Sashe 14
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Yana mirmishi ya shafa kumatuna kafin ya ce"To a saki fuskar, shan kunin ya isa haka."
Kalamansa suka ba ni dariya, sai na murmusa, mun cigaba da karyawa mun gama kenan na kallesa ina faÉ—in"Wata kwangilar a ka samu a Rano kuma?
Ya na miƙewa ya ce"Ban sani ba. Abba ya ce na shigo mu je mu gani."
 Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Allah ya sa a dace? To su dai waɗancan masu payment ɗin shuru ko?
 Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Wallahi shuru. Amman ban cire rai ba tun da sun ce ko da yaushe zan iya jin su." Fatan alheri na yi masa amman ban yi ɗoki ba domin ni nasan yanayin aikin shi, sai a yi shekara ana cewa za a biya shuru amman fa aka biya muna warkewa masha Allah tunda kuɗi ne ba kaɗan ba, kuma in aka samu aikin ana yin shi muna shiga hali tunda kuɗin shi zai ɗauka ya yi amfani dashi a karkashin kamfaninsa na HM. TAFIDA AND SON'S LIMITED. office ɗinsa na can hanyar zoo road kan titin Zaria Road.
 Ni na raka shi har bakin mota kamar yadda muka saba, ya ba ni 2k ya ce na hau adaidaita zuwa gidansu da ke Gwammaja, muka rabu bayan ya rumgumeni ya sumbaceni, nima na maida masa martani, yana ɗaga min hannu nima ina ɗaga masa da fatan Allah ya kai shi lafiya ya dawo mini dashi lafiya.
 Bayan tafiyarsa na koma cikin gida, falon farko na zauna saboda ka da Saude ta zo ta yi ta buga gida ina ciki ban sani ba, sai na kunna kallo tunda akwai wuta a tashar arewa 24 suna haskawa wani film hausa mai suna Ahalil kitab duk da na kalli Film din amman ina son waƙoƙin ciki sai na zauna ina kallo har na ji buga gida na je na buɗe ma Saude muka shigo tare, na zauna na cigaba da kallona ita kuma ta fara aikinta.
 Kafin azahar ta gama min komai, ni har barci ma na yi a saman kujera anan falo da za ta tafi na ba ta 500 na ce ta hau abin hawa, tafiyarta ba dadewa su Jidda suka dawo daman na yi ma Salisu maganan zai kai su Alu Venue anguwan su Anty Maimuna sai ya ce mini bari ya je ya yi sallar jumma'a ya dawo kan nan sun shirya.
 Sai murna suke yi tunda na ce can za su yi Weekend,tunda akwai jikokin yarta na fari Mardiya suna wajen Anty Maimunan ne sa'anin Baby ne, sannan autan ta ma sa'ar Jidda ne Afiyatu.
 Ban yi musu girki ba, Coorfleck na ce su sha bayan sun sauya kaya sun yi sallah. Kayan su suka saka iri ɗaya shadda mai ruwan ƙasa da na ɗinka musu da sallah da ta wuce da mayafansu, iri ɗaya har takalminsu iri ɗaya ne, na faɗa ma Jidda su yi kitso a can saboda na san ba da wuri za su dawo ba. Ban san me ya sa Anty Maimuna ta ke kulafacin su Jidda ba, ko don Baby ita aka yi ma takwara? Ko kuma daman can ita mai son yara ce gaskiya.
Ɗaya da rabi na rana Salisu ya dawo ya ɗauke su suka tafi. Suna tafiya nima na shirya na saka wata atamfata hollad mai ruwan ganye, sai na yi amfani da green ɗin mayafi jaka da takalmina kuma na saka baƙi, key ɗin gidan da na ɗauka sai da na tabbatar da na kashe komai na wuta sannan na fita na rufe get ɗin da makulli, ban samu adai daita ba sai da na taka zuwa babban titi, anguwan shuru daman haka take to ta masu kuɗi ce, kowa na gidajenshi shi ya sa ƙawa ko ɗaya ban da shi a rukunin nan sun shigomin lokacin da muka tare amman ni da ya ke halina sai ni sau ɗaya na taba shiga gidan gefen mu gidan maman muhsana, da ta haihu na yi barka. Allah ya halliceni mace mara sson shige ma mutane, ko yan gidanmu in ba wani abu ya faru ba, ba kasafai nake zuwa ba, gwara na yi zama na a gida in yi barci ya fiye minim
 Drop na ɗauka zuwa Gwammaja. Muna tafe na ji wayata na ringing a jaka na ɗaukota na duba sai na ga Zaituna ce Matar Yaya Abubakar. Na yi mamakin ganin kiranta domin ni dai ban wani yi da ita na fi yi da Anty Khaleesat ɗin Yaya Hamza. Ita Zaituna akwai kwaɗayi da surutu da an ce kace kace shi ya sa ban cika sakin mata ba, sannan daman ina jin haushin mijinta shi ya sa na ɗauka a dakune ban sakar mata fuska ba.
Bayan mun gaisa, sai na yi shuru ina jiran abin da za ta ce.
"Kina gida ne Sadiya?
 Yamutsa na yi kafin na ce"A'ah me ya faru?
Kai tsaye ta ce"Ayya daman ina kusa da anguwarku ne, mun zo suna gidan wata Æ´ar'uwarmu ne, na ce bari in kira ki in kina gida, sai na biyo."
 Daga yanayin yadda take magana kamar a wahale, na fi tunanin ƙila sun je ne ma ba abinci za ta ce ina kusa bari ta kirani ta daɓo gayyar danginta su zo min gida, na ji daɗi da ba na gida saboda ita ma Zaituna ƴar ƙashin bayan Ma'u ce.
