÉ—in" Ko za a mini kishiya sai an yi miki Munnira in sha Allahu."
Da karfi ta amsa da cewa" Wallahi ba Amin ba. Cab"
Ina mirmishi na ce" Au ashe ba daÉ—i? Sai ta marairai ce tana faÉ—in" Daga Wasa? To a bar mganar kawai."

  Ni kuma na ce sai an yi ta. Munnira uwar kishi ta ce ita fa ta tsani labarin kishiya. Ganin na na ce ina cewa Nasir sai ya yi aure nan kusa in sha Allahu Hauwa na taya ni sai kawai ta sauya mganar da cewa" Na ce ba ya mganar kayan gyaran can ɗin? Ina ga zan siya nawa nawa ne?
Ni da Hauwa har muna tafawa saboda dariya sai da na gama ja mata aji sannan na yi mata bayanim ingancin kayan gyara na Hajiya Surayya Halin yau.
Cikin mamaki Munnira ta ce" Da gaske suna da kyau? Ba su dai cutarwa ko?
Kai tsaye na ce" In da suna cutarwa da tuni sun cutar da ni. Ke Munnira ki cire wannan tunanin a ranki na matan da ba su san kansu ba. Yanzu mata sun fahimci muhimmamci gyara a jikinsu wanda ba zai zama cuta a gare su ba. Kin ga mganin infection ɗin nan yana da kyau duk bayan wattani uki mace ta riƙa shan shi. Saboda shi infection 90% na mata muna dashi sannan mu ke zuwa gidajen biki da suna muna mu'alama da banɗakuna mabambamta. Kin ga kowani lokaci za mu iya ɗauka sai mun dage da mgani sannan maganar gyara Munnira ba wanda zai cutar dake ba yar gumbar nan ta mata ɗan kazan nan na haɗin uwargida ba komai a cikinta sai itatuwan maganin da zai ƙara miki Ni'ima. Bayan nan za ki riƙa gyaran ki a cikin gida kayan marmarin nan ki riƙa shan su madara su rage kayan ganye da sauran su duk suma suna taimakama wajen dawo da ruwan jikin mu kin gani nan duk bayan wata uku sai na siya mganin infection na sha sannan na bi da kayan gyara bayan kuma ina yin nawa dubarun a cikin gida hatta fatata ban  zauna ba bayan wani lokaci ina siyan mayukan gyaran jiki domin kaina da kuma Mijina. Ba kuma domin shi ɗin ba sai domin ka riƙe wannan martaban da Allah ya ba ka na ƴ'a mace. Sannan yana da kyau ka yi gyara domin ka farantama mijinka Munnira ba sai an kawo maka wata ka haukace ba. Wanda ko da watan ta zo sai dai ita ta yi gasa da ke ba dai ki yi da ita ba tunda komai ta zo ta iske ki kin san shi kuma kina yi saboda haka ki yi ma kanki faɗa ki gyara jikin ki da kanki saboda martaban ki Munnira"

"Gaskiya ne Sadiya mganar ki Haƙƙun."

  Hauwa ta faɗa tana mai jinjina kai.  Munnira da ta yi tagumi ta na saurerena sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Kuma gaskiyan ku ne. To zan dage in sha Allahu. Kuma kamar na fara ganin wani alamu a wajen Nasir duk da bai yi mini mgana ba."

"Alamun me?

Na tambaya ina kallonta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Yanzu ba ya daÉ—ewa da mun fara mintina goma sai ya sauka kuma da ba haka ya ke yi ba"
Ni da Hauwa muka kalli juna kafin na maida kallona kan Munnira ina faɗin" You see. Akwai sanyi ajikinki kuma a yadda na fahimta ba ya wani jin daɗin ki yana dai yi ne saboda fita haƙƙi ki sai kin dage Munnira"
Tuni ta natsu tana faɗin" To zan dage gaya mini mafita. Allah Sadiya ba na ƙaunar kishiya"
Yadda ta yi mganar ne cikin tausayi ya sa muka tsintsire da dariya ni da Hauwa kamar za ta yi kuka ta ce" Don Allah ba dariya ba. Ku taimaka mini."

Sai na gyara zama ina faɗin" Za mu taimake ki amman ke ma sai kin miƙe kin taimaki kanki."
Sai ta ce ta ji duk za ta yi nan take na ɗauko wayata na kira Hajiya Surayya Halin yau. Bayan mun gaisa sai na ce zan haɗa ta da Munnira domin ta yi mata bayani ina ba ta wayar sai na ce ta shiga ciki yadda za ta samu damar yi mata bayani sosai. Sun ko jima suna waya sannan Munnira ta kawo min wayar nan Surayya ke faɗa min za ta fara shan na infection kafin haɗin kayan gyaran ya biyo.   Mun rabu akan Munniran za ta karɓi lambar wayarta su ƙarishe mgana.
Washegari ma ta ce za ta aiko ma da Munnira saƙon ko ba ta saka kuɗin ba tunda ta hannuna ne.
Duk mai bukatar mganin infection sadidan, ko mganin gyaran uwargida da amarya contact Surayya Halin yau.
+234 803 277 3332.
Kano Nigeria.