"Ai ko ba na gida, ina hanya za ni Gwammaja gidan su Yallaɓai."
 Sai ta ce to shike nan, daman ta ɗauka ina gida ne, daga nan muka yi sallama.
Na kashe wayata ina hararan wayar kamar ita ce a ciki, na tuna ko faÉ—an da muka yi da Ma'u a gidan Rahila, suna yan gaba gaban saka bakin cewa ni ce ba ni da gaskiya.
 Wayata na mayar jaka, ni kaɗai ina ƙunƙuni ni fa su san halina duk wanda ya ci tuwo da ni wallahi miya ya sha, ga su ga Ma'un duk za su ci ubansu.
 Mai adaidaita bai direni ko'ina ba sai ƙofar gidan Iyayen Mijina da ke Anguwan Gwamnaja. Na sauko daga adaidaitan ina miƙa mi shi kuɗin shi na ji an kira sunana.
"Anty Sadiya.."
 Ina juyawa sai na ga Adnan ne, sai da na sallami mai adaidaitan ya tafi sannan na nufe shi, ya na tsaye a ƙofar gidan shi da abokonsa guda biyu sun sha manya kaya ƙila daga masallacin jumma'a suke.
"Adnan manyan kasa, yaushe a gari?
Na faÉ—a ina kallonsa yana dariya ya ce"Jiya na shigo garin. Ina su Jidda?
 Ina amsa masa da cewa sun tafi gidan Anty Maimuna, abokansa suka gaisheni na amsa, jakar hannuna ya karɓa muka jera zuwa get ɗin gidan.
 Gidan Marigayi Alhaji Muhammad Inuwa babban gida ne, mai bene sama da ƙasa. Ko haraban gidan wargajeje ne, duk da mai gidan ya fi shekara ashirin da rasuwa, gidan bai rankwafa ba, saboda ya hayyafa, kuma ƴa'ƴa sun tasa, in wannan bai kawo ba wannan zai kawo, shi ya sa ƙyallin gidan har gobe bai daina haskawa ba.
 Muna tafe ne zuwa cikin gida Adnan na yi min hira makaranta. A ABU ZARIA ya ke karatunsa na Engniaring, a tsakar gidan muka ga Jawahir na shanyan ƙananun kayanta da ta wanke.
 Tana ganina ta washe baki ta na faɗin" Anty Sadiya."
Na amsa ina faÉ—in"Au kema kin zo hutun ne? Ko guduwa kika yi?
Dariya ta saka tana faÉ—in" Kai Anty Sadiya, da ne fa yanzu ai mun zama Æ´an makaranta."
 Adnan ya ce"Tunda ba ki son bokon ki yi aure mana ko Anty Sadiya? Kai na gyaɗa ban yi magana ba Jawahir ta balla ma Adnan harara lokaci ɗaya ta na faɗin" To ai sai ka zo ka yi min auran ubana."
Yana Æ´ar dariya kafin ya ce"Ko ba ki faÉ—a ni ubanki ne, domin zan iya É—aura miki aure."
 Suka kacame da gaddamansu na saƙo da saƙo ni kuma ina ta dariya. Jakata na karɓa hannun Adnan ina faɗin"Bari na karisa, su Hajiya Iya ba sa nan ne na ji gidan shuru?
 Jawahir ta ce" Maman Farko ba ta nan an yi musu rasuwa, Iya kuma ta kwanta ne Nene kuma ki haura sama ta na ciki."
 Wuce su na yi, na bar su suna musu, ya na cewa shi ubanta ne, ita kuma ta na cewa Allah ya kyauta ya zama babanta.
 Shashen ƙasa Hajiya Iya ne da Mahaifiyar su Jawahir marigiyayiya Hajiya karima Allah ya jiƙanta, sama kuma Hajiya Nene da Maman Farko suke bangaren sama, amman a ƙasa akwai ɗakunan baki daga can haraba kuma akwai ɗakunan mazan gidan.
 Sama na haura, ƙofar shashen Nene ne a farko tun kafin na shiga na jiyo hayaniya, ina sallama bayan na cire takalmi na sannan na shiga babban falon na Nene. Hauwa na gani zaune a falon sai fama take yi da yara, Hauwa matar ƙanin Yusuf ne mai bi masa, Muttaƙa. Sai ƴaƴan Halima da su ban ga uwarsu ba, ina ga su kaɗai aka kawo Nene ba ta falon ma gabaɗaya.
 Hauwa na ganina ta tare ni da mirmishi, karamar ƴarta, Sahla ta nufoni ta na min oyoyo na taro ta ina ƴar dariya saboda yarinyar ta gane ni, duk in da ta gani ta riƙa gwarancin mgana kenan, suna zuwa gidana sosai nima ina zuwa saboda Hauwa tawa ce, duk cikin Facalolin gidan ba ni da kamar Hauwa.
 A bangaren Matan gidan ba ni ba ce Babba ba, akwai Matar Yaya Usman Zabba'u, sai ni sannan Muniran Yaya Nasir sai Hauwa da tsakanin auren mu da na su shekara shidda ne. Amman ina son Hauwa saboda muna da kamaceceniyar hallaya, ba ruwanta tana da sanyin hali duk da yar uwa ce tun da ƴar rano ce a can Mutaƙƙa ya auro ta.
Gaisawa muka yi faram faram kamar yadda muka saba in mun haÉ—u.
"Ina Nene?
Sai ta ce mini ta shiga ciki ta kwanta.
Yaran Halima na kallah kafin na ce"Tare da Haliman suke? Na ga ban ganta ba?