  Nuna Gwammaja har wajen ƙarfe goman dare. Domin da mazajen namu suka shigo gidan can bayan sallar isha'i gabaɗyansu suna falon Nene da ƴan'uwansu suna ta hira a tsakaninsu. Mu kuma muna ƙasa mun yi sallah mun koma muna ta zaman hira. A lokacin mganar haihuwa muke yi sun sin ina son na ƙara haihuwa ko daga yadda na ke kan hanyar yawon asibiti. Hauwa ce ke tambayata ya ake ciki ne yanzu? Kai na rausayar kafin na ce" To ana dai kan gwaje gwaje duk da kamar guda biyu suka rage amma Likitan tana ta ba ni tabbacin ba matsala ko ma akwai ba wacce za ta gagare su ba ne."

  Tare da Munniran suka haɗa bakin faɗin" In sha Allahu ma ba wata matsala."
Sai na amsa da Allah ya sa cikin wani yanayi na ce" Yallaɓai na son yara sosai. Biyu sun yi masa kaɗan ni na sani."
Hauwa ta ce" Amma ai ba ya nuna damuwa ko?
Sai na gyaɗa mata kai Munnira ce ta karɓe da cewa" Yallaɓai fa bai da damuwa. Damuwar su ne su Anty Bahijja. Ni da na ji ma wani batu amma dai ba ri na yi shuru."

  Sai na kalleta gabana ya faɗi saboda na san tabbas abin da ta ji ya shafe ni.
Da sauri Hauwa ta ce"Gwara ki yi shurun Munnira. Ni ma da na je Rano cikin azumi na ji batun a gida."
Sai kawai na kallesu kafin na yi mgana Munnira ta ce" Au kema? To me za a ɓoye mata ai mgana ce ba cewa muka yi ya tabbata ba. Kuma zaman tare kenan gwara mu faɗa mata ta san halin da ake ciki ko da ta faru ma  ta san in da za ta bullo ma lamarin."

Cikin É—auriya na ce" Wai menene? Ku faÉ—a min ai ban isa na hana Allah ya yi ikon shi ba."
Hauwa ce ta kalleni kafin ta ce" A bakin  Autar gidanmu na ji wai ƙannen Gimbiya ke faɗin Tafida za ta aura. Da na ce ban san da wannan mganar ba Innamu ta ce itama ta ji kuma a bakin makusantan ita Hajiyar Tafidan an ce daman tun farko Hajiya Nene da Hajiya tafidan sun so su haɗa zumunci na auran Gimbiya da Tafida Allah bai yi a wancan lokacin ba. Mutuwar mijinta ya nuna cewa rabon Tafida ce."
Ina kallon Hauwa amman na kasa mgana Munnira ta karɓe da cewa" Nima haka na ji wallahi. Kun san wacece ta min mganar?
Hauwa ce ta girgiza mata kai ni dai ko motsi ban yi ba

"Suwaiba ce fa kwanaki da ta zo gidana ta ke min zencen. Wai Anty Bahijja ta ce wannan karon Gimbiya Rabon Tafida ne. Shi ya sa ma wai ƙila aka dawo da ita wajen Nene."
Hauwa ta ce" Ni kaina na yi mamakin dawowarta. In aiki ne ai ba kullum ta ke zuwa ba kuma tunda tana da mota za ta iya zuwa a ranar kuma ta koma gida."
Munnira ta ce" Har Nasir na yi ma mgana ya ce mini shi bai sani ba gulma ce ta mu ta mata. Amma wallahi Sadiya na hango gaskiya ba rami me zai kawo mganar rami? Da man ta yi ta shige masa ni fa wallahi haushi ta ke ba ni."
Hauwa ta yi tagumi kafin ta ce" Ni kaina na fara hango hakan. Mganar fa daga bakin ƙannen Gimbiyar ta fito. Kin ga ko sun ji ana mganar ne."

  Ganin yadda na yi shuru kawai ina sauraran su ya sa Hauwa ta dafa kafaɗata tana faɗin" Kar ki damu Sadiya. Ni na san ko auranta Yallaɓai ya yi ba za ta sha gaban ki ba."
Munnira ta taɓe baki kafin ta ce" Ni wallahi da wata ta waje ne wacce ba a sani ba. Amma wannan Gimbiyar fa ban so. Sai Sadiya ta zama mujiya Allah su Anty Bahijja ware ta za su yi daman ya ya a ka cika?

Hauwa ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce" Da wannan kuma da wanman."
Munnira cikin jin haushi ta ce" Har fa wani suna take kiran shi Daddy shi kuma ya ce mata me ne ma?

"Daughter"

Na faɗa ina kallon Munnira da ta yi tsaki kafin ta ce" Ke kuma wai duk kika ƙyale? Suna waya to?
Sai na gyaÉ—a kaina kafin na ce

" Suna yi mana."
Chapter 71 · 0% Book details